Wasa ya fara zafi
Croatia na neman ramawa yayin da Fransa ke naman hana su ko kuma kara musu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labarai da sharhi game fa da wasan karshe na gasar kofin duniya na shekarar 2018 da ake yi a birnin St Petersburg na Rasha
Abdulwasiu Hassan
Croatia na neman ramawa yayin da Fransa ke naman hana su ko kuma kara musu.
Antoine Griezmann ne ya ci wa Faransa ta hanyar fenareti.
Faransa za ta iya ci kuwa?
Faransa nea neman Fenareti. Lafiri zai je dubawa.
Ivan Perisic ne ya ci wa Croatia kwallon
Antoine Griezmann ya kawo kwallo mai kyau kuma Varane ya kusa samun kwallon, amma kafinnan,Mario Mandzukic, ya tura kwallon cikin ragar kasarsa da kai.
Wannan ya ci karo da yadda ake wasa a wannan wasan karshe na gasar kofin duniyar!
Sau daya ne Antoine Griezmann ya taba kwallo cikin mintuna 12 na farko...
Croatia ta fara wasan da karfinta - kawo yanzu sun fi Faransa rike kwallo a gidanta.
Da alama hankalin Croatia na a kwance . Faransa kuma tana kokarin gano kan wasan ne tukunna.
Croatia na amfani da 'yan wasan gefenta wajen kai wa Faransa farmaki.
Faransa ba ta taba sha kaye a wasan da aka ta fara da Pogba da Kante ba. Amma hakan zai iya faruwa a yau kuwa?
Croatia ta fara wasan ne da rige kwallo da kai farmaki. Shin Faransa za ta zauna a gida ne kawai ta rinka aika wa Mbappe kwallo?
An fara wasan karshe na gasar kofin duniya ta shekarar 2018.
Luka Modric, keftin da kuma madugun tawagarsa, shi ne tauraron tawagar kwallon kafa ta Croatia.
Ya samu kyautar gwarzon wasa a wasanni uku cikin shidan da ya buga a gasar kofin duniyar.
Duk da cewar ya barar da fenareti a wasansu da Denmark bai damu ba. A cikin nitsuwa ya zura fenareti cikin raga a karshen wasan.
Amma masoya kwallon kafa da yawa Croatia suna korafi game da irin rawar da dan wasan na Real Madrid ke takawa.
Tsohon dan wasan Ingila, Rio Ferdinand, ya ce 'yan wasan da suka hada kai a matsayin tawaga guda kuma suka fahimci abinda mai horaswarsu ke so sun taka rawar gani a wannan gasar.
(Croatia) Sun taba yin irin haka a muhimman gasa. Shi ya sa suka samu shiga wannan wasan karshen, in ji Ferdinand.
Zai zam dan wasan Faransa mafi karanci shekaru da ya taba buga wasan karshe na gasar kofin duniya.
Wannan shi ne wasan karshe na goma na kofin duniya (a jere) da za a samu akalla dan wasa daya daga Bayern Munich da Inter Milan a cikin masu taka leda.
Wadannan ne 'yan wasan Madrid da za su buga wa kasashe biyun da ke karawa a wasan karshe na gasar kofin duniya ta shekarar 2018.
Kasashen biyu dai ba su sauya 'yan wasansu ba. 'Yan wasan da suka buga musu wasan da suka buga na baya bayan nan ne za su fara musu wasa.
Jama'a, barkanku da shigowa wannan shafin inda za mu kawo muku labarai da sharhi game da wasan karshe na gasar cin kofin duniya tsakanin Faransa da Croatia.