Sharhi
A karon farko cikin shekaru biyu Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na ziyara a Kano. 'Yan siyasa a jihar sun jima suna korafi kan lokacin da shugaban ya shafe bai kai ziyara jihar ba, wacce take 'cibiyar siyasar sa'.
Kano ce ta bawa Buhari kuri'a mafi yawa a lokacin zaben shugaban kasa na 2015. To sai dai magoya bayan Buharin na cewa ba su damu da rashin ziyarar ba, tun da dai akwai kauna tsakaninsu da shugaban.
A bangare daya kuma wasu na ganin cewa Shugaba Buhari ya kai ziyarar ne a yanzu kasancewar lokacin zabe ya fara karatowa.
To amma wasu na hannun daman Buharin na cewa Shugaban ya jinkirta ziyarar ne har sai an samar da manyan ayyukan da zai kaddamar idan ya je ziyarar.
A ziyarar ta kwanaki biyu, Shugaba Buhari zai bude wasu manyan asibitoci biyu a birnin da gwamnatin Ganduje ta karasa.
To sai dai masu suka na cewa babu wani aikin gwamnatin tarayya da za a nuna a jihar a cikin shekaru biyu da Buhari ya hau mulki.
An dai tsarara matakan tsaro a jihar, inda aka jibge yan sanda 8,000 bayan ga jami'an tsaron farin kaya da sojoji da ke sintiri a birnin. Haka kuma akwai jirage masu saukar aungulu guda biyu da ke shawagi a birin.