MDD na cikin haɗari idan ba ta sauya salo ba - Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta canza salo idan har tana son ci gaba da kasancewa mai tasiri a duniya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar ta hannun mataimakinsa, Kashim Shettima, a yayin taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a birnin New York, inda ya zargi MDD da yin watsi da ainihin matsalolin da duniya ke fuskanta.
A cewarsa, rashin sauya salo na iya sa duniya ta fara kauce wa Majalisar wajen tattauna muhimman lamurra.
Shugaban ya nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da harkokin MDD da kuma jinkirin da ake samu wajen kawo Ƙarshen rikice-rikicen kasa da kasa, musamman rikicin Falasɗinu.
Ya ce "Rashin tsayin daka wajen ɗaukar mataki akan irin wadannan rikice-rikice ya zama babbar matsala ga rayuwar mutane” Shugaban ya jaddada cewa mafita ta dindindin ga Falasdinu ita ce tsarin kafa ƙasashe biyu domin tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban ya kuma sake jaddada buƙatar Najeriya ta samu kujerar dindindin a kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewa dole a sabunta tsarin domin ya dace da halin da duniya take ciki a yanzu.
A bangaren tattalin arziki kuwa, Shettima ya buƙaci a samar da wata kotu ta kasa da kasa da za ta rika kula da lamuran bashi, domin taimaka wa ƙasashe masu tasowa.