Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/09/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Jama'a nan muka kawo ƙarshen shafin namu na yau.

    Sau kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya

  2. Mutum miliyan 30.5 ne za su kamu da cutar kansa nan da 2050 - Rahoto

    Wani sabon rahoto kan cutar kansa ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2050 mutum miliyan 30 da rabi za su kamu cutar a duniya.

    Rahoton na mujallar lafiya ta 'The Lancet' ya ce ƙasashe matalauta ne matsalar za ta fi shafa inda aka yi hasashen samun ƙaruwar cutar da samun yawan mace-mace.

    Rahoton ya ce za a samu ƙaruwar masu cutar kansa da kashi 61 zuwa 2050.

    Hasashen binciken ya ce mutum sama da miliyan 30 za su kamu da ciwon na kansa a 2025 daga mliyan 19 da aka yi hasashe a shekarar 2024.

    Binciken ya ce hakan zai faru ne saboda ƙaruwar yawan jama'a a duniya.

    Binciken ya kuma yi hasashen cewa sama da mutum miliyan 18 ne ciwon na kansa zai kashe inda adadin zai kai kusan kashi 75 cikin dari .

    Rahoton ya yi nazari ne kan nau'ikan ciwon kusan 47 a ƙasahse 204 tare da bibiyar yawaitar mace-mace daga 1990 zuwa 2023 wanda ya bayar da damar yin hasashen zuwa shekarar 2050.

  3. WHO ta musanta ikirarin alakanta cutar galahanga da maganin Paracetamol

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta musanta ikirarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa shan maganin zazzaɓi na Paracetamol a lokacin da mace ke da juna biyu na haifar da cutar matsalar ƙwaƙwalwa wato galahanga.

    WHO ta ce babu wata hujja a kimiyyance da ta tabbatar da iƙirarin shugaban na Amurka.

    Cikin wata sanarwa da hukumar Lafiyar ta duniya ta wallafa a shafinta na intenet, ta ce akwai tarin biciken kimiyya masu yawa da aka gudanar cikin shekaru 10 da suka gabata, amma babu wanda ya taɓa tabbatar da alaƙar cutar galahanga da kuma maganin na Paracetamol.

    WHO ta shawarci mata masu juna biyu su ci gaba da bin shawarar likitocinsu, waɗanda su ke taimaka musu ta hanyar ba su maganin da ya kamata su sha.

    A cewar hukumar lafiyar kowane magani na da ƙa'idar da ake bi wajen shansa, musamman a watanni ukun farkon kowane juna-biyu, kuma ana sha ne bisa shawarar likitoci.

    A makon da ya kamata ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wani jawabi game da cutar, galahanga, inda ya ce ta fara yawaita a Amurka, yana mai cewa dole gwamnatinsa ta ɗauki mataki bayan gano musabbabinsa."

    Wasu bincike da aka gudanar sun alaƙanta shan sinadarin acetaminophen - wanda shi ne asalin sinadarin da ke cikin Paracetamol - da cutar kwakwalwa, amma binciken ba su fayyace alaƙar ba, da kuma irin illar da maganin ke yi.

    A cewar hukumar lafiyar matsalar galahanga na daga cikin manyan matsalolin lafiya da ta ke bai wa fifiko a ayyukanta kuma ake yawan tattauna ta a manyan tarukanta na duniya.

    Alƙaluman hukumar sun nuna cewa kusan mutum miliyan 62 ne a duniya ke fama da matsalar galahanga - da ake samu sakamakon wasu matsaloli masu alaƙa da ƙwaƙwalwa.

    Duk da ƙaruwar kiraye-kirayen wayar da kai da ake yi game da matsalar a shekarun baya-bayan nan, WHO ta ce har yanzu ba a gano haƙiƙanin abin da ke haifar da matsalar ba, kodayake an fahimci abubuwa da dama ne ke haifar da matsalar.

    Daga ƙarshe hukumar Lafiyar ta duniya ta ce tana jajanta wa masu fama da lalurar a faɗin duniya tare da kira ga mutane su guji ƙyamar masu lalurar, saboda kowa da irin ƙaddarar lalurar da ubangiji ke jarrabarsa da ita.

  4. Shugaban Falasɗinawa ya yi jawabi a taron MMD ta bidiyo bayan hana shi zuwa Amurka

    Shugaban Falasɗinwa Mahmoud Abbas, ya yi jawabi ga bababn taron Majalisar Dinkin Duniya ta bidiyo daga Ramallah, bayan da gwamnatin Trump a hana shi biza shigar Amurka.

    A jawabin nasa Mista Abbas ya nanata Allah wadansa kan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila tare da jaddada cewa babu rawan da Hamas za ta taka bayan ƙarewar yaƙin Gaza.

    ''Mun tabbatar kuma za mu ci gaba da sanar da cewa , Zirin Gaza na daga cikin wani ɓangare na ƙasar Falasɗinu. Jagorancin kuma a shirye mu ke mu ɗauki nauyi game da lamarin tsaro a can. Hamas ba ta da wata rawa da za ta taka wajen jagorencin'', in ji shi.

    Shugaban Falasɗinawan ya kuma zargi Israila da kai farmakin yaƙi na kisan kiyashi a Gaza. Toh sai dai ya yi kira a kawo ƙarshen yaƙin tare da sakin waɗanda ake garkuwa da su, sannan a karɓe makaman ‘yan Hamas.

    Mahmoud Abbas mai shekara 89 - wanda jami'an diplomasiya ke masa kallon wanda zamaninsa ya shuɗe kuma ba zai iya taka wata rawa mai tasiri ba.

    Amurka na zargin shugaban Falasɗinawa da rashin kataɓus wajen yin allah wadai da ta’adanci kuma ta hana shi bizar shiga ƙasar.

    An dai jima ana tuhumar hukumomin Falasɗinu da ke jagorancin yankin Gaɓar Yamma da cin hanci da rashawa da rashin ƙwazo da kuma rashin hallasci.

    Zuwa yanzu da dama daga ƙasashen Yammaci da kuma na yankin larabawa sun yi imanin cewa hukumomin Falesɗinu ba za tabba samun taimakon da zai basu karsashin tafiyar da Gaza bayan tsagaita wuta ba.

  5. Singapore ta buƙaci Meta ya dakatar da masu amfani da sunayen jami'an gwamnati a Facebook

    Singapore ta ce ta bai wa kamfanin Meta wa’adin zuwa ƙarshen wannan watan na Satumba domin daƙile yawaitar masu yaudarar jama’a da ke yin ungulu da kan zabo da hanyar amfani sunan jami’an gwamnati a dandalin Facebook.

    Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta ƙasar ta gargaɗi kamfanin cewa, za a ci shi tarar fiye da dala 750,000 idan ya gaza bin umarnin.

    Hukumomin Singapore sun ce masu zambar na amfani da Facebook wajen karɓe wa mutane kuɗaɗe da suka kai miliyoyin daloli.

    Kamfanin na Meta ya ce yana da wani tsari na musamman domin gano asusun da aka buɗe na bogi, tare kuma da aiki da hukumomin tsaro wajen ɗaukar matakan shari’a kan waɗanda ke da hannu a cikin wannan zamba.

  6. Abin da ya sa muka kira taron jiga-jigan APCn Kano - Ganduje

    Ganduje Tsohon shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai butuwa uku da ya sa suka kira taron jiga-jigan APCn Kano a Abuja.

    A yau ne jiga-jigan jam'iyyar suka gudanar da wani taro a Abuja.

    Tsohon gwamnan na jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce abu na farko da ya sa suka kira taro shi ne taya juna murna kan irin nasarororin da APC ta samu a Kano tun bayan faɗuwa zaɓen gwamnan jihar.

    Ganduje ya kuma ce abu ne biyu shi ne domin tsara shrye-shirye da dabarun samun nasarar APC a zaɓe mai zuwa.

    ''Abu na uku kuma shi ne domin gode wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu kan irin ayyukan gwamnatin tarayya da ake yi a jihar kano, da kuma tarin muƙaman da ya bai wa Kano a gwamnatinsa'', in ji Ganduje.

  7. Ma'aikatanmu na buƙatar makamai - Shugaban FRSC

    Shugaban Hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗurra ta Najeriya, (FRSC), Shehu Mohammed, bai wa jami'ansa makamai ne hanya guda ɗaya tilo da za ta tabbatar da dokokin tuƙi a kan manyan titunan ƙasar.

    Yayin wata hira da gidan talbijin na ARISE NEWS ranar Alhamis, Mohammed ya bayyana irin hatsarin da ya ce jami'an hukumar na shiga a lokacin da suka gamu da masu ababen hawa.

    Ya ce ta yaya jami'ai ƙalilan da ke sintiri za su iya dakatar da manyan tirelolin da aka yi wa lodi fiye da ƙima da kuma tankokin da ke ɗaukar kaya haɗe da gomman fasinjoji.

    Shugabab na FRSC ya ce matsawar ba a bai wa jami'ansa abin da ya kira ''ƙarfin aiki'' to zai yi wahala a iya tabbatar da dokokin tuƙi a ƙasar.

    “Idan ba ka da ƙarfin da za ka tilasta yin abu, ba yadda za ka tabbatar da bin doka'', in ji shi.

    Ba wannan ne karon farko da jami'an hukumar ke kiraye-kirayen ba su makamai ba.

    To sai dai masana na ganin aikin jami'an hukumar ba ya buƙatar makami, yayin da wasu ƴan ƙasar ke ganin ba abin da hakan zai haifar sai ƙara dakula lamurra.

  8. An kama tan 10 na hodar Ibilis a tekun Afirka ta Yamma

    Sojojin ruwan Faransa sun ce sun kama kusan tan goma na hodar iblis a bakin tekun Yammacin Afirka da darajarta ta kai kusan dala miliyan ɗ600.

    Gammayya kungiyoyin da ke sintiri a tekun ciki har da na yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ne suka kama jirgin.

    An kuma gano hodar ibilis ɗin ce a cikin jirgin da ba shi da tutar wata ƙasa a cikin tekun Atlantic.

    Wata ƙungiya da ta taka rawa a aikin ta ce kamen ya nuna yadda yankin Yammacin Afirka ya zama muhimmin wurin ya-da zango kafin jigilar hodar iblis daga Kudancin Amurka zuwa Turai.

  9. 'Rabin ƙananan yaran Somaliya ka iya fuskantar yunwa nan da 2026'

    Wani rahoto da ƙungiyar agaji ta 'Save The Children' ta fitar ya yi gargaɗin cewa kusan rabin yaran Somaliya ‘yan ƙasa da shekara biyar na cikin hatsarin fuskantar matsananciyar cutar Tamowa nan da tsakiyar shekarar 2026.

    Ƙungiyar ta ce ƙasar na dab da fuskantar barazanar ɓarkewar ƙarancin abinci mai gina jiki a tasakanin ƙananan yara, sakamakon matsalolin da suka shafi yanayi da tashin farashin kayan abinci da kuma rikice-rikicen da ke da nasaba da tsaro.

    Save The Childen ta ce hakan na zuwa ne sakamakon yanke tallafin agaji ya tilasta rufe wasu muhimman cibiyoyi da ke samar da abinci mai gina jiki a ƙasar.

    An yi hasashen kusan kashi ɗaya bisa huɗu na al’ummar ƙasar, za su shiga matsanancin ƙarancin abinci kafin ƙarshen shekarar 2025 da muke ciki.

  10. Jiga-jigan jam'iyyar APCn Kano na taro a Abuja

    Jagororin jam'iyyar APC na jihar Kano sun fara gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki na musamman a Abuja.

    Taron ya samu halartar tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau Jibril da Sanata Kawu Sumaila da Abdullahi Abbas da Murtala Sule Garo da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

    Ana sa ran taron zai tattauna muhimman batutuwan da suka shafi makomar jam'iyyar, musamman a siyasar jihar Kano.

  11. Ma’aikatan lantarki sun fara yajin aiki a Najeriya

    Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta ƙasa a Najeriya (NUEE) ta umarci dukkan mambobinta da su dakatar da aiki nan take, kamar yadda ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar.

    Matakin ya janyo fargaba kan yiwuwar katsewar lantarki a sassan ƙasar, musamman a wuraren da aka samu ci gaba wajen samun wutar tun bayan ƙara kuɗi a shekarar da ta gabata.

    Ƙungiyar ta bayyana dalilan yajin aikin da suka haɗa da rashin biyan albashi tun daga watan Afrilun 2025, da gazawar gwamnati wajen aiwatar da mafi ƙarancin albashi da rashin kayan aiki da na kariya, da kuma rashin biyan hakkokin fansho.

    Haka kuma ta koka da yadda aka ci gaba da riƙe ma’aikata a matsayin na ɗan lokaci ba tare da daidaita matsayinsu ba.

    Sakamakon wannan yajin aiki, jama’a na iya fuskantar matsalolin samar da wuta, inda ake hasashen wutar za ta ragu ko ta daina samuwa gaba ɗaya a wasu wurare.

  12. Kusan rabin yaran Somaliya na cikin ƙangin yunwa

    Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta yi gargadin cewa yara a Somaliya na dab da fuskantar matsananciyar yunwa.

    Ta ce kusan rabin ƙananan yara a ƙasar na fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki saboda rikice-rikice da kuma ƙarancin tallafin agaji.

    Rahoton ya nuna cewa nan da tsakiyar shekarar 2026, kusan rabin yaran ƙasa da shekaru biyar a Somaliya za su iya fuskantar matsananciyar rashin abinci mai gina jiki.

    Wannan matsala ta samo asali ne daga haɗuwar matsalolin da suka haɗa da sauyin yanayi da tsadar abinci da rikice-rikicen cikin gida.

    Babban abin da ya ƙara wa matsalar girma shi ne yanke tallafin agaji, wanda ya tilasta rufe cibiyoyin lafiya da na ciyar da yara, abin da ya bar dubban yara ba tare da samun kulawar gaggawa da za ta iya ceton rayukansu ba.

    A halin yanzu, mutum miliyan 4.4 na fama da matsananciyar rashin abinci, kusan miliyan ɗaya kuma suna cikin mawuyacin hali, yayin da kimanin yara miliyan 1.85 za su iya fuskantar rashin abinci mai gina jiki a cikin ‘yan watanni masu zuwa.

    Ƙungiyar ta gargaɗi cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, rayukan dubban yara a Somaliya na cikin babban haɗari.

  13. Tsohon shugaban Malawi Peter Mutharika ya dawo mulki bayan cin zaɓe

    Tsohon shugaban ƙasar Malawi, Peter Mutharika, ya dawo mulki yana da shekaru 85, bayan da aka bayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓen makon da ya gabata.

    Ya samu kashi 57% na kuri’u, yayin da shugaban ƙasa Lazarus Chakwera, mai shekaru 70, ya samu kashi 33%.

    Chakwera ya amince da rashin nasara kuma ya taya Mutharika murna.

    Mutharika, tsohon farfesa a fannin doka, ya yi shugabanci daga 2014 zuwa 2020.

    Hukumar zaɓe ta ce ta ɗauki kwanaki takwas kafin ta ayyana sakamakon don tabbatar da sahihancinsa.

    Wannan shi ne karo na huɗu da Mutharika da Chakwera suka fafata a zaɓe.

  14. Mawaƙiya Rihanna ta haifi ƴa mace a karon farko

    Shahararriyar mawaƙiyar Amurka Rihanna ta haifi ƴarta mace ta farko tare da abokin zamanta ASAP Rocky.

    An sanya wa jaririyar sunan laƙabin mahaifinta - sai dai an canza harafin ƙarshe na sunan, daga 'y' zuwa 'i'.

    An haifi yarinyar - wadda yanzu sunanta Rocki Iris Mayer ne a ranar 13 ga watan Satumba, kamar yadda mawaƙiyar ta sanar a shafinta na Instagram, inda ta wallafa hotonta rungume da ɗiyar tata.

    Dama a bikin Met Gala ne iyayen suka sanar da cewa Rihanna na ɗauke da juna biyu.

    Rihanna da Asap na da ƴaƴa biyu maza Riot da RZA.

    Masoya mutanen sun yi maraba da labarain haihuwar ta Rihanna, inda sanawar ta samu 'likes' miliyan biyar a cikin awa biyu.

    Rihanna ta haifi ɗanta na farko RZA ne a 2022, sai na biyu Riot a 2023.

  15. An kama hodar ibilis mai yawan gaske a gaɓar Yammacin Afirka

    Sojojin ruwan Faransa sun tabbatar wa BBC cewa sun kama hodar ibilis mai nauyin tan 10 wadda kuɗinta ya kai dala miliyan 600 a wani jirgin ruwan kamun kifi, kusa da gaɓar ruwan Afirka ta yamma.

    Jiragen ruwan sojin Faransa biyu ne suka yi kamen a ranar Litinin bayan wata hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta Birtaniya ta ƙyanƙyasa musu bayanin jirgin.

    Bayan haka ne jiragen sojin biyu suka tare jirgin kamun kifin a kan tekun Atalantika.

    Kamen na daga cikin shirin samamen daƙile safarar ƙwaya da aka yi wa laƙabi da 'Operation Corymbe'.

  16. An yanke wa tsohon shugaban Faransa Sarkozy hukuncin ɗauri

    Wata kotu a Faransa ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Nicolas Sarkozy hukuncin ɗauri na shekara biyar bayan samun shi da laifin haɗa baki wajen tafka laifi a wata shari'a da ta shafi karɓar kuɗaɗe daga tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi.

    Sai dai kotun ta wanke shi daga sauran tuhume-tuhume a shari'ar wadda ta kasance mai sarƙaƙaiya.

    Duk da cewa kotun ta wanke shi daga laifin karɓar kuɗi kai-tsaye daga Gaddafi a shekara ta 2007 domin gudanar da yaƙin neman zaɓe, ɗaya daga cikin alƙalan ya ce Sarkozy ya bar mutanen da ke kusa da shi sun yi wasu abubuwa na neman tallafin kuɗi domin yaƙin neman zaɓen nasa.

    Sauran laifukan da aka wanke shi sun haɗa da rashawa da kuma amfani da kudin haram wajen yaƙin neman zaɓe.

    Sarkozy ya yi zargin cewa shari'ar wani bi-ta-da-ƙulli ne na siyasa.

    Masu shigar da ƙara sun zargi Sarkozy da yi wa Gaddafi alƙawarin wanke sunansa a tsakanin ƙsashen Yamma.

    Sarkozy mai shekara 70 a duniya ya kasance shugaban ƙasar Faransa daga shekarar 2007 zuwa 2012.

  17. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Haruna Talle Maifata

    A cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na wannan mako mun kawo muku tattaunawa da mai shiryawa kuma tauraro a masana'antar Kannywood, Haruna Talle Maifata wanda ya daɗe yana jan zarensa.

    Ɗan asalin garin Jos, Maifata ya ce har yanzu yana cikin harkar fim dumu-dumu duk da yadda wasu ke ganin kamar ya ɓace a harkar.

    Ya yi ƙarin bayani kan rawar da yake takawa a fina-finan Hausa da ake nuna a kafafe daban-daban na zamani.

  18. Najeriya ta fitar da taken bikin ƴancin kai na shekarar 2025

    Gwamnatin Najeriya ta fitar da taken bikin ƴancin kai na shekarar 2025. Taken shi ne “ Nigeria@65: Dole mu haɗa hannu domin ciyar da ƙasa gaba.”

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan bayani da hulɗa da Jama’a, Segun Imohiosen, ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

    Sanarwar ta bayyana cewa taken na nuni da buƙatar haɗin kai da aiki tare da kishin kasa tsakanin hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da ƙungiyoyin farar hula, da ‘yan ƙasa baki ɗaya domin tabbatar da zaman lafiya da arziki, da ci gaban kasa.

    Gwamnati ta ce zaɓen wannan taken yana nuna juriya da ƙwarin guiwar Najeriya tun samun ‘yanci a shekarar 1960, tare da jaddada muhimmancin karfafa nasarorin da aka samu a baya yayin da ake neman cimma manyan manufofi.

    Daga cikin ayyukan da aka tsara gudanarwa don bikin ƴancin kai na Nigeria@65 akwai Sallar Juma’a a ranar 26 ga Satumba da addu'o'i a coci daban-daban a ranar 28 ga Satumba, da kuma taron manema labarai a ranar 29 ga Satumba a babban birnin tarayya, Abuja.

  19. Sudan da Rasha sun sa hannu kan yarjejeniyoyin kasuwanci da zuba jari

    Sudan da Rasha sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi da dama, ciki har da yarjejeniyar haɗin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci, bayan zama na takwas na kwamitin hadin gwiwa na ministoci kan haɗin Kai na tattalin arziki a birnin Moscow, in ji rahoton jaridar Sudan Tribune da ke Paris.

    Ma’aikatar ma’adanai ta Sudan ta ce cikin yarjejeniyoyin akwai takardun fahimtar juna (MoU) kan sufuri da ababen more rayuwa da na banki.

    Rahoton ya ce ɓangaren Rasha ya yi alƙawarin sauƙaka zuba jari daga ɓangaren gwamnati da na masu zaman kansu, musamman a fannin sake gina Sudan bayan yaƙin basasar da take fama da shi.

    Sudan ta samu wakilcin ministan ma’adanai, Nur al-Daim Taha, yayin da tawagar Rasha ta samu jagorancin ministan Albarkatun Kasa, Alexander Kozlov.

  20. Saudiyya ta gindaya sabbin sharuɗɗan zuwa aikin hajji

    Tuni dai aka fara bayyana fargaba bayan da kasar Saudiyya ta bullo da wasu sabbin tsauraran ka'idoji ga maniyyata aikin Hajjin bana.

    Saudiyya ta tsaya kai da fata wajen yin aiki da sababbin ka'idojin, wanda idan ta tabbata da yawa daga cikin maniyyatan Najeriya ba za su sami damar zuwa sauke farali a aikin Hajjin da ke tafe ba.

    Yanzu haka dai wasu jami'an hukumar alhazan Najeriya suna kasar mai tsarki, domin tattauna yadda za a fuskanci sababbin matakan.

    Fatima Sanda Usara, mai rikon mukamin daraktar yada labarai ta hukumar alhazan Najeriyar, wato NAHCON ce, ta shaida wa BBC cewa, babban matakin da Saudiyya ta dauka shi ne da zarar an daina karbar kudin aikin hajji, to ba za su koma baya ba, ama'ana babu wanda za a karbi kudinsa daga baya.