Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/09/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Buhari Muhammad Fagge, Haruna Kakangi, da Umar Mikail

  1. An tabbatar da ɓullar cutar ƙyandar biri ta farko a Guinea

    Ma'aikatar lafiya ta Guinea ta tabbatar da bullar mpox ta farko a kasar, wacce aka gano a cikin wata yarinya 'yar shekara bakwai daga birnin Macenta da ke kudancin ƙasar, a cewar wani rahoto daga shafin intanet na Africaguinee mai zaman kansa.

    An ɗauki samfurin yarinyar wacce ta fito daga ƙaramar hukumar Koyama da ke Macenta , inda aka fara bullar cutar Ebola a shekarar 2014 a ranar 30 ga watan Agusta domin gwaji a cibiyar bincike na virologyinda a ranar 2 ga Satumba 2024, sakamakon binciken ya tabbatar da kasancewar cutar.

    Ma'aikatar ta kuma bayar da rahoton mutum tara da ake zargi da kamuwa da cutar tun daga ranar 26 ga Agusta.

  2. Tinubu ya ƙara wa babban sufeton 'yan sandan Najeriya wa'adin shekara 3

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarawa Babban Sefotun 'yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, kamar yadda wata majiya daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta bayyana.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito an ƙara wa shugaban 'yan sandan wa'adin shekara uku ne, ma'ana sai zuwa 2027.

    Ta ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ne ya bai wa Babbab Sufeton 'yan sandan takartar ƙara masa wa'adin a ranar Litinin.

    A watan Yulin da ya gabata ne Majalisar Dattijan Najeriya ta yi garambawul ga dokar 'yan sanda ta 2020 ƙarƙashin sashe na 8, wadda ta ci karo da ƙarawa ma'aikacin gwamnati wa'adin aiki bayan shekara 35 ko kuma bayan kaiwa shekara 60 a raye.

    Egbetokun wanda aka naɗa IG a watan Yunin 2023 zai cika shekara 60 ne a gobe 4 ga watan Satumba.

  3. An kashe mutum 129 da su kai yunƙurin tserewa daga gidan yari a DR Congo

    Ministan cikin gida na Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo, Jacquemain Shabani Lukoo, ya bayar da rahoton cewa, fursunoni 129 ne aka kashe a wani yunƙurin tserewa daga gidan yarin Makala da ke Kinshasa, wanda shi ne gidan yari mafi girma kuma mafi suna a ƙasar.

    Daga cikin waɗanda suka mutu, an harbe 24, yayin da wasu suka mutu sakamakon shaƙe musu wuya da aka yi da kuma turmutsutsu.

    Lamarin ya kuma yi sanadin raunata mutum 59 a gefe guda kuma an yi wa mata da yawa fyaɗe.

    Gobara ta kuma lalata wasu muhimman cibiyoyin gidan yarin da suka haɗa da gine-ginen gudanarwa da ma'ajiyar abinci.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin kisan gilla da aka yi a lokacin tserewa daga gidan yarin.

    Ƙungiyoyin sun yi amannar cewa cunkoson fursunoni 14,000 a gidan yarin wanda aka gina da zai iya ɗaukar fursunoni 1,500 kaɗai ne ya haddasa tarzomar.

  4. Dakarun Najeriya sun kama masu kai wa 'yan bindiga makamai

    Sojojin Najeriya tare da takwarorinsu na tsaro sun kama wasu mutane 15 da ake zargi da samar wa ‘yan bindiga makamai da sauran kayan aiki.

    Cikin wata sanarwa da sojojin suka wallafa a shafinsu na X, inda suka ce an yi kamen ne bayan samun bayanan sirri kan mutane.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an kashe wani mutum guda da ake zargin ɗan bindiga ne yayin wannan samamen a wurare da dama.

    A yayin saman dakarun Najeriya sun yi nasarar kama makamai masu dama da harsasai da kuma wasu kayayyaki na daban.

    “A ranar 30 ga watan Agusta 2024, dakaru sun kai hari kan 'yan bindiga da masu yi musu jigilar kayayyakinsu a Mararaba Donga da ƙauyen Manya da suke a Ƙananan hukumomin DDonga da Takum a jihar Taraba.

    "An kama mutum biyar da ake zargi a lokacin samamen, an kuma kamaya kayayyaki kamar haka: bindiga uku ƙirar AK-47, bindiga biyu ƙirar cikin gida, bindiga biyu ƙirar da ba ta gida ba, bindiga biyu ta farauta, wata bindiga mai ɗaukar harsashi 61 da dai sauransu.

    "A Yobe dakarun sun kama wasu masu kaiwa mayaƙan Boko Haram kayan aiki a ƙauyen Jimbal da ke ƙaramar Hukumar Tarmuwa.

    "A Kaduna an kama makamantan waɗannan mutane masu kai kayan aiki a ƙauyen Rijana a ƙaramar Hukumar Chikun. Tare da su akwai wayoyi uku da ke da katin waya sama da naira 100,000, an kuma samun garin kuɗi naira 1,532,900.

  5. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barka da wannan lokaci.

    Da fatan kun wayi gari lafiya a wannan rana ta Talata.

    Sai ku kasance da mu kamar kodayaushe da za mu kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya leƙawa domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.