KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 18ga watan Yulin 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Muna goyon bayan FRSC na hana wa’azi da tallace-tallace a cikin motocin haya - MURIC

    FRSC

    Asalin hoton, FRSC

    Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta bayyana goyon bayanta ga ƙudirin da Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) ta gabatar, wanda ke neman hana yin wa’azi da talla a cikin motocin haya.

    Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin wanda ya dace kuma zai taimaka wajen kare rayuka da rage haɗurran ababen hawa.

    A wata sanarwa da Darakta Janar na MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a ranar Asabar, ya ce yin wa’azi a cikin motocin kasuwanci na janye hankalin direbobi daga tuƘi, lamarin da ke iya haddasa haɗurra tare da jawo asarar rayuka da jikkata mutane.

    Ya ce ƙungiyar na ganin ƙudirin FRSC a matsayin mataki na hangen nesa da kuma kariya ga matafiya.

    Ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta gaggauta duba ƙudirin, tana mai nuni da yawaitar haɗurran mota a Najeriya.

    MURIC ta kuma buƙaci shugabannin Kirista da majami’u su ba da haɗin kai domin kare rayuka saboda shine ya kamata ya kasance fifiko ga kowa.

  2. Kotu ta yi watsi da ƙarar buƙatar gyaran zaɓen fidda gwanin APC a Magama/Rijau ta jihar Neja

    Babbar Kotun Tarayya da ke Minna ta yi watsi da wata buƙata da aka gabatar domin sauya sunayen ɓangarorin da ke cikin ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a mazaɓar Magama/Rijau ta jihar Neja.

    Ƙarar dai ɗan takarar APC, Shehu Auna, ya shigar ta hannun lauyansa, Abubakar Danjuma, yana ƙalubalantar sahihancin zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 16 ga Yunin 2026, wanda ya tsayar da Yakubu Auna a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

    A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Abdullahi Aminu Dan-Ige ya ce masu ƙarar sun kasa gabatar da gamsassun hujjoji da za su sa a amince da buƙatarsu saboda haka kotun ta yi watsi da ita.

    Sai dai lauyan mai ƙarar ya ce hukuncin bai shafi ainihin ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwanin ba.

    Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga Yulin 2026.

  3. Mutum bakwai sun mutu a harin Ukraine kan babban kamfanin sayayyar Rasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum bakwai sun mutu yayin da wasu 49 suka jikkata bayan hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da Ukraine ta kai kana rumbunan adana kaya guda biyu mallakin Wildberries, babban kamfanin sayayya ta intanet a Rasha.

    Mahukuntan Rasha sun ce dukkan mutanen da suka mutu da kuma mutum 25 daga cikin waɗanda suka jikkata suna cikini rumbun adana kaya da ke Tambov, kudu maso gabashin Moscow yayin da sauran mutum 24 da suka jikkata na ɗaya rumbun da ke Elektrostal a yankin Moscow.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce sun kai hare-haren ne kan manyan cibiyoyin jigilar kaya da ake amfani da su wajen samar da kayan da aka sanya wa takunkumi domin ƙera jiragen yaƙi marasa matuƙa da na’urorin kewayawa.

    Babbar jami’ar gudanarwar Wildberries, Tatyana Kim, ta bayyana lamarin a matsayin “mummunan dare” ga kamfanin da kuma Rasha.

  4. Iran ta ce ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma da Amurka

    ...

    Asalin hoton, IRNA

    Iran ta ce ta dakatar da aiwatar da dukkan alƙawurran da ke ƙarƙashin Yarjejeniyar Islamabad, tana mai zargin Amurka da karya yarjejeniyar ta hanyar abin da ta bayyana a matsayin hare-hare da matakan rashin mutunta yarjejeniyar.

    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce Amurka ta karya dukkan alƙawurranta na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu ta hanyar shiga tsakanin Pakistan.

    Ya bayyana matakin Iran a matsayin martani ga abubuwan da Amurka ke aikatawa.

    Gharibabadi, wanda ke cikin tawagar tattaunawar Iran da Amurka, ya ce a halin yanzu fifikon ƙasarsa shi ne kare kanta da kuma mayar da martani ga waɗanda take zargi da kai mata hari.

    An cimma Yarjejeniyar Islamabad ne domin kawo ƙarshen yaƙin da aka fama tsakanin Iran da Amurka na dindindin. Sai dai tun bayan hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa, sake rufe mashigar Hormuz ya sa an sake komawa musayar wuta tsakanin Iran da Amurka.

  5. Su wane ne waɗanda aka kama da zargin sace ɗaliban Oyo?

    ....

    Asalin hoton, Attorney-General of di Federation (AGF)

    Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wasu mutum da ta ce tan zargin su ne suka kitsa tare da jagorantar ƙaddamar da hari a makarantar jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar tare da sace ɗalibai.

    A makon jiya ne rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto dukkan ɗalibai da malamai su 44 da aka sace kimanin wata biyu da suka gabata daga makarantu a jihar Oyo da ke, sannan ta ce an kama wasu daga cikin masu garkuwar.

    Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin sojojinta sun rasa rayukansu yayin gudanar da aikin ceton.

    Sace ɗaliban na Oyo ya matuƙar ɗaukar hankali, inda har fitaccen mawaƙin Najeriya Davido ya isar da batun zuwa duniya bayan ya taka rawa a raƙashewar share fagen Gasar Kofin Duniya sanye da riga mai ɗauke da sunan ɗaliban.

    Matakin nasa ne ya haifar da zazzafar muhawara tsakaninsa da fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara a kafofin sadarawa.

  6. An yi kutse a shafin intanet ɗin fadar shugaban kasar Kenya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    An yi zargin cewa wasu masu kutse ta intanet sun kutsa cikin shafin intanet ɗin fadar shugaban Kenya, William Ruto, tare da neman a biya su kudin bitcoin biyar, wanda darajarsa ta kai kimanin shilling miliyan 41 na Kenya (dala 320,000) kafin su saki shafin a cewar rahotannin kafafen yada labaran cikin gida.

    Masu kutsen sun canza shafin gaba na intanet ɗin inda suka maye gurbin bayanan hukuma da saƙonnin cin mutunci ga shugaban kasar tare da barazanar fitar da wasu muhimman bayanan gwamnati.

    A halin yanzu, shafin president.go.ke ba ya aiki, kuma yana nuna saƙon cewa ana gudanar da gyare-gyare kuma za a dawo da shi nan ba da jimawa ba.

    Har yanzu hukumomin Kenya ba su yi wani jawabi kan wannanba.

    Lamarin na zuwa ne watanni kaɗan bayan wani babban harin kutse a watan Nuwamban 2025 wanda ya shafi wasu shafukan intanet na gwamnati a abin da hukumomi suka bayyana a matsayin hari na hadin gwiwa

  7. Kuwait ta ba da rahoton tashin gobara biyu sakamakon hare-haren Iran

    Kuwait ta ce hare-haren da Iran ta kai ranar Asabar sun haddasa tashin gobara a wurare biyu a ƙasar, lamarin da ya jikkata wasu daga cikin jami'an kashe gobara.

    Tun da farko dai an ba da rahoton cewa Iran ta kai hari kan wata tashar samar da wutar lantarki da kuma cibiyar tace ruwan teku a ƙasar.

    Hukumar kashe gobara ta Kuwait ta bayyana a wani saƙo da ta wallafa a shafin X cewa jami'anta na aiki kan kashe gobara biyun da suka tashi sakamakon sabbin hare-haren Iran ɗin.

    Hukumar ta kuma ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa cibiyoyin kiwon lafiya domin samun kulawa..

  8. Shugaban Lebanon ya tafi Washington don ganawa da Trump

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Lebanon, Joseph Aoun, ya bar birnin Beirut zuwa Washington, inda ake sa ran zai gana da shugaban Amurka Donald Trump, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta sanar.

    Ziyarar tasa na zuwa ne bayan kammala zagaye na shida na tattaunawar Lebanon da Isra'ila, wanda aka gudanar a ofishin jakadancin Amurka da ke Rome a Italiya a ranakun 13 da 14 ga watan Yuli.

    Fadar shugaban ƙasar Lebanon ta ce Aoun zai yi tattaunawa da wasu manyan jami'an Amurka kan halin da ƙasar ke ciki da kuma hanyoyin ƙarfafa yarjejeniyar tsagaita wuta, musamman a kudancin Lebanon.

    Ana kuma sa ran za a tattauna batun janye sojojin Isra'ila daga wuraren da har yanzu suke mamaye da su a Lebanon, wanda ke daga cikin manyan batutuwan da ke gaban ƙasashen biyu.

  9. Ba za mu lamunci ana tattaunawa ana kai hare-hare ba - Iran

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Iran ta ce ba za ta ci gaba da amincewa da salon gudanar da tattaunawa tare da ci gaba da kai hare-hare a lokaci guda ba, tana mai gargaɗin cewa idan Amurka ta ci gaba da yaƙin cikin kwanaki biyu ko uku masu zuwa, za ta ɗauki matakin mayar da martani mafi tsauri na ba sani ba sabo.

    Mai ba Jagoran addinin Iran shawara kan harkokin soja, Mohsen Rezaei, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi ta talabijin, inda ya ce manufar “ana tattaunawa ana kuma yaƙi” ta zo ƙarshe.

    Ya ƙara da cewa Iran tana mutunta gwamnatoci da al'ummomin duniya, amma za ta ci gaba da kai farmaki kan sojojin Amurka da sansanoninsu idan rikicin ya ci gaba.

    Rezaei ya ce Iran na nuna taka-tsantsan ne saboda tsoron rikicin ya bazu zuwa wasu yankuna, yana mai cewa hakan na iya haddasa sabbin rikice-rikice tsakanin ƙasashe daban-daban, ciki har da Turkiyya da Isra'ila, China da Taiwan, da kuma Rasha da Turai.

    A cewarsa, Iran ba ta son ganin yankin ya faɗa cikin wani babban rikici.

    Ya kuma yi kira ga al'ummomin yankin da su taimaka wajen hana rikicin ƙara kamari, yana mai cewa batun yaƙi abu ne mai matuƙar muhimmanci.

    Rezaei ya gargɗii Amurka da cewa ta yi tsammanin sabbin hare-haren makamai masu linzami idan rikicin ya ci gaba.

  10. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'ƴan ta'adda' biyu da ceto mutum uku a Benue

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Whirl Stroke tare da haɗin gwiwar jami'an tsaron al'umma na jihar Benue sun kashe wasu da ake zargin 'yan ta'adda biyu tare da ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

    A cewar sanarwar rundunar, an fara aikin ne da misalin ƙarfe 3 na safiyar ranar 16 ga Yulin 2026, inda sojojin suka bi ta Takum a jihar Taraba zuwa ƙauyukan Tse Togo da Utenge da ke kusa da sansanin Orter, inda aka ce waɗanda ake zargin 'yan ta'addan ne ke fakewa.

    "A yayin musayar wuta kuma sojojin suka samu nasarar kashe mutum biyu daga cikinsu." in ji sanarwar.

    Mutanen da aka ceto dukkaninsu mazauna ƙaramar hukumar Katsina-Ala ne in ji sanarwar.

    Rundunar ta ce wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su sun tsere daga sansanin yayin artabun.

    Sojojin sun kuma ƙwato makamai da harsasai daban-daban da kayan soji yayin samamen.

  11. Kotu ta yi watsi da ƙarar PDP ɓangaren Turaki

    ....

    Asalin hoton, @kabiruturakisan

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu shugabannin jam'iyyar PDP suka shigar domin tilasta wa hukumar zaɓe ta INEC, ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.

    Alƙali Salim Ibrahim ya yanke hukuncin cewa masu shigar da ƙarar ba su da hurumin gabatar da ƙarar. Saboda haka kotun ta ce ba ta da ikon sauraron shari'ar.

    Alƙalin ya ce masu ƙarar sun kasa tabbatar wa kotu cewa INEC ta taɓa amincewa da kwamitin riƙon ƙwaryar da suke goyon baya, ko kuma cewa suna da ikon shigar da ƙara a madadin jam'iyyar PDP.

    Shugaban kwamitin amintattu na PDP tsagin Turaki ƙarƙashin Sanata Adolphus Wabara, tare da wasu mambobin kwamitin ne suka garzaya kotu suna neman a umarci INEC ta sabunta bayananta tare da amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.

    Sun kuma buƙaci kotun ta umarci hukumar zaɓen ta wallafa sunayen shugabannin riƙon ƙwaryar a shafinta na intanet.

    Sai dai wani tsagin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya nemi shiga shari'ar tare da ƙalubalantar ikon kotun, inda ya ce shi ne shugabancin PDP halastacce, kuma masu ƙarar ba su da hurumin shigar da ita a madadin jam'iyyar.

  12. Me ya bambanta ƴansandan jihohi da 'askarawan' da gwamnoni suka samar?

    ....

    Asalin hoton, Zamfara state govt

    Ana ci gaba da tattaunawa a Najeriya kan shirin kafa rundunar ƴansandan jihohi, bayan Majalisar Dokokin tarayyar kasar ta amince da ƙudurin dokar.

    Majalisar ta amince da ƙudurin ne bayan karatu na biyu, inda aka zaɓi amfani da ƙudurin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a maimakon wanda ƴan majalisa suka gabatar tun da farko.

    Buƙatar kafa ƴansandan jihohi dai ta daɗe tana cikin abubuwan da gwamnonin ƙasar ke nema. Sun yi ta jaddada cewa rashin ikon kafa rundunar ƴansanda ta jiha na hana su ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar yankunansu.

    Tun kafin wannan yunƙuri, jihohi da dama sun riga sun kafa rundunonin tsaro na cikin gida, kamar ƴan sa-kai, ƴan banga da kuma askarawa, domin taimakawa jami'an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi.

    Sai dai akwai masu nuna damuwa cewa idan aka kafa ƴansandan jihohi, za su iya kasancewa tamkar waɗannan rundunonin da ake da su yanzu, waɗanda ake yawan zargin su da rashin ƙwarewa da kuma cin zarafin jama'a a wasu lokuta.

  13. Iran ta ce ta kai hari kan wuraren adana man Amurka a Bahrain

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Iran sun yi iƙirarin cewa sun kai hari kan wuraren ajiyar jiragen sama da tankunan adana man fetur a sansanin Sheikh Issa da ke Bahrain, wanda suka bayyana a matsayin sansanin Amurka, ta hanyar amfani da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

    A cikin sanarwar, sojojin sun kuma ce sun kai hare-hare kan gadoji da dama a Bahrain.

    Sai dai kawo yanzu, hukumomin Bahrain ko na Amurka ba su fitar da wata sanarwa ba game da girman ɓarnar da aka yi, ko kuma ko akwai waɗanda suka jikkata ko suka mutu sakamakon hare-haren.

  14. Hare-haren Amurka kan kayayyakin more rayuwar Iraniyawa laifin yaƙi ne - Iran

    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya aika wa Kwamitin Tsaro na MDD wasika inda ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Amurka ta kai kan kayayyakin more rayuwar fararen hula a Iran.

    Iravani ya ce hare-hare da ake ci gaba da kai wa wuraren fararen hula, musamman muhimman hanyoyin mota da na jirgin kasa, sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa kuma sun kai matsayin laifin yaƙi.

    Jakadan ya kuma yi gargadin cewa idan Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro ba su dauki matakin da ya dace ba, Iran za ta ci gaba da amfani da haƙƙinta da dokokin kasa da kasa suka tanada domin kare ikon ƙasarta, mutuncin yankinta, al'ummarta da muhimman muradunta na kasa.

  15. Assalamu alaikum

    Mabiya shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar, hutun ƙarshen mako.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.