Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/10/20224

Wannan shafi ne da kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/10/20224

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Nabeela Mukhtar da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin a yau. Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Albashin naira miliyan 14 nake karɓa a wata a matsayin sanata - Orji Kalu

    Kalu

    Asalin hoton, Senator Orji Uzor kalu

    Sanata mai wakiltar mazaɓar Abia ta arewa a majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce albashin naira miliyan 14 yake karɓa duk wata a matsayinsa na sanata a Najeriya.

    Sanatan ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na tashar talabijin na Channels na yau Alhamis.

    "Ana biyana albashin naira miliyan 14 ne duk wata, kuma wannan ya ƙunshi komai da komai ne."

    Sanatan ya bayyana hakan ne domin mayar da martani ga waɗanda suke ganin albashin sanatocin ya wuce misali.

  3. An tsige mataimakin shugaban ƙasar Kenya

    Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dattawa ta ƙasar Kenya ta tsige matamakin shugaban ƙasar Rigathi Gachagua.

    Shugaban majalisar ya ce sanatoci sun tabbatar da tuhume-tuhume biyar daga cikin 11 da aka gabatar a kan tsohon mataimakin shugaban ƙasar, waɗanda duka ya ƙaryata.

    Daga cikin laifukan akwai raba kan al'umma da saɓa dokokin aikin ofis ɗinsa da kawo tsaiko a aikin tattara bayanan sirrin ƙasar.

    Rigathi Gachagua mai shekara 59 ya yi iya bakin ƙokarinsa domin hana tsigewar, sannan ko a yammacin yau lauyansa ya ce ba zai samu halartar zaman majalisar ba saboda yana kwance a asibiti, har ya buƙaci a ɗage zaman, amma sanatocin suka ƙi amincewa, inda suka cigaba da tattaunawa ba tare da yana nan ba, har suka kai ga tsige shi.

    Sai dai yana da damar ƙalubalantar tsigewar a kotu.

  4. An kwantar da mataimakin shugaban ƙasar Kenya da ke fuskantar tsigewa

    Kenya

    Asalin hoton, Reuters

    Mataimakin shugaban ƙasar Kenyan Rigathi Gachagua, wanda yake fuskantar tsigewa ya kwanta rashi lafiya a asibiti.

    A wannan daren ne ya kamata Rigathi Gachagua ya bayyana a gaban majalisar dattawan ƙasar domin amsa wasu tambayoyi, amma sai lauyansa ya ce an kwantar da shi a asibiti.

    "Mataimakin shugaban ƙasar Kenya ba shi da lafiya, yana fama da jinya sosai, yanzu haka yana kwance a asibiti," in ji Paule Muite.

    Tuni majalisar ta yi watsi da batun neman a ɗage zaman majalisar, inda ta cigaba da zamanta ba tare da shi ba.

  5. Gwamnatin Najeriya ta buƙaci mutane su tashi daga yankunan da ake fargabar ambaliya

    Ambaliya

    Asalin hoton, BBC/GIFT

    Gwamnatin Najeriya ta shawarci ƴan Najeriya da suke zaune a gaɓar tekuna da bar yankunan cikin gaggawa.

    Darakta-janar na hukumar albarkatun ruwa, Umar Mohammed ne ya yi wannan gargaɗin, inda ya ce ruwan da ke tekun Benuwe ya kai matakin ambaliya saboda ƙaruwar mamakon ruwan sama, kamar yadda shafin intanet na tashar Channels ya ruwaito.

    Ya kuma yi kira ga waɗanda suke zaune gaɓar tekun Neja da suma su bar yankin, domin hukumomin dam Kainji da Jebba suna aikin kare aukuwar ambaliya.

    Shugaban hukumar ya yi kira ga ƴan Najeriya su ba su haɗin kai domin rage ta'azzarar lamarin.

  6. An kashe sojojin Isra'ila biyar a kudancin Lebanon

    IDF

    Asalin hoton, EPA

    Rundunar tsaron Isra'ila IDF ta ce an kashe mata sojoji biyar a wata gwabzawa da aka yi a kudancin Lebanon a jiya Laraba.

    A wata sanarwa da IDF ta fitar, ta ce akwai kuma wasu sojojinta guda tara da suka jikkata a wurare daban-daban a Lebanon da Gaza daga ranar Laraba zuwa yau Alhamis.

  7. APC ce take haɗa rikici a jam'iyyun adawa – NNPP

    NNPP

    Asalin hoton, NNPP/Facebook

    Jam'iyyar NNPP ta ce jam'iyyar APC mai mulki ce take haɗa rikice-rikice a jam'iyyun adawa domin samun sauƙi a zaɓen 2027.

    Shugaban jam'iyyar NNPP, Ajujij Ahmed ne ya bayyana hakan a wurin ƙaddamar da yaƙin zaɓen gwamnan jihar Ondo a Akure, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    "APC ta yi duk abin da za ta iya yi ne domin samun nasara a zaɓen 2027. Akwai alama a zahiri cewa suna haɗa rigingimu a jam'iyyun adawa domin a dagula musu lissafi kafin zaɓen."

    Shugaban ya ce Bola Tinubu ya shirya miƙa mulki a zaɓen 2027, inda ya ce NNPP na ƙokarin haɗa gwiwa da wasu jam'iyyun domin hada ƙarfi da ƙarfe domin fuskantar zaɓen na 2027.

  8. Fashewar tankar mai a Jigawa: Ƙungiyar Sevilla ta Spain ta aike da saƙon jaje

    Sevilla

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Spain ta yi wa ƴan Najeriya, musamman ƴan jihar Jigawa ta'aziyar rasuwar mutane a sanadiyar fashewar tankar mai a jihar Jigawa.

    Ƙungiyar ta Sevilla ta bayyana hakan ne a shafukanta na sadarwa, inda ta rubuta, "muna aika jajenmu da ta'aziya da addu'a ga duk waɗana abin da ya faru a jihar Jigawa ta Najeriya."

    Fashewar tankar man ta yi ajalin aƙalla mutum 153, sannan da dama suka jikkata.

  9. Netanyahu ya ce akwai sauran yaƙi bayan kashe shugaban Hamas

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Firaiministan Isra'ila, Benjamin Natanyahu ya ce kashe shugaban Hamas, Yahya Sinwar ba zai kawo ƙarshen yaƙin da suke yi a Gaza ba.

    Netanyahu ya ce Sinwar ne ya shirya harin nan na 7 ga Oktoba da aka yi a Isra'ila, wanda ya bayyana da "kisan kiyashi mafi muni da aka yi wa mutanemu bayan na yaƙin duniya na biyu."

    Ya ce, "aikinmu bai ƙare ba," domin Isra'ila za ta cigaba da yaƙi ne sai waɗanda aka yi garkuwa da su sun dawo.

    "Sinwar ya tarwatsa rayuwarmu, amma yanzu da ya rasu, Hamas ba za ta iya samun ƙarfin iko a zirin ba," in ji shi, sannan ya ce wannan dama ce ga mutanen zirin domin su ƴantar da kansu.

    "Dawowar mutanenmu da aka yi garkuwa da su ne zai kawo ƙarshen yaƙin," in ji shi.

  10. Ranar 8 ga Nuwamban 2025 za a yi zaɓen gwamnan Anambra - INEC

    INEC

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta sanya ranar 8 ga Nuwamban 2025 domin gudanar da zaɓen jihar Anambra.

    Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a yau Alhamis a shafukanta na sada zumunta.

    "Hukumar ta amince da ranar Asabar, 8 ga Nuwamban 2025 domin gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra na 2025.

    "Domin cika ƙa'idar fitar da sanarwar da zaɓen na kwana 260 kafin zaɓe, za a wallafa sanarwar zaɓen a ranar 13 ga Nuwamban 2024. Jam'iyyu za su gudanar da zaɓukan fid-da-gwani ne tsakanin 20 ga Maris zuwa 10 ga Afrilun 2025, sannan za a buɗe shafin sanya sunayen ƴantakara a ranar 18 ga Afrilu zuwa 12 ga Mayun 2025, sannan a fitar da sunayen ƴantakara na ƙarshe a ranar 9 ga Yunin 2025.

    "Za a fara yaƙin neman zaɓe a ranar 11 ga Yunin, sannan a gama a ranar 6 ga Nuwamba, sannan a gudanar da zaɓe a ranar 8 ga Nuwamban 2025," kamar yadda sanarwar ta nuna.

  11. Zamfara ta kafa kwamittoci shida domin samar da 'sabuwar Zamfara'

    Zamfara

    Asalin hoton, Sulaiman Bala Idris

    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya nanata ƙudurinsa na tabbatar da cewa Zamfarawa sun mori romon dimokuraɗiyya.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya kafa kwamitoci guda shida daban-daban a fadar gwamnatin domin tabbatar da tsare-tsare da shirye-shiryen samar da sabuwar jihar.

    A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce kwamitocin da aka kafa sun haɗa da kwamitin yaƙi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi da na kula ƙasa sufiyo da na jin daɗin mutane da na tsara cigaban jihar da sauransu.

    Gwamnan ya ce an bi a tsanaki ne wajen zaƙulo waɗanda za su yi wannan gagarumin aiki.

  12. Fashewar tanka: Atiku ya yi kira a koma sufurin mai ta jiragen ƙasa

    Atiku

    Asalin hoton, Twitter

    Tsohon shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira da a duba yanayin hanyoyin sufurin albarkatun man fetur a Najeriya.

    Atiku ya yi wannan kiran ne a shafukansa na sada zumunta a lokacin da yake ta'aziyar rasuwar waɗanda ibtila'in fashewar tankar mai ya rutsa da su a Jigawa.

    A cewarsa, "Ina alhini da jimami tare da ta'aziyya ga iyalai da gwamnati da mutanen Jigawa bisa rasuwar da mutane suka yi a sanadiyar fashewar tankar mai a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a jihar Jigawa. Wannan ibtila'in, ba shi ba ne farau a ƙasar nan. Ina ganin lokaci ya yi da za mu sauya salon sufurin man fetur.

    "Ya kamata mu gwada wasu hanyoyin kamar amfani da jiragen ƙasa domin sufurin albarkatun man fetur. Sannan akwai buƙatar a ba direbobin irin motocin nan horo na musamman," in ji shi.

  13. Ɗan ƙunar bakin wake ya kashe sojoji da fararen hula a Mogadishu

    Somalia

    Asalin hoton, AFP

    Aƙalla mutum bakwai ne, ciki har da sojoji da fararen hula aka kashe, sannan wasu shida suka jikkata bayan wani ɗan ƙunar bakin wake ya tayar da bam a wani shagon sayar da shayi a kusa da kwalejin horar da ƴansanda da ke yankin Hamar Jajab da ke Mogadishu a ranar Alhamis, kamar yadda ƴansanda suka tabbatar.

    Ganau daga babban birnin ya bayyana wa BBC ta wayar tarho cewa ɗan ƙunar bakin waken ya hari shagon shayin ne kasancewar mutane suna taruwa.

    Ganau ɗin ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun zo wajen, sannan ana cigaba da gudanar da bincike.

    Tuni ƙungiyar al-Shabaab ta Somalia, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda ta ɗauki nauyin kai harin, inda ta ce ta kai harin ne a kan kwalejin horar da ƴansandan.

  14. Najeriya ta samu tallafin allurar riga-kafin maleriya guda miliyan ɗaya

    Maleriya

    Asalin hoton, Reuters

    Najeriya ta karɓa tallafin allurar riga-kafin maleriya 846,000 samfurin R12/Matrix-M daga hukumar kula da riga-kafi ta duniya wato GAVI domin yaƙi da cutar maleriya.

    "Riga-kafin zai taimaka mana wajen yaƙi da cutar maleriya, da rage mace-mace a tsakanin ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara biyar da kashi 13, da rage zuwa asibiti da kashi 22," in ji Dokta Muyi Aina, babban daraktan hukumar kula da lafiya a matakin farko.

    Kamar yadda ƙididdigar hukumar lafiya ta duniya WHO ta nuna, Najeriya ce kan gaba a cutar maleriya a duniya, inda ƙasar ke da kashi 27 na cutar a duniya, kuma take kan gaba wajen yawan mace-mace a sanadiyar cutar.

    Za a fara riga-kafin ne a watan Nuwamba a jihohin Kebbi da Bayelsa, ina cutar ta fi ƙamari, inda za a yi wa ƙananan yara masu wata biyar zuwa 16, inda za a musu allura huɗu domin kariya.

    Za a faɗaɗa cutar zuwa jihohi 19 a shekarar 2025, sannan kuma akwai shirin ba masu raino da shugabannin al'umma da ma'aikatan jinya.

    WHO ta amince da riga-kafin R12.Matriz-M ne a watan Disamban 2023 domin amfani da shi ga ƙananan yara.

  15. Wani bincike ya tabbatar da sakaci a ayyukan hukumar leƙen asirin Amurka

    US

    Asalin hoton, EPA

    Wani sabon rahoto ya ce akwai buƙatar hukumar leƙe asirin Amurka ta magance kura-kuren da ta ke tafkawa domin sake faruwar irin yunƙurin kisan da aka yi wa Donald Trump a wajen yaƙin neman zaɓe.

    Wani rahoton bincike mai zaman kansa da aka gudanar a kan harbin na ranar 13 ga watan Yuli ya ce hukumar ta yi sakwa-sakwa da aikin ta.

    Rahoton da aka fitar ranar Alhamis ya yi kiran a gaggauta canza shugabancin hukumar leƙen asirin Amurkan, saboda sakacin da aka riƙa samu a bakin aikin su, wanda har ya kai ga kai hari a kan ɗan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican.

    Tuni dai hukumar leƙen asirin Amurkan ta amsa cewa an samu gazawa a ayyukan ta, kuma shugabanta ya yi murabus mako guda bayan harin da aka kai wa Donald Trump.

    A martanin da ta bayar a yau Alhamis, muƙaddashin shugaban hukumar, Ronald Rowe ya ce za su yi kyakkyawan nazari a kan abubuwan da rahoton ya ƙumsa.

    Ya ce "Mun inganta tsarin aikin mu, da hanyoyin isar da saƙonni da kuma ƙara matakan tsaro a kan tsohon shugaban ƙasar.''

    A cikin rahoton wanda jami'an tsaro a matakin jihohi da na tarayya suka haɗa, an yaba da ƙoƙarin jami'an hukumar leƙen asirin masu sadaukar da ransu wajen kare manyan jami'an gwamnati, amma an soki sakaci da ake samu daga ɓangaren shugabannin su.

  16. Bangladesh ta bayar da izinin kama tsohuwar firaminista Hasina

    Hasina

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu ta musamman a Bangladesh ta bayar da izinin a kama tsohuwar firaiministar ƙasar da ta yi gudun hijirah Sheikh Hasina saboda zargin ta da hannu a kisan da aka yi a lokacin zanga zangar da ta yi sanadin hambarar da gwamnatinta.

    Babban mai shigar da ƙara na kotun hukunta manyan laifuka a ƙasar, Mohammad Tajul Islam, ya ce alƙalai sun bayar da umarnin ta bayyana gaban kotu a watan Nuwamba mai zuwa domin ta fuskanci tuhume tuhumen da aka mata akan laifukan take hakkin dan adam.

    Ms Hasina ta tsere zuwa India bayan juyin juya halin da aka yi a watan Yuli da Augusta, wato bayan ta shafe shekaru 15 a kan mulki wanda ya janyo mata zarge zargen take hakkin dan adam.

    Masu suka sun ce kotun wadda gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar ta kafa bata da gogaggun alƙalai waɗanda suka ƙware a ɓangaren shari'ar ƙasa da ƙasa.

  17. Isra'ila na ƙoƙarin tantance ko ta kashe jagoran Hamas Yahya Sinwar

    Yahya Sinwar

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana bincike domin tabbtar da raɗe-raɗin kisan jagoran ƙungiyar Hamas, Yahya Sinwar a Gaza.

    Sanarwar da rundunar sojin Isra'ilan ta fitar ta ce har yanzu ba a gama tantance ko su waye ''Ƴan ta'adda uku'' da dakarun suka kashe ba.

    "Akwai ƴan ta'adda da aka kashe a cikin wani gini, kuma babu alamar akwai mutanen da aka yi garkuwa da su a cikin ginin.'' inji sanarwar.

  18. Tarayyar Turai za ta ƙara yawan baƙin haure da take mayar wa ƙasashensu

    Ursula von der Leyen

    Asalin hoton, Reuters

    Shugabar ƙungiyar tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce akwai darasin da ƙungiyar za ta koya daga tsarin ƙasar Italiya game da baƙin haure da ke kwarara ta Albania.

    Wannan na zuwa ne gabanin taron shugabbanin ƙungiyar mai mabobi 27, wanda zai mayar da hankali kan matsalar kwararar baƙin haure.

    A saƙon da ta aikewa shugabannin kafin taron da za a yi a birnin Brussels, shugabar ta ce za su gabatar da wani ƙudirin doka da zai bayar da damar mayar da baƙin haure ƙasashen su.

    A farkon makon nan Italiya ta fara wani shiri na tura baƙin haure Albania domin mayar da su ƙasashen su.

    An tura wasu maza 16 gaɓar tekun Shenjin ta Albania a ranar Laraba amma bayan isar su wajen sai aka gano biyu daga cikin su ƙananan yara ne, ga kuma wasu biyu da ke cikin matsanancin ciwo, lamarin da ya sa aka yanke shawarar mayar da su Italiya.

    Ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai sun fara tsara yadda za su mayar da baƙin haure ƙasashen su na asali, musamman waɗanda suka fito daga ƙasashe masu tasowa.

    A ranar Laraba gwamnatin Jamus ta ce tana nazari kan tsarin hana mafakar siyasa ga waɗanda suke nema daga Uganda.

  19. Shugaban Mali Assimi Goita ya zama babban Janar

    Assimi Goita

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Mali, Kanal Assimi Goita ya samu ƙarin girma zuwa muƙamin babban janar a rundunar sojin ƙasar.

    Wannan mataki ya ruruta raɗe-raɗin da ake yi cewa gwamnatin sojin na shirin yadda zai ci gaba da mulkin ƙasar bayan kammala wa'adin da aka tsara tun da farko.

    Majalisar ministocin ƙasar ce ta amince da ƙarin girman a ranar Laraba, inda ta kuma amince da naɗin sabbin masu muƙamin Kanal da laftanar-janar da kuma manjo-janar.

    Kafin Assimi Goita dai mutum biyu ne suka taɓa riƙe wannan muƙami a lokacin da suke kan ragamar shugabancin ƙasar bayan ƙwace mulki, wato Janar Moussa Traoré da kuma Janar Amadou Touré, waɗanda suka mutu a 2020.

    Ƙara wa Assimi Goita girma zuwa matsayin Janar ya bashi ikon ɗaukar ƙwararan matakai a kan tsaron ƙasar da kuma sauran harkokin rayuwar ƙasar yayin da ya ke ci gaba da zama shugaban riƙon ƙwarya.

  20. Gwamnatin Najeriya da ƴan ƙwadago sun tashi taro babu matsaya kan tsadar rayuwa

    Taron ƙwadago da gwamnati

    Asalin hoton, The Cable

    Ba a cim ma matsaya ba a taron tattaunawa tsakanin haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin Najeriya game da tsadar rayuwa a ƙasar da ƙarin farashin mai ya haifar.

    Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito shugabannin ƙungiyar ma'aikata ta NLC da ta 'yankasuwa TUC sun gana da wakilan gwamnatin tarayya a ofishin sakataren gwamnati da ke Abuja ranar Alhamis.

    Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris, ya shaida wa manema labarai a ƙarshen taron cewa taron alama ce da ke nuna yadda gwamnati ta mayar da hankali wajen tattaunawa da ƴan ƙwadago a kan batun.

    Sai dai kuma ministan ya ƙi faɗar abubuwan da aka tattauna a wajen taron, yana mai cewa gwamnati ba za ta zura ido har sai abubuwa sun lalace ba sannan ta gana da ƙungiyoyin ƙwadagon.

    “An tattauna abubuwa da dama amma kamar yadda na faɗa tun farko, har yanzu ana cikin sasanci ne, kuma wannan harka ce da ba za a iya gamawa a zama ɗaya ba, kuma kawo yanzu ba mu cim ma wani abu da za a iya faɗa wa ƴan Najeriya ba," in ji shi.

    Ƴan Najeriya da dama sun bayyana rashin jin daɗinsu kan ƙarin farashin man fetur da aka yi kwanan nan a ƙasar, da kuma tsadar rayuwa da ake fama da ita.