An gudanar da jana'izar babban kwamandan Iran a Tehran
Dandazon mutane ne suka taru a Tehran, babban birnin Iran domin halartar jana'izar Abbas Nilforoushan, wani babban kwamandan dakarun juyin-juya hali na Iran.
An yi imanin cewa an kashe Nilforoushan ne tare da tsohon shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah a wani hari da Isra'ila ta kai Lebanon ranar 27 ga watan Satumba.
An kuma yi wasu jana'iza guda biyu a Iraqi a jiya Litinin kafin mayar da gawar zuwa ƙasarsa ta haihuwa.
Kwamandan dakarun juyin-juya hali, Esmail Qaani, shi ma ya halarci jana'izar kamar yadda gidan talabijin na Iran ya nuna, abin da ya kawo karshen raɗe-raɗen wajen da yake.
A ranar Juma'a, dakarun juyin-juya halin suka sanar da gano gawar Nilforoushan, inda aka yi jana'izar binne shi a garinsa ta haihuwa na Isfahan a Iran, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.