Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Nabeela Mukhtar

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muku ƙarshen wannan shafin a wannan rana ta Talata. Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa asuba ta gari.

  2. 'Babu hannun Ukraine wajen taimaka wa ƴan tawaye a Mali'

    Ukraine ta ƙaryata zarginta da ake yi da tallafa wa masu tada ƙayar bayan ƙasar Mali da jirage marasa matuƙa domin cigaba da yaƙi da sojojin ƙasar da ma sojojin haya da suke samun goyon bayan Rasha.

    Wannan na zuwa ne bayan jaridar Le Monde ta Paris ta ruwaito cewa jirage marasa matuƙa daga Ukraine ne ƴan tawayen Tuareg suke amfani da su.

    Gwamnatin sojin Mali ta yanke alaƙa da Faransa wadda ta raine ta a shekarar 2022, ta koma alaƙa da Rasha, inda ta ce ta yi hakan ne domin yaƙi da matsalar tsaro a arewacin ƙasar.

    Sai dai har yanzu yaƙin na cigaba da ruruwa.

    Suma ƙasashen Nijar da Burkina Faso da suke maƙwabtaka da Mali, kuma dukkansu suke ƙarƙashin mulkin soji, sun zargi Ukraine da taimakon ta'addanci a ƙasashensu.

    Amma ministan harkokin wajen Ukraine ya bayyana a wata sanarwa cewa ƙasarsa, "ta yi watsi da zargin taimakon ta'addanci na cewa Ukraine na taimaka wa ƴan ta'adda da makamai irin su jirage marasa matuƙa a Mali."

  3. Uganda za ta gina titin jirgin ƙasa mai amfani da lantarki

    Uganda ta ce ta rattaba hannu a yarjejeniyar dala biliyan uku da wani kamfanin ƙasar Turkiyya don gina hanyar jirgin Ƙasa mai amfani da lantarki wadda za ta haɗa ƙasar da maƙwabciyarta Kenya.

    Hanyar za ta fara daga Kampala babban birnin Uganda zuwa Malaba da ke kan iyaka da Kenya sama da kilomita ɗari biyu da saba'in.

    Wakilin BBC ya ce:Ministan Sufuri Katumba Wamala ya ce za a kammala aikin hanyar cikin shekara huɗu, kuma za ta taimaka wajen rage jinkirin da ake fuskanta wajen dakon kaya daga gaɓar tekun Indiya a Mombasa.

    Wani jami'i ya ƙara da cewar hanyar jirgin ƙasa za ta rage fiye da rabin kuɗaɗen da ake kashewa wajen fiton kaya.

    Yarjejeniyar Ugandan ta biyo bayan yarjejeniya tsakanin wani kamfanin Turkiyya (Yapi Merkezi) da Tanzaniya don gina hanyar jirgin ƙasa mai amfani da lantarki tsakanin Dodoma babban birnin ƙasar da Dar es salaam.

  4. Masana sun ce akwai buƙatar sabunta kayayyakin babban layin lantarki

    A Najeriya masana kan harkar wutar lantarki sun yi kira a sabunta kayayakin babbar cibiyar wutar lantaki ta kasar.

    Sun ce yawan katsewar wutar lantarkin da ake fuskanta na da alaƙa ne da rashin sauya kayyakin babbar cibiyar wutar lantakin ƙasar.

    A jiya ne cibiyar ta fuskanci tangarɗa, abin da kuma ya jefa mutanen ƙasar cikin duhu.

  5. Kawu Sumaila ya zargi ƴan siyasa da ƙarfafa masu shaye-shayen ƙwayoyi

    Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta kudu a majalisar dattawa, ya zargi ƴan siyasa, musamman ƴan majalisa da ƙarfafa shaye-shayen ƙwayoyi a tsakanin matasa.

    Ya ce ƴan siyasa suna sayo wa matasan ƙwayoyi, sannan suna ƙarfafa musu gwiwar ta'ammuli da su domin samun damar yi musu dabar siyasa musamman a lokacin zaɓe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

    Kawu ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake nasa bayanin a kan ƙudurin da Sanata Rufa'i Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya ya gabatar, mai taken, "dokar kafa cibiyar hana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da gyara tunanin mashaya da sauran abubuwa masu alaƙa," a yau Talata.

    "Yanzu da nake wannan maganar, yawancin ofisoshinmu da gidajenmu ba za a rasa ƙwayoyi ba," in ji Kawu.

    "Na san wasu jagororin siyasa da suke ƙarfafa gwiwar masu shaye-shaye a Najeriya. Don haka akwai buƙatar mu ɗauki wannan batu da muhimmanci."

    Ya ƙara da cewa, "mutum nawa ne a cikinmu za su iya rantse wa Ƙur'ani ko Baibul cewa ba sa ƙarfafa wa masu shaye-shaye a mazaɓunsu?"

    A ƙarshe ya yi kira da a riƙa yin gwajin shaye-shaye ga duk wani wanda yake son tsayawa takara.

  6. Mataimakin shugaban Hezbollah ya ce tsagaita wuta ce hanyar maslaha da Isra'ila

    Mataimakin shugaban ƙungiyar Hezbullah a Lebanon, ya ce tsagaita wuta ce hanyar warware rikici da Isra'ila.

    Sai dai kuma Naim Qassem ya faɗa a cikin wani jawabi da ya yi ta bidiyo cewar ƙungiyar wadda Iran ke goyon baya a shirye take ta kai hari a dukkan yankunan Isra'ila.

    Ya ce kisan da aka yi wa galibin shugabannin ƙungiyar Hezbullah na baya-bayan nan abin takaici ne, amma har yanzu mayaƙansa za su iya ramuwar gayya mai raɗaɗi.

    Wakilin BBC ya ruwaito cewa, Isra'ila ta ce burinta shi ne rusa ƙarfin Hezbollah, ta harba rokoki da makamai masu linzami a iyakoki hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce wani kashi na al'ummar Lebanon na ficewa daga ƙasar biyo bayan umarnin da Isra'ila ta yi. Sama da mutane miliyan ɗaya aka tilastawa tserewa daga muhallansu.

  7. Amurka ta yi barazanar katse tallafin makamai ga Isra'ila kan Gaza

    Amurka ta rubuta wa gwamnatin Isra'ila wasiƙa inda ta ba ta kwana 30 da ta ƙara yawan kayan agajin da ake kai wa Gaza ko kuma ta katse tallafin makaman da take ba ta.

    Wasiƙar dai ita ce wani saƙo mafi zafi da gwamnatin Biden ta taɓa aikewa zuwa babbar ƙawarta wato Amurka tun bayan fara yaƙi a Gaza shekara guda.

    Takardar wadda aka aike da ita kwana biyu ta samu sa-hannun sakatare ƙasashen wajen ƙasar, Anthony Blinken da sakataren harkokin tsaro, Lloyd Austin, ta ce Amurka na cikin damuwa kan taɓarɓarewar yanayin jinƙai a Gaza.

    Har wa yau, wasiƙar ta ƙara da cewa Isra'ila a watan da ya gabata ta ƙi amince wa ko kuma ta daƙile kaso 90 na harkokin jinƙai arewacin Gaza.

    Wasiƙar ta kuma ambaci umarnin da Isra'ilar ke bai wa jama'a na su bar yanki inda ta ce umarnin ya tilasta mutane fiye da miliyan 1.7 yin tururuwa zuwa bakin ruwa inda rayuwarsu ke fuskantar barazana kamuwa da cutukan da ka iya sa su rasa rai.

    Daga ƙarshe wasiƙar ta bai wa Isra'ilar wa'adin wata guda na "ɗaukar matakan gaggawa wajen magance matsalar".

    "Dole ne Isra'ila ta ta fara aiki daga yanzu zuwa kwana 30 wajen ɗaukar ƙwararan matakai domin bai wa kayan agaji damar shiga", inda ta ƙara da cewa gaza yin hakan "na da tasiri kan tsare-tsaren Amurka."

  8. Ba zan ce uffan ba kan dambarwar da ke faruwa a jam'iyyar NNPP ba - Kwankwaso

    Ɗantakarar shugabancin ƙasar Najeriya, a jam'iyyar NNPP kuma jagoran kungiyar Kwankwasiyya , Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ba zai magana dangane da dambarwar da ke cikin jam'iyyar tasu a Kano ba.

    Kwankwaso wanda ya shaida wa ƴan jarida hakan bayan wani taron karɓar ƴan jam'iyyar APC da suka sauya sheƙa zuwa NNPP a gidansa da ke birnin kano, ya ce "ba na son na tattauna a kan wannan batun. Ka da ku tsoma ni a cikin al'amarin da bai kamata na shiga ciki ba. Shugaban jam'iyya ya riga ya yi magana saboda haka za ku iya tuntuɓar sa."

    Rikicin jam'iyyar NNPP a Kano dai ya janyo dakatar da sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol.

    Dakatarwar ta zo ne jim kaɗan bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jogoranci sasanci tsakanin sakataren gwamnatin, Abdullahi Bichi da wasu ƴan mazaɓarsa.

    Baffa Bichi dai ya nesanta kansa ne daga zargin kafa wata ƙungiya mai suna "Tsaya da Ƙafarka" da ke fafutukar raba kan gwamna Abba Kabir Yusuf da ubangidansa, Rabi'u Musa Kwankwaso.

  9. Isra'ila ta tilasta Falasɗinawa zaɓe tsakanin yunwa da hijra - Amnesty

    Ƙungiyar Amnesty International mai kare haƙƙin ɗan'adam ta ce ya kamata "Isra'ila ta ƙyale shigar da kayan agaji da suka haɗa da abinci da man fetur zuwa Gaza ba tare da wata matsala ba kuma cikin gaggawa".

    A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, shugabar Amnesty International a Gabas ta Tsakiya da Afirka ta Yamma, Heba Morayef ta ce an tilasta mutane "zaɓe tsakanin yunwa da gudun hijra, sannan kuma ana ta kai hare-hare a gidajensu da titunan da suke yawo a kai".

    Morayef ta ƙara da cewa ƙungiyar ta samu rahotanni da ke nuna yadda ƴan gudun hijra a sansanin Jabalia "ke cikin tsoron ka da a harbe su idan suka bar gidajensu domin neman bugun fulawa."

  10. CAF ta ɗaga wasan Najeriya da Libya

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, CAF ta ɗage wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da tawagar ƙasar Libya, wanda ya kamata a buga yau Talata.

    Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ba za a fafata wasan ba, kamar yadda aka shirya fafatawa a daren yau.

    An shirya fafata wasan ne na rukunin D a filin wasa na Martyrs of Benna da ke Benghazi, kafin tsaikon tarba tawagar Najeriya a ƙasar ya haifar da ce-ce-ku-ce, har ƴan wasan Najeriya suka koma gida.

    Wannan matakin na CAF ya kwantar da fargabar da ake yi na ƙasar da za a ba nasarar a wasan, inda wasu magoya bayan wasan Super Eagles suka yi fargabar za a ba Libya nasara a wasan da ci uku da nema, kamar yadda ake yi idan abokin kara wa bai zo ba.

    CAF ta ce ta tura lamarin zuwa kwamitin da abin ya shafa domin ɗaukar matakin da ya dace, tare da sanar da ranar da za a fafata wasan.

  11. Isra'ila ba za ta samu galaba a kanmu ba - Sheikh Naim Qassim

    Mataimakin sakatare janar na ƙungiyar Hezbollah, Sheikh Naim Qassem ya gargaɗi Isra'ila cewa hanya ɗaya tilo da za a samu sulhu ita ce tsagaita wuta.

    Sheikh Naim ya ce "Hezbollah na da damar kare kanta ta hanyar kai hare-hare duk inda take son kaiwa" tunda dai Isra'ila ce ke kai wa Lebanon hare-hare.

    Ya ƙara da cewa Isra'ilawa da ke arewacin Isra'ila za su ci gaba da fuskantar barazanar Hezbollah idan dai har Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon da Gaza, inda ya ƙara da cewa "hanyar warware al'amarin ita ce tsagaita wuta....ba za a iya samun galaba a kan Hezbollah ba saboda an shigo gonarmu ne".

    Masana dai na alaƙanta jawabin Sheikh Na'im da yadda wasu ƴan ƙasar Lebanon ke nuna tsoronsu ga yaƙin, inda ake tunanin an yi jawabin ne domin tausasa su.

    Mataimakin sakatare janar ɗin ya kuma ja hankalin ƴan ƙsar cewa idan har Isra'ila ta samu nasara a kan Hezbollah to lallai za ta sauya Lebanon ne da ma yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.

  12. Libya za ta shigar da Super Eagles ƙara

    Hukumar kwallon kafa ta Libya ta yi Allah wadai da matakin da Hukumar kwallon Kafa ta Najeriya ta ɗauka na fasa buga wasa na biyu na neman gurbibn gasar cin kofin nahiyar Afrika.

    Ta yi ƙorafin hukumomin Najeriya ba su nuna musu dattaku ba a wasan da suka yi a Najeriya, tare da cewa halin da 'yan waswan Najeriya suka shiga bai kai kwatankwacin wanda 'yan wasanta suka shiga ba a Najeriyar a makon jiya.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ɗau alwashin shigar da ƙarar Super Eagles kan matakin da ta ɗauka na komawa ƙasarta da fasa buga wasan.

    Ta ce Najeriya ta ja ta sabawa magoya bayanta da suka shirya ganin wasan da aka tsara yi a yau, hakan ya sa ta baiwa magoya bayan Libya hakuri cikin sanarwar.

  13. An samu ragin masu ƙetarawa zuwa yankin Turai

    Hukumar kula da kan iyakokin Tarayyar Turai ta ce an samu raguwar kashi 42 cikin dari na yawan baƙin hauren da ke yunƙurin tsallakawa ƙasashen Turai ta hanyar da ba ta dace ba a watanni tara na farkon wannan shekara.

    Hukumar ta ƙara da cewa an samu raguwar kashi 79 a cikin dari a hanyoyin yammacin Balkan, yayin da aka samu raguwar kashi 64 cikin dari a Bahar rum.

    Yayin da da ƙasashe da suka haɗa da Italiya da Girka suka ƙaddamar da tsauraran matakan hana tsallakowa daga Libiya da Tunisiya.

    Sai dai hukumar ta kara da cewar tsallakawa Turai ba bisa ƙa'ida ba ya karu da kashi uku a iyakokin gabashin Tarayyar Turai daga Poland sakamakon yaƙi a makociyarta Ukraine.

    Italiya ta zamo ƙasa ta farko da ta mayar da ƴan ciranin da aka kama a Bahar Rum zuwa cibiyoyin tantancewa a Albania.

    Wakilin BBC ya ce shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, babban taron EU a wannan makon zai duba sabbin tsauraran matakai da za su bayar da damar hanzarta mayar da bakin haure.

  14. Mata da yara aka fi kashewa a arewacin Lebanon - MDD

    Ofishin kare hakkin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya samu rahotannin da ke cewa cikin mutum 22 da aka kashe a wani hari da Isra'ila ta kai ƙauyen Aitou a arewacin Lebanon, sun kasance mata da yara.

    Mai magana da yawun MDD Jeremy Laurence ya ce mata 12 da yara biyu na cikin waɗanda aka kashe.

    Ya ce an ruguza wani gini mai hawa huɗu, wanda ya ce abin damuwa matuka musamman ga mutunta dokokin jin-kai na ƙasa da ƙasa.

    Ya kuma yi kira da a gudanar da bincike kan abin da ya faru.

  15. An yi wa yara sama da 90,000 riga-kafin Polio a Gaza

    Kusan yara 93,000 ne ƴan ƙasa da shekara 10 aka yi wa allurar riga-kafin polio a ranar Litinin, a cewar hukumar kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (Unrwa).

    Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita wuta na ɗan wani lokaci domin ba wa jami'ain lafiya damar yin riga-kafin bayan Gaza ta tabbatar da ɓullar cutar polio karon farko cikin shekara 25 a watan Agusta, abin da ya janyo shanyewar ɓarin jikin wani jariri ɗan wata goma.

    An fara kashi na biyu na riga-kafin ne a ranar Litinin, sai dai wani harin Isra'ila ya faɗa wa wata makarantar da aka yi niyyar amfani da ita don yin riga-kafin, abin da ya jawo mutuwar mutum 22.

    A wata sanarwa da Unrwa ta fitar a shafin X, ta ce: "Ba za mu iya bai wa yara riga-kafi a wurin da ke cike da bama-bamai ba. Ya kamata dukkan ɓangarori a rikicin sun mutunta yarjejeniyar da aka amince da ita na ɗan wani lokaci domin a samu damar yin riga-kafin."

  16. Hotunan harin da Isra'ila ta kai ƙauyen Aitou na Lebanon

    BBC ta samu wasu hotuna na wani wuri da Isra'ila ta kai hari ta sama ranar Litinin a arewacin Lebanon.

    An kashe mutane aƙalla 21 tare da jikkata takwas ranar Litinin, a hari a ƙauyen Aitou wanda mafi yawan mazauna wurin suka kasance Kiristoci.

    Yanzu dai an fara aikin share wurin a yau Talata.

  17. Google ya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar bunƙasa ayyukan AI

    Kamfanin Google ya rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya ta amfani da ƙananan injinan makamashin nukiliya don samar da ɗimbin makamashin da ake buƙata don bunƙasa ayyukan ƙirƙirariyar basira ta AI.

    Wannan yarjejeniya ce tsakanin Google da wani kamfani mai suna Kairos Power wanda ya zurfafa bincike kan ƙera kananan na'urorin da ke sarrafa makamashin nukilya.

    Suna shirin ƙera injina guda bakwai, amma sai bayan sun samu izini daga hukumomin Amurka.

    Kamfanonin fasaha suna ƙara karkata akalarsu zuwa makamashin nukiliya don haɓaka manyan cibiyoyin gudanar da ayyukan AI.

  18. MDD na fatan ci gaba da kai agajin abinci Gaza duk da wahala da ake ciki

    Ma'aikatan jin-kai na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce suna fatan ƙarin motoci 30 ɗauke da kayan abinci za su shiga Gaza yau Talata.

    Sun ce wuraren rarraba abinci da dama na aiki a wasu yankuna, duk da cewa birnin Jabalia ya kasance mai wahalar kai wa saboda ci gaba da ɓarin wuta da Isra'ila ke yi, wanda ta ce tana yi ne don ruguza mayaƙan Hamas waɗanda ke ci gaba da samun karfi.

    A yammacin ranar Litinin, hukumar Isra'ila da ke kula da tsallakawa zuwa Gaza, (COGAT), ta ce ta bar motoci 30 ɗauke da kayan abinci daga shirin samar da abinci na MDD su shiga Gaza.

    Wannan ya kawo karshen ƙorafin da MDD ta yi na cewa an rage kai kayan agaji yadda ya kamata cikin makonni biyu.

    "Al'amarin abin damuwa ne. Ba mu da isassun matsugunai, babu wadataccen abinci kuma babu wani tabbaci daga Isra'ila na cewa za a iya kai agaji cikin Jabalia inda sama da mutum 100,000 ke maƙale," in ji Georgios Petropoulos, shugaban ofishin kula da jin-kai na MDD a Gaza.

    Sama da Falasɗinawa 400,000 suka rage a arewacin Gaza, a cewar MDD.

    Dubun-dubatar mutane ne aka ɗaiɗaita da gidajensu a yankin Jabalia, yayin da sauran mutane suka kasance ba su da madogara a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da yin lugudan wuta.

  19. Gwamnonin PDP sun soke dakatarwar da aka yi wa Iliya Damagun

    Gwamnonin babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP sun soke dakatarwar da aka yi wa muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Iliya Damagum.

    Gwamnonin sun kuma soke dakatarwar da aka yi wa sakataren hulɗa na ƙasa na jam'iyyar, Debo Ologunagba, da mai ba da shawara kan harkokin shari'a, Kamaldeen Ajibade.

    Wannan na kunshe ne cikin jawabin da shugaban gwamnonin jam'iyyar kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi wa manema labarai a safiyar yau Talata.

    Bala ya ce Damagum ne shugaban jam'iyyar da suka sani yanzu kuma shi zai ci gaba da riƙe kujerar.

    Tun da farko dai, wani ɓangaren kwamitin zartaswar jam'iyyar na ƙasa da ya ɓalle ya sanar da naɗa Yayari Mohammed a matsayin wanda zai maye gurbin Damagum, inda kowane ɓangare ya yi iƙirarin dakatar da ɗayan.

    A wata sanarwa ranar Lahadi, Yayari ya ce kwamitin zartaswar jam'iyyar ya naɗa shi ne domin mayar da dawo da jam'iyyar kan turba.

    Ya ce PDP ba ta yin adawa yadda ya kamata saboda kowa ya ɗora buƙatar kansa a gaba kafin ta jam'iyya - musamman ma wasu jagororin kwamitin na zartaswa.

  20. Babban layin wuta na ƙasa ya sake lalacewa, sau biyu cikin awa 24

    A safiyar Talata ne, babban layin wuta na ƙasa ya sake lalacewa inda ya jefa ɗimbin mutane cikin duhu.

    Hakan na zuwa ne ƙasa da sa'a 24 bayan da kamfanonin rarraba wutar lantarki a faɗin ƙasar suka sanar da cewa layin ya lalace da misalin karfe 6:48 na yammacin ranar Litinin.

    Wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki a jihar Legas Eko ya fitar, ta ce an samu matsala a babban layin ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Talata, abin da ya janyo rashin wuta ga ɗimbin mutane.

    "Muna aiki tukuru tare da abokan hulɗar yayin da muke ƙoƙarin mayar da hasken wutar lantarki. Za mu sanar da mutane da zarar al'amura sun daidaita," in ji kamfanin.

    Shi ma kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Kaduna ya tabbatar da sake lalacewar babban layin wutar, inda ya yi alkawarin mayar da wuta nan ba da daɗewa ba.

    "Muna neman afuwar kwastomomin mu kan rashin wutar lantarki a jihohin da muke hulɗa da su tun yammacin jiya Litinin. Wannan ya faru ne sakamakon lalacewar babban layin wuta na ƙasa," in ji KEDCO.

    Ya ce jami'ai a kamfanin rarraba lantarki ta ƙasa (TCN) na iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin al'amura sun daidaita, daga nan kuma wutar lantarki za ta koma yadda aka saba.