Tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu zai bayyana a gaban kotu yau
A yau ne tsohon mataimakin Sudan ta Kudu na farko Riek Machar, zai bayyana gaban kotu inda zai fuskanci shari'ar da ake masa kan zargin aikata kisa da cin amanar ƙasa da kuma laifukan da suka shafi take haƙƙin bil adama.
Tuhume-tuhumen na da alaƙa da harin da mayaka masu ɗauke da makamai waɗanda ake zargi na bashi goyon baya suka kai wanda ya yi sanadin rasa rayukan sojojin Sudan ta Kudun 250.
An cire Mista Machar daga kan muƙaminsa a lokacin mulkin gwamnatin haɗin kai ƙarkashin shugaba Salva Kiir inda aka yi masa ɗaurin talala bayan harin da aka kai a watan Maris.
Magoya bayansa sun bayyana shari'ar a matsayin bita da ƙullin siyasa sannan sun zargi Mista Kiir da neman rufe bakin abokin hamayyarsa.
Wannan Shari'ar ta sanya fargabar yiwuwar sake dawowar yaƙin basasar ƙasar da kuma rikicin ƙabilanci wanda aka kawo ƙarshensa a 2018 bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.