'Najeriya na maraba da taimakon Amurka idan za a kare martabarta'
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi maraba da duk wani taimaka daga Amurka kan magance masatsalar masu tayar da ƙayar baya, matsawar za a mutunta kimarta.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato ɗaya daga cikin masu magana da yawon shugaban ƙasar,Daniel Bwala ya fitar a ranar Lahadi ya ce ''Muna maraba da taimakaon Amurka wajen yaƙi da masu tayar da ƙaya baya a ƙasarmu matsawar za ta kare mutuncinmu''.
Shugaba Trump na Amurka ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, idan hukumomin ƙasar ba su ɗauki mataki bakan abin da ya kira ''yi wa kiristoci kisan kiyashi a ƙasar''.
A ranar Lahadi ne Donald Trump ya shaida wa manema labarai cewa sojojin Amurka za su aika dakaru Najeriya ko su ƙaddamar da hare-hare ta sama domin dakatar da abin da ya kira ''kisan kiristoci a ƙasar'', sai dai bai bayar da cikakken bayani ba.