Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ahmad Bawage da Aisha Ja'afaru

  1. Ina ne 'Timbuktu Triangle' kuma me ya sa ya zama maɓoyar Boko Haram?

    Kashe sojojin Najeriya sama da 22 da mayaƙan Boko Haram suka yi a ƙarshen mako a dajin Timbuktu Triangle ya ɗaga hankalin mutane, ganin yadda aka yi asarar sojoji masu yawa a lokaci guda.

    Tun a ƙarshe-ƙarshen shekarar da ta gabata ne hare-haren mayaƙan Boko Haram suka fara komawa a yankin arewa maso gabas, wanda ya daɗe yana fama da matsalar tsaro, musamman rikicin Boko Haram.

    A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran shalkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar ranar Lahadi, ya ce, an kashe sojojin ne a lokacin da suka suka ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin mayaƙan ƙungiyar da ke yankin na Timbuktu.

    Wannan ya sa BBC ta yi nazari kan ina ne wannan wuri, kuma mene ne ya sa ya zama maɓoyar mayaƙan?

  2. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Talata.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.