Firaministan Serbia Milos Vučević ya sauka daga muƙaminsa
Firaiministan Serbia Milos Vučević (Milo Vulvi) ya sauka daga muƙaminsa sakamakon zanga-zangar ƙin gwamnati, wadda aka shafe watanni ana gudanarwa bayan mutuwar mutane 15 ya yinda rumfar wata tashar jirgin ƙasa ta rikito.
Al'amarin ya haifar da zarge-zargen cin hanci tare da buƙatar hukunta wadanda suke da hannu.
A daren Litinin an jikkata wata 'daliba ya yin arangama tsakanin ƴan adawa da masu goyon bayan jam'iyya mai mulki a birnin Novi sad.
Yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a birnin Belgrade, Mista Vulvi ya roƙi al'umma su kwantar da hankulansu.
Mista Vulvi ya ce bayan abinda ya faru a Novi Sad a daraen jiya, na dauki matakin sauka daga muƙamin firaiministan Serbia, na tyi doguwar tattaunawa da shugaban ƙasa, kuma ya amince da buƙata ta, saboda gujewa rabuwar kan al'umma, 'yan siyasa sun dauki alhakin abinda ya faru kuma a shirye suke a samar da kwanciyar hankali.