Zaɓen Ghana: Ministan cikin gida ya rasa kujerarsa ta ɗan majalisa
Ministan cikin gida na Ghana, Henry Quartey na jam'iyyar NPP mai mulki ya rasa kujerarsa ta ɗan majalisar gundumar Ayawaso ta Tsakiya.
Kafin naɗa shi muƙamin ministan, Mista Quartey shi ne ministan jihar Greater Accra
Ɗan takarar jam'iyyar NDC mai hamayya, Abdul Rauf Tubazu ne ya kayar da shi a mazabar tasa, kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana ya nuna.
Ga yadda sakamakon hukumar zaɓen ƙasar ya nuna:
- Henry Quartey (NPP) - 23,345
- Abdul Rauf Tubazu (NDC) - 29,755
- Charles Kwame Adams (NDP) - 163
Jim kaɗan bayan bayyana sakamakon zaɓen gundumar, ɗan takarar NDC da ya yi nasara ya ce tuni dama yana da ƙwarin gwiwar lashe zaɓen.