Magoya bayan NDC a Accra sun fara murnar nasarar zaɓe
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage
Asuba ta gari
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Kafin nan, za ku iya ziyartar shafin mu na bbchausa.com domin ci gaba da karanta labarai da kuma kallon bidiyo.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Labarai da dumi-dumi, Faɗuwar gwamnatin Assad babban tarihi ne - Biden
Shugaba Joe Biden na Amurka ya yi jawabi kan faɗuwar gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Syria.
Ya kira batun da "babban tarihi", kuma ya ce Rasha da Iran da kuma Hezbollah sun ƙasa ceto gwamnatin daga faɗuwa.
Biden ya ce Amurka za ta tattauna da dukkan ƙungiyoyi a Syria tun da yanzu Assad ya tafi.
Ƴan sanda a Ghana sun kama mutum 12 da zargin lalata wuraren ajiye kayayyaki
Ƴan sanda a Ghana sun ce sun kama mutum 12 waɗanda ake zargi da sata da kuma lalata wuraren ajiye kayayyaki a wasu sassan ƙasar.
Mai magana da yawun ƴan sandan ƙasar, ACP Grace Ansah-Akrofi, ta ce bincike ya nuna cewa mutanen da ake zargin sun kai hari tare da lalata kayayyaki.
Wuraren da suka lalata sun haɗa da ofishin hukumar zaɓen ƙasar a mazaɓar Damongo da ke yankin Savannah.
Sun kuma lalata gidajen wasu shugabanni al'ummomi a sassan ƙasar, har ma da wasu cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.
"Wasu daga cikin mutanen da muke zargin, sun kutsa cikin rumbun ajiye abinci na ɗalibai a Tamale tare da yin awon gaba da kayan abinci," in ji kakakin ƴan sandan.
Ƴan sanda sun buƙaci mutane su kwantar da hankali yayin da suka aika jami'an tsaro zuwa muhimman wurare domin yin sintiri da mayar da doka da oda.
An ji ƙarar fashewar abu a Damascus
An sake jin ƙarar fashewar abu mai girman gaske a Damascus. Wannan shi ne ƙara ta biyu da aka ji.
Tun da farko, rahotanni sun ce Isra'ila ta kai hari lardin Kafr Sousa da kuma wata cibiyar bincike, wuri da a baya ta ce masana kimiyyar Iran na amfani wajen ƙera makamai masu linzami.
Sai dai ba mu tabbatar da hakan ba.
Mun ga wuta na ci a wurin da aka samu fashewar.
Labarai da dumi-dumi, Kafofin yaɗa labaran Rasha sun ce Bashar al-Assad ya tsere zuwa ƙasar
Hamɓararren shugaban Syria Bashar al-Assad ya isa Moscow da iyalansa, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Rasha suka ruwaito daga majiyoyi a Kremlin.
Rahotanni sun ce Rasha ta bai wa Assad zaman mafaka tare da iyalansa.
BBC ba ta kai ga tabbatar da gaskiyar wannan labari ba.
Pillars ta samu maki uku a kan Katsina United
Asalin hoton, Kano Pillars
Kano Pillars ta doke Katsina United da ci 1-0 a wasan mako na 16 a Premier League ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, Najeriya.
Tun kafin hutu ne Pillars ta ci ƙwallon ta hannun Abba Adam, haka kuma aka tashi, kenan wadda ake kira sai masu gida ta haɗa maki ukun da take bukata.
Karon farko da Pillarrs ta samu nasara a bana a gida, bayan da ta dinga buga wasanninta a jihar Katsina, sakamakon gyara da aka yi wa filinta.
Ministan sufurin jiragen ƙasa ya sha kaye a zaɓen kujerarsa ta majalisa
Asalin hoton, John Peter Amewu/Facebook
Ministan sufurin jiragen ƙasa a Ghana, John Peter Amewu ya sha kaye a kujerarsa ta majalia daga jihar Volta.
Gundumar Hohoe ce mazaɓa ɗaya tilo daga cikin mazaɓun jihar 18, da jam'iyyar NPP ta samu nasara a jihar a zaɓen 2020 da ya gabata.
Jihar Volta ta kasance inda jam'iyyar NDC ke da rinjaye.
Firaministan Birtaniya ya yi maraba da faɗuwar 'gwamnatin zalunci' ta Assad
Asalin hoton, PA Media
Firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer ya yi maraba da faɗuwar 'gwamnatin zalunci' ta Assad.
Firaministan ya yi kira da a "samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali" a ƙasar.
"Ba mu taɓa ganin abubuwan da ke faruwa a Syria a sa'o'i da kuma kwanaki da suka gabata ba, kuma muna magana da abokan mu a yankin da saka ido kan lamarin," in ji shi.
Ya ce ƴan Syria sun sha wahala a karkashin mulkin zalunci ta Assad na tsawon lokaci, kuma suna maraba da faɗuwar gwamnatinsa.
Tinubu ya taya Mahama murnar samun nasarar zaɓen Ghana
Asalin hoton, Tinubu/Facebook
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya taya ɗan takarar shugaban ƙasar Ghana na jam'iyyar NDC mai hamayya, John Dramani Mahama, murnar nasarar da ya samu a zaɓen ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan da mataimakin shugaban ƙasa Muhammadu Bawumia ya amince da shan kaye.
Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce shugaba Tinubu ya yi fatan cewa hulɗa tsakanin ƙasashen biyu za ta ƙaru da kuma ganin kwanciyar hankali a faɗin ƙasashen ƙungiyar Ecowas.
Tinubu ya jinjinawa ƴan Ghana ta yadda suka fito suka yi zaɓe, inda a ɗaya gefen ya kuma yaba wa halin dattako da Bawumia ya nuna na amsa shan kaye tun kafin hukumar zaɓen Ghana ta sanar da sakamakon.
Har yanzu dai hukumar zaɓen ƙasar ba ta fara bayyana sakamakon zaɓen a hukumance ba.
Ɓata-gari sun lalata wuraren ajiye kayayyaki a Tamale
Wasu ɓata-gari sun far wa gidajen ajiye kayyaki a yankin Tamale.
Rahotonni na cewa an fasa wurare biyu a yankin wato wuraren ajiye kayyakin majalisa da na kayayyakin aikin noma.
Ministan ciniki ya rasa kujerarsa ta majalisa
Asalin hoton, Ministry of trade and industry/Facebook
Ministan ciniki n aƙasar Ghana, Kwabena Tahiru Hammond ya rasa kujerarsa ta ɗan majalisa daga gundumar Adansi Asokwa a jihar Ashanti.
Mista K.T Hammond, kamar yadda aka fi saninsa a ƙasar, ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar NDC mai hamayya.
Ministan cinikin na ɗaya daga cikin ƙusoshin gwamnatin Nana Akufo-Addo, masu ƙarfin faɗa a ji.
Ga sakamakon mazaɓar da hukumar zaɓen ta fitar
KT Hammond (NPP) - 13,275
Godwin Dorgbadzi (NDC) - 14,229
Justice Mensah (CPP) - 346
Atiku ya taya Mahama murnar samun nasarar zaɓen Ghana
Asalin hoton, Facebook/Atiku Abubakar
Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya aike da saƙon taya murna ga ɗan takarar shugaban ƙasar na NDC mai hamayya a Ghana, John Dramani Mahama, kan nasarar da ya samu a zaɓen ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan ɗan takarar jam'iyyar NPP mai mulki Mahamudu Bawamia ya amince da shan kaye tare da taya Mahama murna.
"Ina miƙa sakon taya murna kan nasarar da ka samu, mai girma zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana John Mahama,'' in ji Atiku
Har yanzu dai hukumar zaɓen ƙasar ba ta fara bayyana sakamakon zaɓen a hukumance ba.
Hotunan yadda aka lalata gidan Assad a Damascus
Yayin da muke kawo muku rahotonni daga Syria, 'yantawayen sun kutsa cikin gidan hamɓararren shugaban ƙasa Bashar al-Assad tare da lalata shi.
Wakilanmu da ke birnin Damascus sun samu aukar hutunan gidan.
A yanzu an sanya dokar taƙarta zirga-zirga a birnin Damascus har zuwa ƙarfe 5:00 na asubahin gobe.
'Yantawayen Syria sun saki fursunonin siyasa
Asalin hoton, Reuters
'Yantawayen Syria sun ce sun saki fursunonin siyasa da dama daga gawurtaccen gidan yarin Sednaya da ke kusa da birnin Damascus.
Dubban mutane aka tsare a gidan yarin da ƙungiyar Amnesty ta taɓa bayyana shi da ''gidan yanka mutane''.
Kafofin yaɗa labaran Iran, sun ce 'yantawayen sun yi wa ofishin jakandancin ƙasar a Syria ƙawanya.
Bidiyon da aka yaɗa ya nuna yadda aka lalata ginin ofishin tare da fasa tagoginsa.
Haka kuma bidiyon ya nuna yadda 'yatawayen suka yaga hotunan tsohon shugaban sojin Iran, Janar Qasem Soleimani da na tsohon shugaban ƙungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah.
Ina Bashar al-Assad ya shiga?
Asalin hoton, Reuters
Tun bayan da 'yantawayen Syria suka sanar da ƙwace iko da birnin Damascus tare da hamɓarar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad - da ya mulkin ƙasar na kusan shekara 25 - ake ci gaba da aza ayar tambayar inda ya shiga.
Rahotonni sun ce shugaban ya fice daga jirgin a jirgin sama.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce wasu manyan jami'an soji biyu sun yi iƙirarin cewa shugaban ya fice daga birnin zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta tabbatar da ficewar Assad daga birnin ''bayan ƙulla yarjejeniyar miƙa mulki da wani ɓangare daga cikin 'yantawayen''.
To sai dai ma'aikatar harkokin wajen Rashar ta musanta hannu a ƙulla yarjejeniyar.
Ministan Lafiya ya rasa kujerarsa ta majalisa
Asalin hoton, Dr Okoe Boye/Facebook
Minista n lafiyar Ghana, Dakta Bernard Okoe Boye ya kasance minista na baya-bayan nan da ya rasa kujerarsa ta majalisa.
A watan Fabrairun wannan shekara ne shugaban ƙasar ya naɗa shi ministan lafiyar ƙasar, bayan korar Kweku Agyemang Manu daga muƙamin.
Dakta Boye ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar NDC mai hamayya, Ayiku Benjamin Narteh.
Ga sakamakon da hukumar zaɓn ta bayyana:
Dr Bernard Okoe-Boye (NPP) - 19,866
Ayiku Benjamin Narteh (NDC) - 23,913
Magoya bayan NDC a Accra sun fara murnar nasarar zaɓe
Magoya bayan jam'iyyar NDC mai hamayya a birnin Accra sun fatsama kan tituna domin yin murnar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar.
Kawo yanzu dai hukumar zaɓen ƙasar ba ta bayyana sakamakon ƙarshe na shugaban ƙasar a hukumance ba, amma tuni ɗan takarar jam'iyyar NPP mai mulki Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaɓen.
Cikin wani gajeren jawabi da ya yi wa manema labari, mataimakin shugaban ƙasar ya ce bayan zaɓen da aka gudanar ranar Asabar a faɗin ƙasar hankulan jama'a sun karkata kan sanin samakon zaɓen.
Ɗan takarar na jam'iyya mai mulki ya kuma ce jam'iyyar hamayya ta NDC ta kuma samu gagarumin rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.
Tun da farko wasu ministoci, jiga-jigan gwamnatin NPP, sun sha kaye a kujerun majalisar dokokin ƙasar.
Zaɓen ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke fama da matsain tattalin arziki da hauhawar farashin kayyaki.
Ɗan takarar majalisar na indifenda ya ci zaɓe a jihar Ashanti da NPP ke da ƙarfi
Asalin hoton, Ohene Kwame Frimpong/Facebook
Dan takarar majalisa na indifenda nya lashe zaɓen ɗan majalisar gudnumar Asante Akim ta Arewa da ke jihar Ashanti.
Ohene Kwame Frimpong ya lashe zaɓen da tazarar fiye da ƙuri'a 18,000
Wannan sakamako ya bai wa mutane da dama mamaki musamman irin tazarar da Mista Frimpong ya bai wa ɗan majalisar NNP mai ci, Andy Appiah Kubi.
Ga sakamakon da hukumar zaɓen ta fitar.
Andy Appiah Kubi (NPP) - 8,933
Ohene Kwame Frimpong (independent) - 26,926
Kofi Asamoah (NDC) - 2,469
Ministar sadarwa ta rasa kujerarta ta 'yar majalisa
Asalin hoton, Ursula Owusu-Ekuful/Facebook
Ɗaya daga cikin ƙusoshin gwamnatin Akufo-Addo, Ursula Owusu-Ekuful ta rasa kujerarta ta 'yar majalisar dokokin ƙasar daga gundumar Ablekuma ya Yamma ta jihar Greater Accra.
Ministar sadarwar ta sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar NDC mai hamayya, Reverend Kweku Addo.
Ms Ursula - wadda ta kwashe shekara takwas tana riƙe da muƙamin ministar sadarwa - ta kasance ɗaya daga cikin kusoshin gwamnatin NPP.
Ga sakamakon mazaɓar da hukumar zaɓen ta bayyana:
Ursula Owusu-Ekuful (NPP) - 26,575
Reverend Kweku Addo (NDC) - 31866
Ministan yawon buɗe idanu ya faɗi kujerarsa ta ɗan majalisa
Asalin hoton, Andrew Egyapa Mercer/Facebook
Ministan yawon buɗe idanu na ƙasar Ghana, Andrew Egyapa Mercer ya faɗi zaɓen kujerarsa ta ɗan majalisar gundumar Sekondi da ke jihar Wester Region.
Andrew - wanda ke cikin jiga-jigan jam'iyyar NPP mai mulki - ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar NDC mai hamayya.
Andrew Mercer ya kasance 'yan majalisar gundumar Sekondi tun 2016.
Ga sakamakon mazaɓar da hukumar zaɓen ta bayyana:
Andrew Egyapa Mercer (NPP) - 11,084
Blay Nyameke Armah (NDC) - 14, 558
A jawabinsa na muranar lashe zaɓen, Blay Nyameke Armah na NDC ya gode al'ummar mazaɓar Sekondi bisa nasarar da ya samua a zaɓen tare da alƙawarta sake gina gundumar.