Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/07/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 24 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. EFCC ta kama ƴan damfara ta intanet 25 a Kano

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta kama wasu mutum 25 da ake zargi da aikata damfara ta intanet a wani samame da ta kai a harabar jami’ar Bayero da ke Kano.

    Hukumar ta ce jami'anta sun gudanar da samamen ne bisa sahihan bayanan sirri da suka samu da ke nuna cewa mutanen na da hannu a ayyukan damfara ta intanet da kuma satar bayanan mutane.

    Hukumar ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntanta na X.

    Dukkan waɗanda aka kama dalibai ne na jami’ar, kuma an gano wayoyi da kwamfutoci da mota kirar Honda Accord a hannunsu.

    Kayan da aka kwato daga wurin sun haɗa da wayoyin salula, kwamfutoci, na’urorin haɗi da mota kirar Honda Accord.

    EFCC ta ce an kama su ne bayan makonni ana sa ido a kansu kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.

  2. Amurka za ta lalata magungunan tazarar haihuwa da aka shirya raba wa kasashen duniya

    Gwamnatin Amurka na shirin lalata magungunan tazarar haihuwa da kimarsu ta kai kusan dala miliyan 10, waɗanda hukumar tallafawa ƙasashen duniya ta Amurka (USAID) ta saya domin rabawa asibitoci a ƙasashen duniya.

    An adana magungunan ne a wani dakin ajiya da ke ƙasar Belgium, inda aka shirya aikewa da su zuwa ƙasashen da samun magungunan ke da wuya.

    Sai dai tun bayan rufe hukumar USAID da gwamnatin shugaba Donald Trump ta yi a bana, ayyukanta da shirin rabon kaya suka tsaya cik.

    Gwamnatin Amurka ta ce an yanke shawarar lalata magungunan ne saboda dokoki da ƙa’idodin Amurka da bai goyon bayan zubar da ciki.

    Haka kuma, gwamnati ta ce fiye da kashi 30 na magungunan sun kusan lalacewa kuma sake musu kwali da sake sayar da su zai iya cin miliyoyi.

    Sanata Jeanne Shaheen daga jihar New Hampshire ta gabatar da kudirin doka domin dakatar da lalata magungunan inda ta ce magungunan suna da muhimmanci gare ta da kuma sauran mata saboda tasirin da zai iya yi ga lafiyar mata a kasashe masu ƙaramin karfi.

  3. Ma’aikatar Ilimin Thailand ta rufe makarantu saboda rikicin da ya ɓarke da Cambodia

    Ma’aikatar ilimi ta Thailand ta bayar da umarnin rufe wasu makarantun da ke yankunan kan iyaka na ɗan wani lokaci, sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakaninta da ƙasar Cambodia.

    Jaridar Thai Enquirer da ke Bangkok ta ruwaito cewa makarantu 582 aka rufe a jihohin Surin da Sisaket da Buriram, bayan da aka harba rokoki zuwa unguwannin da jama'a ke zaune.

    Rahotanni sun ce wasu makarantun da ba su cikin yankunan da rikicin ya shafa aiki a matsayin mafaka na ɗan wani lokaci ga waɗanda rikicin ya shafa kamar yadda ministar ilimi, Farfesa Narumon Pinyosinwat, ta buƙata.

    A nata bangaren kuma, ma’aikatar harkokin wajen Thailand ta buƙaci Cambodia da ta dakatar da abin da ta kira matakan da suka ci karo da dokokin ƙasashen duniya.

    Thailand ta ƙara da cewa za ta ƙara tsaurara matakan kariya idan Cambodia ta ci gaba da kai hare-haren soji.

    Cambodia kuwa ta zargi Thailand da yin amfani da ƙarfin fiye da kima a yankin da ke gefenta na iyaka.

  4. NAFDAC ta gano gidan ajiye sinadaran haɗa abubuwa masu fashewa a Kano

    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta gano wani babban gidan ajiya a Kano da ke cike da sinadarai masu haɗari da ake amfani da su wajen haɗa abubuwa masu fashewa, ciki har da sinadarin sulphuric da nitric acid kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Hukumar ta kuma rufe wurin nan take.

    A cewar hukumar, an gano lita 60,000 na sulphuric acid da kuma lita 28,560 na nitric acid da kuma jarkoki da suka kai 330 da aka riga aka fitar da sinadaran cikinsu ba tare da sanin inda aka kai su ba a cikin gidan.

    “Abin da muka gani a nan ya girgiza mu. Ban taɓa ganin adadin waɗannan sinadarai masu haɗari a wuri guda ba,” in ji Farfesa Adeyeye.

    Hukumar ta ce ba a samu wandan yake da gidan ajiyar ba a lokacin da aka isa wurin, amma an kama wani ma’aikacin da ke kula da wurin, kuma ana ci gaba da bincike don gano wanda yake da wurin da kuma inda ya samo sinadaran da kuma inda yake kai su.

    NAFDAC ta bayyana cewa sinadaran na cikin jerin kayan da ke da haɗari sosai ga mutane saboda haka sai da izini daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro kafin a shigo da su ƙasar.

    Hukumar ta kuma tabbatar da cewa za ta lalata sinadaran bisa ka’idojin da suka dace don kare lafiyar jama’a, sannan za ta tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ya mallaki sinadaran a gaban shari’a.

  5. Sabon rikici ya ɓarke tsakanin sojojin Thailand da Cambodia a kan iyaka

    Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin sojojin Thailand da na Cambodia a yankin iyakar ƙasashen biyu, inda kowanne ɓangare ke zargin ɗayan da fara buɓe wuta.

    Ministan lafiya na Thailand ya ce rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar soja guda ɗaya da fararen hula 11.

    Ya ƙara da cewa wajen mutum 35 ne rikicin ya shafa.

    Rikicin dai ya samo asali ne bayan Thailand ta kori jakadan Cambodia daga ƙasarta, tare da janye nata jakadan daga Phnom Penh, babban birnin Cambodia.

    Thailand ta bayyana cewa wasu sabbin nakiyoyi da aka dasawa a yankin sun jikkata ɗaya daga cikin sojojinta.

    Sai dai gwamnatin Cambodia ta musanta zargin cewa tana dasa sabbin nakiyoyi a yankin.

    Rikici tsakanin ƙasashen biyu da ke maƙwaftaka da juna ya fara ƙamari ne tun a watan Mayu, inda lokaci zuwa lokaci ake samun saɓani tsakanin sojojin su.

  6. Shugabar hukumar Turai ta kai ziyara China don ƙarfafa alaƙa tsakanin ɓangarorin biyu

    Shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta isa birnin Beijing domin halartar taron cika shekaru 50 da ƙulla alaƙar diflomasiyya tsakanin Turai da China.

    Da take jawabi bayan isarta, von der Leyen ta bayyana ganawar a matsayin wata dama ta sabunta fahimtar juna da kuma sake daidaita huldar diflomasiyya da kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu.

    Ana sa ran tattaunawar za ta taimaka wajen sauƙaka tashin hankalin da ke tattare da harkokin kasuwanci tsakanin Turai da China, musamman duba da matsin lamba da matakan haraji da shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗora wa ƙasashen waje.

    Kafar yaɗa labarai ta China ta bayyana cewa China na kallon Tarayyar Turai a matsayin abokiyar hulɗa, ba gasa ba.

  7. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Alhamis.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.