Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 09/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 9 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Farashin gangar man fetur ya zarce dala 100 saboda yaƙin Iran

    Yaƙin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka ya janyo tashin goron zabin farashin man fetur, inda farashin ganga ɗaya a yanzu ya zarce dala 100 a kasuwannin duniya.

    Tashin farashin na da nasaba da rufe mashigin Hurmuz da Iran ta yi, hanyar wucewa da kashi 20 cikin 100 na makamashin da ake amfani da shi a duniya.

    Lamarin ya fi muni a kasuwannin Asiya, inda aka fi amfani da makamashin da Iran ke samarwa.

    Masu sharhi na gargaɗin idan yaƙin ya ci gaba har zuwa ƙarshen wannan watan, farashin gangar man fetur na iya haura sama da dala 150.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Internet, shugaban Amurka, Donlad Trump ya ce tashin farashin na wani ɗan lokaci ne, kuma gara ɗaukar wannan ƙaddarar a kan barin Iran ta mallaki makamin Nukiliya

  2. Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila da yankin Gabas ta Tsakiya

    Iran ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa cikin dare kan Isra'ila da wasu ƙasashen Larabawa a yankin gabas ta tsakiya.

    Hukumomi a Bahrain sun ce aƙalla mutane talatin da biyu sun jikkata a wani harin jirgi marar matuƙi a yankin Sitra da ke kudancin babban birnin Manama.

    Wannan shi ne adadi mafi yawa a hari guda da aka samu tun lokacin soma yaƙin.

    Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa biyu, yayin da suke kan hanyar isa wata babbar cibiyar man fetur.

    Suma ƙasashen Qatar, da Kuwait, da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ba da rahoton kai musu sabbin hare-hare.

    A Isra'ila wacce ta sake fuskantar hare-haren makamai masu linzami daga ɓangarori biyu, Lebanon da kuma Iran, an samu wata mata da tarkacen makami mai linzamin ya jikkata.

  3. 'Trump ya nuna adawa da naɗin sabon jagoran addinin Iran'

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa bai ji daɗin naɗin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin Iran ba kamar yadda gidan talabijin na Fox news ya bayyana a wani shirinsa.

    Mai gabatar da shirin, Brian Kilmeade, ya ce ya yi magana da Trump bayan sanar da naɗin, inda shugaban na Amurka ya gaya masa cewa: “Ban ji daɗin naɗin ba, ina adawa da naɗin da aka yi."

    Sai dai mai gabatar da shirin bai bayar da ƙarin bayani game da tattaunawar da ya yi da Trump ba.

    Har yanzu kuma Trump bai fitar da wata sanarwa a bainar jama’a game da batun ba.

  4. Me ya sa shugaban Iran ya nemi afuwar maƙwaftan ƙasar?

    Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian ya bai wa mutane da dama mamaki bayan ya nemi afuwar maƙwaftan ƙasar bisa ga hare-haren da ƙasar ta ƙaddamar a cikinsu.

    Shugaban ya nemi afuwar ne a ranar Asabar, a matsayinsa na ɗaya daga cikin mambobin kwamitin riƙon-ƙwarya na jagorancin ƙasar.

    Abu ne mai wahala wata ƙasa ta nemi afuwar wata, musamman a alokacin da ake gwabza yaƙi, haka nan ma kalmomin da ya yi amfani da su, sun ɗauki hankali.

    A mafi yawan lokuta da wahala ka ga shugabanni sun yi amfani da kalamar "nadama", sannan kuma ba su cika ɗaukan alhaki ba kai-tsaye.

    Amma shi Pezeshkian kai-tsaye ya amince cewa an kai farmaki kan ƙasashe masu maƙwaftaka sannan ya ce a yanzu an buƙaci dakaru su tsagaita daga kai musu hari har sai idan daga cikin ƙasashen ne aka kai wa Iran hari.

    "Na ga dacewar na nemi afuwar ƙasashe maƙwafta waɗanda aka kai wa hari," in ji shi. "Ba aniyarmu ba ne mu far wa maƙwaftanmu."

    To sai dai tambayar ita ce: shin wannan neman afuwa ta kai zuci, kuma me ya sa sai yanzu?

    Wata ƙila mataki ne na shugabancin ƙasar wajen ganin yankin bai hargitse ba.

  5. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.