Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 14/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 14/03/2026

Taƙaitattu

  • Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Isra'ila
  • Amurka ta kai hari tsibirin Kharg na Iran, mai ɗimbin arziki
  • An kai hari ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza
  • Hamas ta nemi Iran da daina kai wa maƙabtan ƙasashe hari
  • Za mu bari jiragen Indiya su wuce lafiya ta mashigar Hormuz - Iran
  • Za mu buɗe mashigar Hormuz 'ko ta halin ƙaƙa' - Trump
  • Za mu mayar da martanin kowane hari kan makamashinmu - Iran

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Mun kakkaɓo makaman linzami 9 da jirage marasa matuƙa 33 a yau - UAE

    Ma'aikatar tsaron ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce na'urar tsaron sararin samaniyarta ta kakkaɓo makaman linzami 9 da jirage marasa matuƙa 33 da aka harba wa ƙasar a yau.

    A rahoton da ma'aikatar ta fitar ta ce tun bayan da Iran ta fara ka mata hare-hare, ta samu nasarar kakkaɓo makaman linzami 294 da jirage marasa matuƙa 1,600.

    Ma'aikatar tsaron ƙasar ta kuma ce mutum 6 ne suka mutu yayin da 141 suka jikkata tun lokacin.

  2. Za mu mayar da martanin kowane hari kan makamashinmu - Iran

    Khamenei Mojtaba

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Iran ta yi barazanar mayar da martani kan kowane hari kan cibiyoyin makamashinta, ta hanyar kai hari kan kamfanonin man Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar Tasnim mai alaƙa da rundunar juyin juya halin ƙasar, ta ce ambato Ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi na bayyana haka a waji jawabi da ya gabatar.

    ''Idan aka kai hari cibiyoyin man fetur ɗinmu, sojojinmu za su kai hari kan cibiyoyin Amurka ko kamfanonin da ke da hannayen jarin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya'', in ji shi.

    "Za mu mayar da martani kan hare-haren, amma za mu ɗauki matakin ganin martannmu bai shafi fararen hula ba'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Kalaman nasa na zuwa ne sa'o'i bayan sojojin AMurka sun ka hari tsibirin Kharg - mai matuƙar muhimmanci ga Iran, da ake tunanin kashi 90 cikin 100 na man da take fitarwa na bi ta wurin.

  3. Za mu buɗe mashigar Hormuz 'ko ta halin ƙaƙa' - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ''nan ba da jimawa ba za mu buɗe mashigar Hormuz ko ta halin ƙaƙa'', don jirage su wuce cikin kwanciyar hankali.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce yana fatan China da Faransa da Japan da Koriya da Kudu da kuma Birtaniya za su aika jiragen ruwa na yaƙi zuwa mashigar ''domin kare duk wata barazana'' daga Iran.

    Ya ƙara da cewa ƙasasashe da dama za su aika jiragen ruwansu na yaƙi domin tabbatar da ''tsaro a mashigar''

    Ya ce a yanzu Amurka za ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai kan jiragen ruwan Iran da ke wajen mashigar''.

    Ya yi iƙirarin cewa Amurka ta ''lalata kashi 100 na ƙarfin sojin Iran, amma ya ce takan yi amfani da jirage marasa matuƙa da dasa nakiyoyi da kuma makamai masu linzami masu cin gajeren zango.

    Wakilin Iran a Geneva, Ali Bahrani ya ce iƙirarin Trump ɗin na lalata ƙarfin sojin Iran ''ƙirƙirarren labari ne''.

  4. Za mu bari jiragen Indiya su wuce lafiya ta mashigar Hormuz - Iran

    Hukumomin Iran sun sanar da cewa za su bari jiragen ruwan Indiya su wuce lafiya ta mashigar Hormuz.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai, jakadan Iran a Indiya, Mohammed Fathali ''Iran da Indiya abokan juna ne kuma suna da muradi gud a iri ɗaya.

    A baya ma'iakat fito ta Indiya ta tabbatar da ''wucewa jiragenta biyu ta mashigar Hormuz''.

    Iran ta sanar da rufe mashigar ga jiragen dakon mai daga ƙasashe daban-dban musamman na yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin martani ga hare-haren Isra'ila da Amurka suka kai wa ƙasar.

  5. Ba a lalata cibiyoyin man fetur a tsibirin Kharg ba - Iran

    Tsibiri

    Asalin hoton, Reuters

    A ranar Juma'a ne shugaban Amurka, Donald Trump ya ce sojojinsa sun kai harin bom kan tsibirin Kharg mai ɗimbin arzikin man fetur na Iran.

    Ya ce ba a kai wa cibiyoyin man hari ba, kodayake ya ce an kai hare-hare kan sansanonin sojin Iran da ke wurin.

    Tsibirin na da muhimmacin gaske a fanin tattalin arzikin Tehran, yayin da wani masani ya ce kusan kashi 90 na man da Iran ke fitarwa na bi ta tsibirin.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars mai alaƙa da dakarun juyin juya halin Iran ya ce an ji ƙarar fashewa fiye da 15 a tsibirin lokacin hare-haren Amurka.

    An kai hare-haren ne kan cibiyoyin sojin sama da na ruwa da na'urar kula da filin jirgin tsibirin, a cewar Fars.

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce ba akai wa cibiyoyin mai da ke tsibirin hari ba.

  6. Dakarun Iran sun ce mazauna kusa da cibiyoyin Amurka a UAE su tashi daga wuraren

    Rundunar sojin Iran ta ce tana da ƴancin kare ƙasarta da kuma kai wa sansanonin Amurka hari a yankin Gabas ta Tsakiya, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Iran suka ruwaito.

    Kakakin rundunar Kanal Ebrahim Zulfiqari, ya ce Iran na da cikakken ƴancin kai harin makamai masu linzami kan tasoshin fito da ke ƙasar Haɗaɗdɗiyar Daular Larabawa da kuma ''mafakar'' sojojin Amurka.

    Ya yi kira ga Musulmai su fice daga biranen ƙasar saboda kauce da cutar da su.

  7. Labarai da dumi-dumi, An ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami zuwa Iara'ila - IDF

    Rundunar sojin Ira'ila ta ce Iran ta harba mata sabbin hare-haren makamai masu linzami.

    Wannan dai shi ne hari na farko cikin sa'o'i 10.

    Sojojin na Isra'ila tabbatar da cewa an bai wa mutane damar ci gba da zama a wurare masu tsaro, amma ta buƙaci al'umma su ci gaba da bin shawarwarin kariya.

  8. Hotunan yadda hayaƙi ke tashi a faɗin Gabas ta Tsakiya

    Yaƙin Iran na ƙera jefa wasu sassan yankin Gabas ta tsakiya cikin matsala da fargaba yayin da kae ganin hayaƙi na tashi a wasu biranen sassan sakamakon jerin hare-hare.

    A ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa an ga hayaƙi na tashi a saman tahar jiragen ruwa ta Fujairah, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ajiyar man fetur a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan da jirgi maras matuƙi ya kai hari kan tashar.

    Can ma a kudancin Lebanon wani gini ya kama da wuta a unguwar Haret Saida na Sidon, a kudancin, bayan harin Isra'ila.

    Haka hare-hare sun lalata wasu gidaje a Isra'ila.

    Rufin wani gini a Shoham da ke tsakiyar Isra'ila ya ruguje bayan hare-hare.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun gano makamai masu linzami da aka harba cikin ƙasar cikin dare

    bakin hayaki

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Hayaƙi na tashi a cibiyar makamashi a tashar jiragen ruwa ta Fujairah
    gini cike da hayaki

    Asalin hoton, Shutterstock

    Bayanan hoto, Harin Isra'ila kan wani gini ya sanya hayaƙi na tashi a ginin da ke unguwar Haret Saida da ke Sidon a kudancin Lebanon
    hayaki

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Bayanan hoto, Yadda hare-hare suka lalata wani gini a unguwar Shoham da ke tsakiyar Isra'ila
  9. Isra'ila ta kai hari cibiyar adana makamai a kudancin Lebanon

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari cibiyar adana makamai a kudancin Lebanon.

    Sojojin Ira'ila sun ce sun kashe mayaƙan Hezbollah da ke jigilar makamai zuwa cibiyar.

    Cikin wata sanarwa da suka wallafa a shafinta na sada zumunta, sojojin na Isra'ila sun ce ''Sojojin saman Isra'ila sunlalata cibiyar tare da kashe mayaƙan Hezbollah''.

  10. Hamas ta nemi Iran da daina kai wa maƙabtan ƙasashe hari

    Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta yi kira ga Iran ta dakatar da ka hare-hare makbatan ƙasashen.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta jaddada cewa Iran na da ƴancin kare kanta daga hare-haren Isra'ila da Amurka.

    ''Kuna da ƴancin kare kanku ta dukla hanyar da kuke da ita, bida dokokin duniya, amma muna kira ga ƴan'uwanmu na IRan du daina kai hare-hare zuwa makwabtan ƙasashe'', a cewar sanarwar.

    Tun bayan fara yaƙin Isra'ila da Amurka kuma Iran a gefe guda, Tehran ta riƙa kai hare-hare kan wasu ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya da kuma sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen.

  11. An kai hari ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza

    h

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani hariin makami mai linzami ya faɗa kan ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza, babban birnin Iraƙi.

    Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na cewa ginin ya kama da hayaƙi, sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

    Kamfanin dillacin labarai na AP ya bayar da rahoton cewa harin makami mai linzami ya faɗa ne kan filin da jirage masu saukar ungulu ke sauka da tashi a harabar ofishin jakadancin.

    To amma kamfanin AFP ya ce jirgi maras matuƙi ya kai hari ofishin.

    Harin ya auku ne jim kaɗan bayan an kashe wasu maya ƙa biyu masu goyon bayan Iran a wasu hare-hare a binrin na Bagadaza, kamar yadda AFP ya ambato wasu majiyoyi na cewa.

    Za mu kawo muku ƙarin bayani game da harin idan mun samu

  12. Amurka ta kai hari tsibirin Kharg na Iran, mai ɗimbin arziki

    Tsibirin Kharg

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce sojojin Amurka sun kai hari tsibirin Kharg na Iran mai ɗimbin arzikin makamashi.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce ''Dakarun Amurka sun ƙaddamar da wani babban harin bom a tarihinsu na yaƙi a Gabas ta Tsakiya in da suka shafe duk wani kayan sojin Iran da ke tsibirin Kharg, mai ɗimbin arziki''.

    "Na zaɓi kada na lalata cibiyoyin man fetur da ke tsibirin. Amma idan Iran ko wani suka yi wani abu da zai kawo tsaikon wucewar jiragen dakon man fetur ta mashigar Hormuz, zan yi gaggawar duba shawarar kai wa cibiyoyin man fetur da ke tsibirin hari,'' in ji shugaban na Amurka.

    Masu shairhi na cewa kashi 90 cikin 100 na man da Iran ke fitarwa zuwa kasuwannin duniya daga tsibirin yake.

    To sai dai a martanin da ta mayar, rundunar sojin Iran ta ce za ta mayar - da duka cibiyoyin mai da na makamashi mallakin kamfanonin da ke aiki da Amurka - zuwa toka, idan ahr Amurka ta kuskura ta kai hari kan cibiyoyin manta da ke tsibirin, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Iran suka ruwaito.

  13. Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Isra'ila

    ginin da ya rushe

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar dakarun juyin juya hali na Iran sun ta ce ta ƙaddamar da hare-hare karo na 48 kan Isra'ila, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Iran suka bayyana.

    Kamfanin dillancin labarai na Jamhuriyar Musulunci ya ce an ƙaddamar da jerin hare-haren tare da na ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon.

    Yaƙi tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka a gefe guda ya ɓarke ne mako biyu da suka gabata bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran, lamarin da ya yi sanadin kisan jagoran addini a Iran.

    A matsayin martani Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

  14. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu an sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.