Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta yanke wa wani shahararren mai sana'ar kwalliya hukuncin ɗaurin wata shida, bayan samunsa da laifin liƙi da naira lokacin bikin aurensa a watan Disamba.
An yanke wa Abdullahi Musa Hussaini, wanda aka fi sani da "Amuscap" a shafukan sada zumunta hukuncin ne, jim kaɗan bayan amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Ana dai liƙi ko watsa takardar kuɗi a sama a Najeriya ne yawanci lokacin bukukuwa musamman ma na aure, domin nuna farin ciki.
Sai dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na da'awar a guji liƙa kuɗi a irin waɗannan bukukuwa, inda ta ce hakan rashin mutunta kuɗin naira ne.
Amuscap shi ne ɗan Najeriya na baya-bayan nan da aka ɗaure kan saɓa wa dokar babban bankin Najeriya (CBN) na 2007.
Dokar ta ce "liƙi da rawa ko kuma taka kuɗin naira laifi ne, hukuncinsa shi ne ɗaurin wata shida a gidan yari ko cin tarar 50,000 ko kuma duka aiwatar da duka hukuncin.
EFCC ta ce Amuscap ya liƙa tare da taka kuɗi naira 100,000 lokacin murnar bikin aurensa.
A shekarar da ta gabata, aka ɗaure shahararren ɗan daudun nan Idris Okineye, da aka fi sani da Bobrisky da kuma wata jarumar Nollywood Oluwadarasimi Omoseyin wata shida a gidan yari, bayan samun su da laifin liƙa kuɗi.