Rasha ta yi alƙawarin sakin dukkan 'yan ƙasar Indiya da ke aiki a cikin sojojinta, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Indiya.
Wannan alƙawarin ya zo ne a ƙarshen ziyarar da firaministan Indiya Narendra Modi ya kai birnin Moscow, inda ya tattauna batun da shugaba Vladimir Putin.
Delhi dai na neman a sako 'yan Indiyawa, wadanda suka ce an yaudare su ne zuwa ƙasar Rasha bisa alkawarin ayyukan da ba na yaƙi ba a cikin sojoji, amma daga baya aka tilasta musu yin fada a Ukraine.
Aƙalla Indiyawa hudu aka kashe a yaƙin da ake yi.
A ranar Talata, sakataren harkokin wajen Indiya, Vinay Kwatra ya ce akwai 'yan Indiya kusan 35 zuwa 50 a cikin sojojin Rasha, wadanda 10 daga cikinsu tuni aka dawo da su gida.
Ya ƙara da cewa a yanzu ƙasashen biyu za su yi ƙoƙarin dawo da sauran mutanen.
Indiyawan da suka maƙale a Rasha sun ce wasu wakilai ne suka yaudare su da neman kudi da fasfo na Rasha.
Yawancin waɗannan mutanen sun fito ne daga iyalai matalauta waɗanda aka yi musu alƙawarin aiki, wani lokaci a matsayin "masu taimako" a cikin sojojin Rasha.
A farkon wannan shekarar, ma'aikatar ta bukaci "dukkan 'yan Indiya da su yi taka tsantsan tare da nisantar irin wannan rikicin".
Sanarwar haɗin gwiwa da Indiya da Rasha suka fitar bayan tattaunawar tasu ta ce ɓangarorin biyu sun tanadi wasu muhimman abubuwa guda 9 na hadin gwiwa da suka haɗa da makamashin nukiliya da magunguna.
Shugabannin sun kuma ce za su yi niyyar haɓaka kasuwancin ƙasashen biyu zuwa dala biliyan 100 nan da shekarar 2030.