Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/07/2024

Taƙaitattu

  • An shiga rana ta ƙarshe a yaƙin neman zaɓen Birtaniya
  • Ɗan jaridar RFI Hausa Kabir Yusuf ya rasu
  • Majalisar wakilan Najeriya za ta ƙirƙiro ƙarin jiha a kudu maso gabashin ƙasar

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Rabi'atu Kabir Runka

  1. Dangote ya koka kan ƙarin kuɗin ruwa a Najeriya

    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya koka kan ƙarin kuɗin ruwa da babban bankin ƙasar CBN ya yi da kusan kashi 30 cikin 100.

    Yayin da yake jawabi a taron kwana uku da ƙungiyar masu masana'atu ta ƙasar ta shirya a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, Aliko Dangote ya ce ƙarin kuɗin ruwar zai kawo cikas ga ayyukan ci gaba tare da rage ayyukan yi a ƙasar.

    Hamshaƙin attajirin na Afirka ya ce a wannan matsayi na kuɗin ruwa da ake ciki, masana'antu ba za su iya samar da ayyukan yi ko wani ci gaba da zai inganta harkokin tattalin arziki ba.

    Babban bankin ƙasar ne ya samar da ƙarin kuɗin ruwan a lokacin zaman kwamitinsa kan tsare-tsaren kuɗi daga kashi 24.75 zuwa 26.35

    Gwamnan babban bankin ƙasar Olayemi Cardoso, ya ce an yi ƙarin ne ''domin magance matsalar hauhawar farashi da ƙasar ke fuskanta''.

    A baya-bayan nan ne Bankin duniya ya gargaɗi CBN ɗin da cewa ƙarin kuɗin ruwa ba zai magance matsalar hauhawar farashi ba, maimakon haka yana iya kawo tarnaƙi wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar.

    Aliko Dangote ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta samar da sabbin tsare-tsare da za su kare masana'atun cikin gida, ta hanyar samar musu da kyakkyawan yanayin da za su inganta kasuwancinsu.

    ''Babu wanda zai samar da ayyuka da wannan tsari na ƙarin kashi 26 a matsayin kuɗin ruwa, babu ci gaban da za a samu a haka'', in ji hamshaƙin attajirin.

  2. Sirrin samun nasara a harkar noma daga bakin Aminu Nyako

  3. Kotu ta yanke wa masu garkuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya

    Wata babbar kotun jiha da ke zamanta a Osun ta yanke wa wasu masu garkuwa biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin sace wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim Adamu, tare da kashe shi.

    An gurfanar da mutanen biyar a gaban alƙali bisa tuhume-tuhume da suka ƙunshi haɗa baki don yin garkuwa da mutumin da kuma laifin kisan kai, zargin da suka musanta a lokacin da aka fara gurfanar da su ranar 28 ga watan Oktoban 2021.

    A lokacin zaman sauraron shari'ar, lauyan gwamnati, Faremi Moses, ya gabatar da hujjoji da ke nuna cewa mutanen biyar sun yi garkuwa da Alhaji Ibrahim Adamu a ranar 17 ga watan Afrilun 2018 daga gidansa da ke ƙaramar hukumar Ede da arewa a jihar Ogun.

    Lauyan ya ce mutanen sun kashe Alhaji Ibrahim Adamu bayan da iyalansa suka biya kudin fansa na naira miliyan uku.

    A nasa ɓangare lauyan waɗanda ake zargin ya ce hujojjojin masu gabatar da ƙara ba su da ƙarfin da za su iya gamsar da kotu.

    To sai dai a lokacin da take yanke hukunci, Mai shari'a, Kudirat Akano ta ce kotu ta samu mutanen biyar da laifuka huɗu da aka tuhume da su, inda ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

  4. Majalisar wakilan Najeriya za ta ƙirƙiro ƙarin jiha a kudu maso gabashin ƙasar

    Majalisar wakilan Najeriya ta gabatar da ƙudurin ƙirƙiro ƙarin jiha guda da za a kira jihar Etiti a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

    Ƙudirin - wanda Amobi Godwin Ogah tare da wasu 'yan majalisa huɗu suka gabatar - ya tsallake karatu na farko a majalisar ranar Talata.

    Ƙudurin na buƙatar yin gyara a sashe na uku na kundin tsarin mulkin ƙasar, domin goge lamba 36 tare da maye gurbinta da lamba 37 don bai wa sabuwar jihar damar shiga jerin jihohin ƙasar, sannan a saka Etiti bayan Enugu cikin jerin sunayen jihohin ƙasar.

    Sabuwar jihar - da za a yanka daga duka jihohin yankin biyar - za ta ƙunshi ƙananan hukumomi 11, inda Lokpanta da a yanzu ke cikin jihar Abia, zai kasance babban birninta.

    Ƙananan hukumomin da za su koma sabuwar jihar sun haɗa da Isuikwuato da Umu-Nneochi (jihar Abia), da Orumba ta Arewa da Orumba ta kudu (jihar Anambra), sannan Ivo da Ohaozara (jihar Ebonyi), sai Aninri da Agwu da Oji River (jihar Enugu), da kuma Okigwe da Onuimo (jihar Imo).

  5. Ɗan jaridar RFI Hausa Kabir Yusuf ya rasu

    Allah ya yi wa fitaccen ɗan jaridar kafar yaɗa labarai ta RFI Hausa, Kabir Yusuf rasuwa.

    Marigayin - wanda ya kasance wakilin RFI Hausa a birnin Abujan Najeriya - ya rasu ne a birnin Kano da ke arewacin ƙasar.

    Kabir Yusuf ya rasu ne sakamakon gajeriyar jinya, kwanaki bayan komawarsa Najeriya daga Saudiyya inda ya sauke farali.

    Marigayin mai shekara 64 ya kwashe shekaru yana aikin yaɗa labarai.

    Za a yi jana'izarsa yau a birnin Kano, kamar yadda abokin aikinsa Bashir Ibrahim Idris ya wallafa a shafinsa na Facebook.

  6. An shiga rana ta ƙarshe a yaƙin neman zaɓen Birtaniya

    'Yan siyasa a Birtaniya na gangamin yaƙin neman ƙuri'u a rana ta ƙarshe a jajiberen zaɓen da za a yi a gobe.

    Jam'iyyar Labour na kan gaba a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a a lokacin yaƙin neman zaɓen da aka ɗauki mako shida ana yi.

    Firaminista Rishi Sunak ya jima yana gargaɗin masu kaɗa ƙuri'a kada su bai wa jagoran 'yan adawa Keir Starmer, damar yin rinjaye a majalisa.

    Jam'iyyar Labour ta sha kaye a zaɓuka huɗu, dan haka Sir Keir ya buƙaci magoya baya su tabbatar sun kaɗa ƙuri'a a gobe Alhamis.

    Tsohuwar sakatariyar harkokin gida ƙarƙashin jam'iyyar Conservative, Suella Braverman, ta ce yawancin 'yan ga-ni-kashe-nin jam'iyyar na komawa jam'iyyar Reform UK, saboda tsattsauran ra'ayinsu kan batun 'yan cirani.

  7. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba da Hausawa ke yi wa kirari da ta Bawa ranar samu.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta