Ƙarshen rahotonnin kenan
Da haka za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/07/2024
Daga Abdullahi Bello Diginza da Rabi'atu Kabir Runka
Da haka za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbin rahotonnin.
Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce an kashe ɗaya daga cikin manyan kwamandojinta a wani harin da Isra'ila ta kai ta sama.
Muhammad Nimah Nasser na ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan ƙungiyar Hezbollah da aka kashe a rikicin kan iyaka da aka kwashe kusan wata tara ana yi.
Da yake jawabi ga sojojin Isra'ila a kusa da iyakar Gaza, ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant, ya yi gargadin cewa sun shirya tsaf domin yakar kungiyar idan bukatar hakan ta taso.
"Muna kai farmaki kan ƙungiyar Hezbollah a kowace rana kuma muna zaune da cikakken shiri don ɗaukar duk wani mataki da ake bukata a Lebanon idan hakan ta taso," in ji shi.
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce Joe Biden ba shi tunanin janyewa daga takarar shugabancin Amurka.
Mai magana da yawunsa Karine Jean-Pierre, ta shaida wa manema labarai cewa Mista Biden na ci gaba da yakin neman zabensa, ta kuma musanta wani rahoton jaridar New York Times cewa shugaban na nazarin janyewa daga takarar.
Wakilin BBC ya ce sakamakon ƙuri''ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan ya nuna cewa kusan kashi uku cikin hudu na ganin cewa lafiya ba ta ishe shi ba, kuma bayanin da ya yi a wani taro na cewa gajiya ce ta hana shi tabuka abin kirki a muhawararasu da Trump bai burge kowa ba.
Wata sabuwar ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da jaridar New York Times ta fitar ta nuna yadda Mista Trump ya kara tserewa Shugaba Biden bayan mahawarar.
Mutum ɗaya ya mutu sannan wani ya ji mummunan rauni a wani hari da aka kai musu da wuƙa a wani kantin sayayya da ke garin Karmiel, a cewar hukumomin Isra'ila.
'Yansanda sun ce maharin wani mazaunin unguar Larabawa ne da ke kusa da wurin, kuma ɗaya daga cikin waɗanda aka kai wa harin ne ya harbe shi nan take.
Bidiyon kyamarar tsaro CCTV ya nuna wani mutum yana caccaka wa wasu mutum biyu wuƙa sanye da kaki kuma ɗauke da makamai, sai kuma ya gudu kafin a harbe shi kuma ya faɗi a ƙasa.
'Yansanda sun ce suna kallon lamarin a matsayin "harin ta'addanci" kuma an kama wasu daga cikin 'yan'uwan maharin.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani mummunan hari da 'yanbindiga suka yi yunƙurin kaiwa a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar ta hanyar kashe biyu daga cikinsu.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Laraba ta ce bayan tattara bayanan sirri, ta yi nasarar yi wa mahara huɗu kwanton ɓauna ɗauke da makamai a yankin Kurmin Aja da ke ƙaramar hukumar Kagarko.
"Cikin ƙwarewa dakaru suka yi musu kwanton ɓauna ta hanyar buɗe musu wuta, inda nan take suka kashe biyu daga ciki yayin da sauran suka tsere da raunikan harbin bindiga," in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa bayan fafatawar ne kuma aka gano bindigogi ƙirar AK-47 biyu, da ƙunshin harsasai 30, da babur biyu na 'yanbindigar.
Majalisar Dattijan Najeriya ta ce gwamnatin kasar ta manta da yankin arewa maso gabas a wasu daga cikin manyan ayyukanta da take yi a fadin kasar.
Sanata Muhammad Danjuma Goje daga jihar Gombe ne ya gabatar da kuduri kan wannan batu, wanda kuma ya samu goyon bayan majalisar baki daya.
Sanata Goje ya ce Shugaba Tinubu ya dauki matakan gina manyan hanyoyi na zamani a sassa biyar na kasar, amma babu ko hanya daya da za ta ratsa yankin arewa maso gabas.
Tinubu ya yi alƙawarin gina babbar hanya daga Legas zuwa birnin Kalaba, da wadda za ta taso daga Legas zuwa Sokoto, sannan ya yi wata daga Kalaba zuwa babban birnin Tarayyar Abuja, in ji Goje.
“Sai na ga idan har za a yi waɗannan hanyoyi da suka mamaye shiyya biyar na kasar nan amma aka manta da yankin da na fito, dan haka na magantu a zauren majalisa," in ji shi.
“Baya ga wannan, an yi mana alƙawarin tagwayen hanyoyin da gwamnatin tarayya ke yi da haɗin gwiwar China, ta farko daga Keffi zuwa Makurdi, daya kuma daga Akonga zuwa Gombe zuwa Adamama.
“An gama ta farko amma tamu har yanzu shiru."
Majalisar Dattijan Najeriya ta ce halin da aikin ‘yan sanda ke ciki a kasar na buƙatar a zauna a sake masa fasali.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mataimakin shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ce ba a gina hukumar ‘yan sandan Najeriyar kan yadda za ta yi nasara ba.
Sanata Ahmed Abdulhamid Malam-Madori wanda shi ne shugaban kwamitin aikin ‘yan sanda na Majalisar dattijan ƙasar, ya shaida wa BBC cewa tabbas batun haka yake, saboda yadda ake da ƙwararrun ƴansanda a ƙasar da za su iya fitar da ita a idon duniya, sai dai aikinsu na cikin gida babu inganci.
''Mu na da ƙwararrun ƴansanda da suka goge a fannin aiki, kuma ko ina muka shiga da su ba za mu ji kunya ba, amma ƙarancin samun kuɗi na gudanarwa da rashin kyautata wuraren ba su horo da lalacewar makarantun ƴansanda sun lalace idan aka kwatanta da na baya.
Sanata Ahmed Malam-Madori ya ce dole a kyautata wuraren da ake bai wa ƴansanda horo, a kuma haɓɓaka aikin ƴansanda ta hanyar ƙara musu kuɗaɗe wajen kasafin kuɗi, da inganta wuraren horonsu da duk wani abu na kyautatawa gare su.
Ya ƙara da cewa "yadda ake gudanar da kasafin kuɗi ta ɓangaren ƴansanda abin bai taka kara ya karya ba, hatta a kasafin kudin bana ba a bai wa wurin fifiko ba,Inda ya ce ya kamata yadda ake bai wa sojin sama da na ƙasa da na ruwa kuɗi su ma ƴansanda indai ba a ba su sama da na sojoji ba, to bai kamata a ba su ƙasa da haka ba, saboda idan ana batun tsaro ƴansanda ne a sahun gaba domin sojoji ba wannan horon aka ba su ba."
Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya ce akwai ƙudurori kan batun inganta aikin ƴansanda da ƴan majalisa za su gabatar a zauren majalisar, za kuma su yi ƙokarin ganin an tabbatar da su.
''A ciki akwai batun gyaran makantun ƴansanda da suka lalace, akwai batun fansho saboda ƴansanda na karbar mafi ƙanƙantar fansho, saboda abin da ake bai wa sojoji ya ninka wanda ake bai wa ƴansanda, lamarin akwai tausayawa a ciki.''
An jima ana sukar gwamnatin Najeriya kan batun na inganta aikin ƴansanda, da albashi mai tsoka da muhalli da walwalarsu, abin da ake ganin na taka rawa wajen ta'azzara cin hanci da rashawar da ake zargin wasu ƴansanda da aikatawa.
A Jamhuriyar Nijar, sama da mutum 27 ne kawo yanzu aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon ambaliya da ruwan sama ya haddasa a wasu yankunan kasar.
Wata sanarwa da hukumar kare jama'a ta ƙasar ta fitar a yau Laraba ta ce an yi ƙididdigar ne tun daga ƙarshen watan Mayu, lokacin da damuna ta sauka a ƙasar.
A cewar sanarwar, mutum 23 ne suka jikkata yayin da lamarin ya shafi sama da mutum 10,000 a ƙananan hukumomi 49 na faɗin ƙasar.
Jihar Maradi ce kan gaba a yawan rasa rayuka inda mutum 15 suka rasu.
Wakiliyar BBC a Nijar Tchima Ila Issoufou ta ce mutum 14 sun rasu ta hanyar nitsewa a ruwa, sai kuma 13 da suka rasu saboda rugujewar gidajensu.
Kazalika an samu asarar dabbobi 10,553.
Shugaban Kenya William Ruto ya ba da umarnin sake duba shirin da ake yi na ƙara wa 'yan majalisar ƙasar da kuma ministoci albashi bayan koke-koken da 'yan ƙasar suka yi.
Lamarin na zuwa ne sati ɗaya bayan gagarumar zanga-zanagar da ta tilasta wa shugaban janye sabuwar dokar harkokin kuɗi da ta nemi ƙara haraji.
Mutane sun fara ɗiga ayar tambaya kan dalilin da ya sa za a ƙara albashin 'yan siyasa, ciki har da gwamnoni, yayin da ake fama da matsalar tattalin arziki.
Hukumar tsara albashi Salaries and Remuneration Commission (SRC) ce ta ba da shawarar ƙara kashi biyu zuwa biyar kan albashin duka jami'an gwamnati, wanda ya ƙunshi har da alƙalai.
A shekarar da ta gabata hukumar ta ce tana sa ran ƙarin zai fara aiki ne a farkon wannan watan na Yuli.
Sai dai kuma Ministan Ma'aikan Gwamnati Moses Kuria ya ce ba zai aiwatar da tsarin ba "musamman" a kan ministoci.
Aƙalla mutum biyar ne suka mutu sakamakon wani hari da Rasha ta kai tsakiyar birnin Dniprom na Ukraine, a cewar hukumar hukumomin ƙasar.
An kuma jikkata wasu 47 a harin da aka kai da asubahin Laraba, kamar yadda gwamnan yankin Serhii Lysak ya bayyana a shafinsa na Telegram.
Hukumomi sun ce harin ya kuma lalata shaguna, da makarantu, da asibitoci a yankin.
Mista Lysak ya siffanta harin da "ƙeta". Bidiyo da hotunan da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna dunƙulen hayaƙi da wuta na tashi daga gine-gine.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi tir da harin kuma ya jaddada kiransa ga ƙawayen ƙasarsana ƙasashen Yamma su bai wa gwamnatinsa ƙarin makaman kare sararin samaniya.
"Abu biyu ne kawai za su kawo ƙarshe waɗannan hare-haren na Rasha - kayan kariyar sama na zamani, da kuma makamai masu linzami masu cin dogon zango," a cewarsa cikin wani saƙo shafinsa na zumunta.
Majalisar Dattawan Najeriya ta ankarar da 'yan ƙasar cewa an shigo da wani nau'i na gurɓataccen man fetur da kuma dizel cikin ƙasar.
Da yake gabatar da wani ƙudiri a yau Laraba, Sanata Asuquo Ekpeyong ya ce a ranar 16 ga watan Yunin 2024 wani rahoto ya nuna cewa wasu jiragen dakon kaya 12 sun kai tan 660 na man dizel zuwa birnin Lome na Togo, inda daga nan aka rarraba su zuwa ƙasashen Afirka ta Yamma musamman Najeriya.
A cewarsa, ingancin man bai kai na wanda aka saba amfani da shi a Najeriya ba.
Ya kuma ce duk da hukumar kula da haƙowa da kuma cinikin man fetur ta NMDPRA ta sauya dokokin nau'in man da ake amfani da shi kamar yadda sabuwar dokar man fetur ta tanada, ba ta iya saka ido kan amfani da man a faɗin ƙasar.
Daga baya Majalisar ta kafa kwamatin gaggawa don bincika man da ake shigowa da shi, wanda suka ce yana da haɗari.
Wani sabon hukuncin da Kotun Ƙolin Japan ta yanke zai bai wa dubban mutanen da aka hana su haihuwa ba tare da son ransu ba damar su nemi a biya su diyya.
Kimanin mutum 16,000 ciki har da masu taɓin hankali ne aka tilasta wa ƙin haihuwa a ƙarkashin wata doka da aka soke a shekarar 1996.
Sai dai har ya zuwa yanzu ba a san ko wadanda abin ya shafa za su iya neman diyya ba bayan shigar da ƙara a kotu saboda lamarin ya dade da aukuwa.
Masayo Fururi mai shekaru 71 na daya daga cikin wadanda abin ya shafa da ke fafutukar neman diyyar kuma ta bayyana farin cikinta kan hukuncin.
"A karshe dai sai yanzu ne gwamnati ta shirya neman gafara, don haka na ji dadin hakan. Na shafe sama da shekara 50 ina yaƙar wannan dokar," in ji ta.
Rahotanni na cewa mahaukaciyar guguwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai a Grenada da, Venezuela da St Vincent.
Yanzu haka dai guguwar ta nufi Jamaica da tsibirin Cayman.
A ranar Litinin ne mahaukaciyar guguwar ta faɗa tsibirin Carriacou da ke ƙarƙashin Grenada.
Cibiyar nazari kan bala'o'in guguwa ta Amurka ta yi gargaɗin cewa "Guguwar na barazana ga rayuka saboda mamakon ruwan sama da iska da guguwar ke tafe da su.
Ana sa ran guguwar za ta isa Jamaica a yau Laraba, sannan kuma za ta wuce tsibirin Cayman cikin dare zuwa wayewar gari.
Mahaukaciyar guguwar ta yi ɓarna a Venezuela sakamakon mamakon ruwan sama da ta haifar a wasu yankunan ƙasar.
Ga hotunan yadda guguwar ta yi ɓarna a jihar Sucre ta ƙasar Venezuela.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce hukumomin jin ƙai a Sudan na fuskantar matsalar satar kayayyakin agaji sakamakon yaƙin da ake yi tsakanin sojoji da dakarun RSF.
Wani babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya,Toby Harward ya shaida wa BBC cewa satar ta yi sanadiyyar asarar miliyoyin daloli.
Ya ce "Mun rasa kayyaykin tallafi da motoci da ofisoshi da sauran kayayyakin aiki da suka kai ɗaruruwan milyoyin dala a sansanonin mu da ke sassa daban daban na kasar,kusan kowane yanki da dakarun RSF suka ƙwace ya fuskanci wannan matsalar.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa za a fuskanci matsananciyar yunwa a ƙasar ta Sudan inda mutane miliyan ashirin da biyar ke bukatar agajin gaggawa.
Wata mata da haifi ƴan huɗu ta bayyana farin cikinta.
Arlene da John Mitchell, da ke Longridge Yammacin Lothian sun zama iyaye ga Ben da Noah da Harrison da Rosy a ranar 14 ga watan Mayu.
Ƙaramin cikinsu, Horrison na da nauyin 2lb 14oz, yayin da Ben da Noah da Rory kowannensu na da nauyin 2lb 15oz
Arlene ta ce ta yi matuƙar farin ciki da haihuwar ƴan hudu.
Ba'a cika samun ƴan huɗu ba, inda likitoci suka ce aƙalla ana samun guda a duk cikin haihuwa 700,000.
Su ne ƴan hudu na farko da aka fara haifa a Lothian.
Arlene ƴar shekara 34 da mijinta mai shekara 38 na da ƴa ƴar shekara 11 mai suna Lauren da kuma ɗa namiji mai shekara uku, Hunter.
Sojojin Isra'ila na ci gaba da fafatawa da mayaƙan Hamas da kungiyar Islamic Jihad a wani yankin birnin Gaza.
Wakiliyar BBC ta ce "an umarci Falasɗinawa da su nemi mafaka a wani yanki da ke gaɓar teku mai ƙarancin ababen more rayuwa amma rahotanni sun ce wani harin da Isra'ila ta kai yankin ya kashe wasu mutane da suka yi hijira daga yankin Khan Younis.
Ana jin ƙarar fashewar abubuwa da harbe-harbe a faɗin birnin Gaza yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a gundumar Shujaiya. A halin da ake ciki, dubban Falasɗinawa da ke kudancin Gaza na ci gaba da neman mafaka bayan sun tsere daga yankin Khan Yunis.
Wata mahaifiya ta amince cewa ita ta bai wa ɗanta mai shekara bakwai da ke fama da jinyar ajali sinadarin morphine da nufin kawo ƙarshen wahalar da yake sha.
Antonya Cooper, 'yar yankin Abingdon da ke kudu maso gabashin Ingila, ta ce ɗan nata, mai suna Hamish na fama da cutar kansa da ta kai mataki na huɗu, kuma yana fama da raɗaɗin zafin jinya, kafin rasuwarsa a 1981.
A yayin da a yanzu ita ma take fama da cuta maras warkewa, matar da faɗa wa BBC cewa ta yi hakan ne a wani ɓangare na bayar da gudunmowarta wajen taimaka wa mutane su mutu.
Taimaka wa mutane su kashe kansu da gangan haramtaccen laifi ne a Ingila.
Hamish na fama da kansar da ta fi kama ƙananan yara, wadda ba kasafai ake samun irinta ba.
An gano yana ɗauke da cutar tun yana da shekara biyar, inda ka fara ba shi magungunan da zai sha wa tsawo wata uku.
Mahaifyar yaron ta ce bayan shafe aƙalla wata 16 yana karɓar magani a asibiti, ciwon nasa ya tsananta inda yake fama da raɗaɗin ciwo.
''A daren da zai mutu, yana ta faɗa min cewa raɗaɗin ciwo na damunsa na taimaka masa, sai na ce masa kana so na cire maka ciwon? sai ya ce e mama ina so?'', in ji ta.
''Sai na saka masa sinadarin morphine mai yawa ta robar cin abincinsa, kuma hakan ne ya zama ajalinsa'', in ji mahaifiyar.
BBC ta tambayi matar ko ɗan nata na sane da aniyarta a kansa kafin mutuwar tasa?, sai ta ce tausayin da take yi masa kan yadda yake shan wahala ne ya sa ta aikata masa hakan.
Bayan shekara 40 da kisan ɗan nata, a yanzu ita ma Antonya Cooper na fama da wani nau'i na cutar kansar.
Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi gwamnatin kasar ta koma amfani da fasahar zamani a yanƙin da take yi da mayakan Boko Haram da 'yan bindiga da sauran masu ɗauke da bindiga.
Hakan na ƙunshe cikin ƙudurin da Sanata Ali Ndume ya gabatar don ɗaukar matakin gaggawa kan harin da aka kai a yankin Gwoza da yake wakilta.
Bayan doguwar muhawara da aka kwashe sa'o'i ana yi tare da jajantawa kan harin, majalisar ta yarda cewa amfani da fasahar zamani a yaƙin zai kawo ƙarshen masu kai hare-haren ƙunar baƙin wake.
Haka kuma Majalisar ta amince a ƙara bayar da muhimmanci a yankin tafkin Chadi da dajin Sambisa da Kuma hayin dutsen Mandara.
Da yake bayar da tasa gudunmuwar, Sanata Adam Oshimole ya ce bai kamata a ƙara wa sojoji kuɗi ba da zimmar samar da makaman zamani da kuma fasaha, yana cewa an ba su kuɗaɗen da suke isassu a wannan lokaci.
Sai dai majalisar ta ƙi amincewa da bukatar tasa, inda mafi yawan mambobinta suka yi watsi da buƙatar.
Kazalika wasu daga cikin sanatocin sun nemi gwamnatin Najeriya ta haɗa hannu da kamfanonin tsaro masu zaman kansu domin ci gaba da yaƙi a yankunan Tafkin Chadi da dajin Sambisa da sauran wasu yankuna da ke fama da matsalar tsaro a Najeriya.
Tawagar Likitoci daga ƙungiyar agaji ta 'International Committee of the Red Cross (ICRC) za ta tallafa wa likitocin asibitin Maidugiri wajen yi wa mutanen - da harin ƙunar baƙin wake a Gwoza - magani.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce tawagar ƙwararrun likitocin nata za ta yi aiki da likitin asibitin koyarwa na birnin Maiduguri wajen ceto rayukan mutanen da harin ya yi musu mummunar illa.
Mutane da dama ne suka samu munanan raunuka a lokacin harin da wasu 'yan ƙunar baƙin wake suka kai garin Gwoza a ƙarshen mako.
An kai mutum 41 da suka jikkata zuwa asibitin na Maiduguri, da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ranarkun Asabar da Lahadi domin ba su kulawar gaggawa.
Ƙungiyar ICRC ta kuma bayar da tallafin magunguna da wasu kayyaki ga asibitin domin taimaka wa ɓangaren kula da masu buƙatar kulawar gaggawa.
Mataimakiyar shugaban tawagar ƙungiyar da suka je Maiduguri, Diana Japaridze ta ce halin da marasa lafiyar ke ciki a asibitin ''abin tayar da hankali ne''.
“Muna kira da babbar murya cewa a yaƙi dole a kare fararen hula musamman mata da ƙananan yara, kuma asibiti wuri ne na ceton rai, ba wurin salwantar da rai ba.”
''Hari kan mai uwa da wabi kan fararen hula, abu ne da ya saɓa wa dokokin duniya, haka ma cibiyoyin kula da lafiya da ma'aikata, su ma dole ne su samu kariya, ba a kai musu hari ba'', in ji ta.
A ranar Asabar ne wasu mata huɗu suka tayar da boma-bomai a wurare daban-daban a Gwoza lokacin da ake tsaka da bikin aure.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 32 tare da jikkata gommai, kamar yadda mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana.
Jami'an ƙasar Mali sun ce wasu ƴan bindiga sun kai hari tare da kashe kusan mutum 40 a wani ƙauye da ke yankin tsakiyar Mali mai fama da ta'addanci.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce harin ya auku ne a ranar Litinin a ƙauyen Djiguibombo da ke yankin Mopti, ɗaya daga cikin yankunan arewaci da tsakiyar Mali da ke fama da ayyukan masu iƙirarin jihadi masu alaƙa da al-Qaeda tsawon gomman shekaru.
Reuters ɗin ya ambato magajin garin Bankass, Moulaye Guindo na cewa "hari ne mai matuƙar muni inda ƴan bindigar suka yi wa ƙauyen ƙawanya tare da buɗe wa mutane wuta".
Mista Guindo bai bayyana adadin mutanen da suka mutu a harin ba, amma wasu jami'an ƙasar da suka nemi a sakaya sunansu sun bayyana wa Reuters cewa kusan mutum 40 aka kashe.
"Sun yi wa ƙauyen ƙawanya, yayin da ake gabatar da bikin aure, an shiga ruɗani inda wasu suka samu tserewa amma an kashe wasu da dama da mafi yawansu maza ne", in ji ɗaya daga cikin jami'an ƙasar.
Hukumomin ƙasar dai ba su bayyanasu wane ne maharan ba, kuma kawo yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin.
Ƙasar Mali dai ta jima tana fama da ayyukan masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka shafe gomman shekaru suna kai hare-hare a wasu sassan ƙasar.