Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 31/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 31/07/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Ba za mu jingine yajin aiki ba har sai an biya mana buƙatunmu'

    Shugaban ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Najeriya, Morakinyo-Olajide Rilwan ya ce mambobinsu za su ci gaba da yajin aiki ne har sai gwamnatin ƙasar ta kammala biya musu manyan buƙatun da suka gabatar.

    A ranar Laraba ne ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai a faɗin ƙasar, duk kuwa da ganawa da suka yi da ministan ƙwadagon ƙasar gabanin fara yain aikin.

    Yayin wata hira da gidan talbijin na Channels, Rilwan ya ce ƙungiyarsa za ta rufe kunnuwanta daga kiraye-kirayen janye yajin aikin da ake yi mata matsawar ba a biya mata buƙatunta ba.

    Buƙatun ma'aikatan jinyar dai sun haɗar da:

    • Gyara alawus ɗinsu na aikin dare.
    • Ƙara kuɗin alawus na tufafinsu na aiki.
    • Samar da tsarin albashi na musamman domin ma'aikatan jinya kawai.
    • Kara alawus na ƙarin ayyukan da suke yi bayan ainihin aikinsu.
    • Gwamnati ta ɗauki ma'aikatan jinya da yawa aiki domin rage karancin ma'aikata.
    • Gwamnati ta buɗe sashen ma'aikatan jinya a Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya domin kula da buƙatun aikin jinya kai tsaye.
  2. Lauyoyin Succès Masra sun soki mayar da shari'arsa kotun ICC

    Lauyoyin jagoran adawar Chadi da ke tsare, Succès Masra sun soki matakin mayar da shari'arsa zuwa kotun hukunta manyan laifuka a matsayin cin zarafin siyasa.

    A watan Mayu ne aka kama tsohon firaminsitan kan zarge-zarge masu yawa ciki har da zargin haddasa rikicin ƙablinaci da kisan kai.

    Jam'iyyarsa ta Les Transformateurs ta ce ana yi masa shari'a ne da nufin rufe bakin ƴan hamayya a Chadi.

    Ƙungiyar kare hakƙin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce matakin ya saɓa da yarjejeniyar sasancin da ta kawo ƙarshen rikicin siyasa a ƙasar.

    A shekaru uku da suka gabata ne jami'an tsaro Chadi suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar neman maido da mulkin farar hula a ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane.

  3. Abin da ya sa na gana da Tinubu - Kofa

    Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga jihar Kano, Hon Abdulmumini Jibrin Kofa ya ce ya ziyarci shugaban ƙasar Bola Tinubu a fadarsa ne domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa.

    A ranar Laraba ne ɗan majalisar, wanda kuma jigo ne a jam'iyyar NNPP mai hamayya ya ziyara shugaban ƙasar a fadarsa da ke Villa a wani abu da mutane da dama ke mamakinsa.

    Sai dai ɗan majalisar ya ce ziyarar tasa ga Tinubu ba abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da alaƙar da ke tsakaninsu da ma jagoran NNPP.

    ''Babu mamaki idan aka yi la'akari da daɗaɗɗiyar abotar da ke tsanakin shugaban ƙasar da kuma jagoran jam'iyyar ta NNPP, Sanata Rabi'u Kwankwaso'', kamar yadda ya bayyana wa manema labarai jim kaɗan bayan ganawar.

    Da aka tambaye shi ko ziyarar tasa na da alaƙa da raɗe-raɗin komawar Sanata Kwankwaso APC, sai ɗan majalisar ya ce ba lokacin wannan maganar ba ne yanzu, amma kuma komai zai iya faruwa.

    ''Kuma idan lokaci ya yi komai zai fito fili, kuma kowa zai ji'', in ji shi.

  4. Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da ci gaba da tsare wani fitaccen mai amfani da shafukan sada a Najeriya mai suna Ghali Isma'ila da aka fi sani da Sultan kan zargin yaɗa wani bidiyo kan 'lafiyar' shugaba Tinubu.

    A ƙarshen makon da ya gabata ne aka kama Sultan tare da tsare shi kan zargin da Amnesty ta bayyana da maras tushe.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce kamun da hukumar DSS ta yi wa matasahin ɗan asalin jihar Kano ya saɓa wa doka.

    Amnesty ta kuma zargi jami'an DSS da zuwa gidan yarin da aka tsare Sultan tare da tilasta masa ba su lambobin sirrin buɗe wayoyinsa da na shiga shafukan sada zumuntarsa (Password) ba tare da tuntuɓar lauyoyinsa ba.

    Ƙungiyar ta Amnesty ta ce hakan ya saɓa wa ƴancinsa na tsare sirri da ƴancin faɗar albarkacin baki.

    Amnesty ta kuma soki yadda hukumomin Najeriya ke kamawa tare da razana masu amfani da shafukan sada zumunta wajen hana su bayyana ra'ayinsu.

    Daga ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin na Najeriya su gaggauta sakin matashin ba tare da wasu sharuɗɗa ba.

  5. Gini kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri - NEMA

    Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta ce mamakon ruwan sama da yin gine-gine kan magunan ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri.

    A ranar Laraba ne aka samu rahotonni ambaliya a wasu unguwannin birnin Maiduguri da yankin ƙaramar hukumar Jere sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka shafe tsawo sa'a uku a tafkawa a birnin.

    Cikin wata sanarwa da shugaban hukumar NEMA, Zubaida Umar ta wallafa a shafinta na Facebook ta danganta ambaliyar da rashin bin tsarin gine-gine.

    ''Ambaliyar na da alaƙa da mamakon ruwan sama da aka samu a birnin da kuma rashin kula da kwalbatoci da yin gine-gine kan hanyoyin da ruwa ke bi'', in ji shugabar ta NEMA.

    Hukumar ta NEMA ta ce jami'anta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi sun taimaka wajen ceto mutanen da ambaliyar ta rutsa da su tare da rage illar ambaliyar.

    Ambaliyar na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan wata mummunar ambaliyar da ta auka wa yankin, wadda ta yi sanadiyyar raba fiye da mutum miliyan guda da muhallansu.

  6. Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas

    Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan sanar da shirinta na amincewa da ƙasar Falasdinu - kasa ta uku da ta sanar da matakin a cikin yan kwanakin nan.

    Firaministan Canada, Mark Carney, ya ce yana fatan samar da ƙasashe biyu domin tabbatar da samar da zaman lafiya.

    Ya ce matakin zai faru ne a watan Satumba idan har hukumomin Falasɗinawa suka gudanar da sauye-sauyen dimokradiyya.

    Matakin na Canada bayan na Faransa da Birtaniya ya ci gaba da mayar da Amurka saniyar ware a goyon bayan da take ci gaba da bai wa Isra'ila a yakin Gaza.

    Shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa shawarar da Canada ta yanke zai zamar mata wahala wajen ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da Amurka.

  7. Boko Haram na barazanar dawowa Najeriya saboda yunwa - MDD

    Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa rashin tallafin agaji zai jefa sama mutum miliyan guda a yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin barazanar Boko Haram.

    WFP ta ce kuɗinta sun ƙare don haka ba za ta iya ci gaba da tallafa wa mutanen da suka tsere wa rikicin Boko Haram ba.

    Ta yi fargabar cewa hakan zai tilatas wa mutane shiga ƙungiyar ta Boko Haram.

    Kungiyar agaji ta likitocin MSF ta ce rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara sama da 600 a yankin a wannan shekara.

  8. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Barkanmu da sake haɗuwa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan shafukanmu na sada zumunta kan labaran da muke wallafawa.