Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin namu na ranar Alhamis 31 ga watan Yulin 2025.
A madadin sauran abokan aiki, A’isha Jaafar ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 31/07/2025
Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin namu na ranar Alhamis 31 ga watan Yulin 2025.
A madadin sauran abokan aiki, A’isha Jaafar ke cewa mu kwana lafiya.
Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da sama da Naira triliyan 68 domin ayyukan samar da wutar lantarki a jamio'i da asibitocin koyarwa a faɗin ƙasar.
Ministan makamashi Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a ƙarshen taron majalisar na yau, wanda shugaban ƙasar Bola Tinubu ya jagoranta.
Ya ce shirin ya nuna jajircewar gwamnatin ƙasar wajen tabbatar da samun wutar lantarki a muhimman fannoni kamar na lafiya da na ilimi.
Adelabu ya kuma bayyana halin da wutar lantarkin ke ciki a yanzu a matsayin abin damuwa kuma wanda ke kawo cikas ga samar da lafiya da ilimi yadda ya kamata.
Za a yi amfani da kuɗin domin taimakawa wajen samar da wuta a jam'ioi da asibitocin koyarwa 8 a faɗin ƙasar.
Ciki har da Jam'iar jihar Legas, da Jam'iar Ahmadu Bello da ke Zaria, sai Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-ife.
Sai kuma Jam'iar Najeriya da ke Nsukka, da Jami'ar Ibadan, da kuma Jam'iar Calabar da sauransu.
Ya kuma ce ana sa ran kammala ayyukan samar da wutan nan da watannin 7 zuwa 9.
Gwamnonin jihohi 36 a Najeriya sun bayyana damuwarsu kan halin da ilimin ƙasar ke ciki.
Shugaban ƙungiyar gwamonin kuma gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron kara wa juna sani kan ilimin matakin farko da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya kuma bayyana damuwa kan cewa ma'aikatan fannin ilimin sun yi karanci kuma ba a martaba su yadda ya kamata.
Fannin ilimin Najeriya dai na fama da matsaloli da dama, kamar karanci da kuma rashin ƙwarrarun ma'aikata, da rashin isassun kayan aiki, da rashin ilimi mai inganci.
Ko a farkon wannan shekara Ministan ilimi na ƙasar Tunji Alausa ya ce gwamnatin ƙasar na aiki tare da gwamnonin jihohi domin magance matsalolin da ke fannin da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, inda ya ce adadin yaran abu ne mai tayar da hankali.
Wata kotun hukunta 'yan ta'adda a Pakistan ta yankewa mambobin jam'iyyar tsohon firaiministan kasar Imran Khan su fiye da 100 hukunci saboda rawar da suka taka a yayin zanga zangar kin amincewa da gwamnatin kasar shekaru biyu da suka wuce.
Wasu manyan 'yan jam'iyyar ta PTI, an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara 10.
Kama Imran Khan a 2023, ya janyo zanga zanga a sassan Pakistan inda magoya bayansa suka nuna kin amincewa da matakin gwamnati na kama shi.
Shugaban jam'iyyar Gohar Ali Khan, ya ce za su kalubalanci hukuncin kotun.
Amurka ta kakaba takunkumai kan wasu jami'an gwamnatin Falaɗinawa, a ranar da jakadan Amurka a gabas ta tsakiya Steve Witkoff ke ziyara a Isra'ila domin ceto tattaunawar tsagaita wuta a Gaza.
Amurka ta ce takunkumin zai shafi wadanda ake zargi da taimakawa wajen kazancewar ayyukan ta'addanci da kuma fadada rikicin Gaza.
Wannan matakin dai zai hana jami'an da abin ya shafa damar shiga Amurkar.
Fadar gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa Mr Witkoff zai je Gaza a gobe Jumma'a inda zai duba yadda ake rabon kayan agaji da kuma lalubo wasu hanyoyin da za a ƙara shigar da kayan agaji Gaza.
Shugabar Mexico Claudia Sheinbaum ta ce ita da shugaban Amurka Donald Trump, sun amince da ɗage shirin ƙara harajin kashi 30 kan kayyayakin ƙasar ta na tsawon kwana 90.
Tun da farko an shirya cewa ƙarin zai soma aiki ne a ranar Juma'a.
Sheinbaum ta ce jinkirin zai bayar da damar ci gaba da tattauna yarjejeniyar kasuwanci na tsawon lokaci tsakanin ƙasashen biyu.
Kafin nan, Mexico za ta ci gaba da biyan harajin kashi 25 kan kayyaykinta da ke shiga Amurka.
Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon, kan wuraren da Hezbollah ke ƙerawa da kuma ajiye makamai masu linzami.
Ministan tsaron Israila Isreal Katz, ya ce Isra'ila za ta kai munanan hare hare kan ƙungiyar idan ta yi yunƙuri dawo da ƙarfinta da kuma yi mata barazana.
Tun da farko shugaban Lebanon Joseph Aoun ya ce a shirye yake ya sa Hezbollah ta ajiye makamanta duk da zanga zangar da ƙungiyar ke yi kan cewa yin hakan zai biya buƙatun Isra'ila.
Ƙungiyar ta rage ƙarfinta sosai lokacin yaƙinta da Isra'ila. A watan Nuwamban bara ne aka cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu.
Wata babbar kotu da ke jihar Kwara a kudu maso yammacin Najeriya ta yanke wa Abdulrahman Bello, wanda ya kashe masoyiyarsa Yetunde Lawal hukuncin kisa ta hanyar rataya.
An zargi Abdulrahman da laifin kisan matashiyar yar shekara 23, kuma dalibar kwalejin ilimi na jihar Kwara da ke Ilorin a watan Fabrairun 2025.
Yan sandan jihar sun kama matashin ɗan shekara 29 bisa zarginsa da kashe ta da kuma daddatsa gawar ta.
Mai shariah Hannah Ajayi ce ta yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi, inda ta ce shaidu sun nuna Bello ya kashe Yetunde ne domin ya yi amfani da gawar ta wurin yin tsafi, ya kuma sayar da sassan jikinta.
A cewar Hannah Ajayi, soyyayar da yake mata da alƙawarin aurenta, ƙarya ne, kuma ya yi mata su ne da nufin yaudarar ta ta je gidansa domin ya kashe ta.
Ƴan sandan jihar sun bayyana cewa Yetunde ta ɓace ne a ranar 10 ga watan Fabrairu, kuma bayan kwana huɗu aka gano gawar ta a gidan wanda ya kashe ta.
Majalisar ɗinkin duniya ta yi kiran a gudanar da bincike a Angola bayan gwamnatin ƙasar ta ce mutane 20 sun mutu a zanga zangar da aka yi a baya baya nan kan ƙarin farashin man fetir.
Ofishin kare haƙƙin bil Adama na Majalisar ya ce hukumomin Angola sun yi amfani da ƙarfi fiye da kima, bayan wasu rahotanni da ke nuna an harba harsasai wajen tawatsa masu zanga zangar.
Majalisar ɗinkin duniya ta kuma buƙaci masu bayyana ra'ayoyisu a kan tituna da su yi hakan cikin kwanciyar hankali da lumana.
A ranar Litinin da Talata, an yi ta sata a wasu sassan babban birnin ƙasar Luanda, da ma wasu biranen.
Shugaban Amurka Donald Trump ya dage kan cewa wajibi ne a samar da yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a ƙarshen wa'adin da ya bayar na 8 ga watan Agusta, a cewar wani babban jami'in diflomasiyya na Amurka.
John Kelley ya shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya cewa Amurka a shirye ta ke ta ɗauki wasu matakai domin samar da zaman lafiya, sai dai bai yi ƙarin bayani kan ko waɗanne matakai ba ne.
Kalaman sa na zuwa ne bayan harin da Rasha ta kai Kyiv, babban birnin Ukraine da jirage marasa matuƙa waɗanda suka kashe mutane 13 da kuma jikkata wasu 130.
Rasha ta yi lugudan wuta a Ukraine da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami inda ta kai hare haren Kyiv, babban birnin kasar.
Aƙalla mutum 15 ne suka mutu yayin da wasu 145 suka jikkata, kuma adadin na ci gaba da ƙaruwa.
Wurare 27 a sassan Kyiv harin ya shafa ciki har da gidaje, inda aka kashe mutane da dama daga cikinsu akwai wani yaro dan shekara 6 da mahaifiyarsa.
Rundunar sojin saman Ukraine ta ce Rasha ta harba jirage marasa matuƙa 309 da makamai masu linzami 8.
Rashan ta kai hare haren ne cikin dare duk da sabon wa'adin kwanaki 10 da shugaba Trump ya bai wa takwaransa na Rashan akan ya bayar da amsa a game da buƙatar tsagaita wuta.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce yanzu duniya ta ga zahirin aniyar Rasha na rashin son zaman lafiya.
Gwamnatin mulkin sojan Myanmar ta ayyana kawo karshen dokar ta-ɓaci da aka kafa shekaru hudu da rabi da suka gabata lokacin da ta hamɓarar da zaɓabbiyar gwamnatin Aung San Suu Kyi.
Rundunar sojin ta ce tana shirin gudanar da zaɓuka a watan Disamba.
Babu wata rana da aka ware a watan, to amma masu suka da kuma ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun ce akwai yiwuwar koda an yi zaɓen, sojojin za su ci gaba da kasancewa masu karfin faɗa aji.
A ɓangare guda kuma, makwabciyar ƙasar China ta bayyana aniyarta na bayar da gudunmuwa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar ta Myanmar.
Matakin da gwamnatin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ta ɗauka na sanya hannu kan wata jarjejeniya da ƙungiyar Barcelona na fuskantar suka a faɗin ƙasar.
Wasu masu sukar na cewa me ya sa ba za a zuba kuɗin domin farfaɗo da gasar ƙwallon ƙafar ƙasar mai fama da rashin kuɗi.
A ƙarƙashin yarjejeniyar - wadda za ta laƙume dala miliyan 50 - Barcelona za ta saka ''DR Congo - Heart of Africa" a bayan rigunan ƴanwasanta na atisaye.
Hukumomin DRC sun ce yarjejeniyar ta ƙunshi samar da sansanin horarsa da matasan ƴan wasan ƙasar, da kuma wasan sada zumunta da za a buga a filin wasan Barcelona, matakin da hukumomin suka ce zai taimaka wajen ɗaga darajar ƙasar.
Ƙasar ta DR Kongo ta sanya hannu kan irin wannan yarjejeniyar da ƙungiyoyin AC Milan ta Italiya da Monaco Faransa.
Tsohon ɗan jamalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kogi ta Yamma ya koma jam'iyyar haɗakar ADC bayan ficewarsa daga PDP.
Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, an ga yadda Dino Melaye ya karɓi katin jam'iyyar ADC daga hannun jagororin jam'iyyar na ƙaramar hukumarsa.
Tun da farko a yau ne Dino Melaye ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP bayan ya rubuta wa jagororin jam'iyyar na mazaɓarsa ta Aiyetoro Gbede wasiƙar ficewarsa daga jam'iyyar.
A cikin wasiƙar Melaye ya bayyana dalilan kasawar jam'iyyar wajen magance matsalolin da ke damunta.
''Matakin ya zama wajibi saboda gazawar jam'iyyar wajen ceto yan Najeriya daga cikin kuncin da ƙasarmu ke ciki", kamar yadda wasiƙar ta bayyana.
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kogin na jam'iyyar PDP ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari kan halin da jam'iyyar ke ciki.
Ƙasar Iran ta ce ba za ta sake komawa teburin sulhu da Amurka kan shirin nukiliyarta ba, har sai Amurkan ta yarda za ta biya ta diyya kan ɓarnar da aka yi mata a yaƙin watan da ya gabata.
Haka kuma Iran ta ce tana buƙatar ƙarin bayani daga Amurka kan dalilin da ya sa ta kai mata hari bayan kuwa suna tattaunawa kan shirin nukiliyar tata.
Iran ta ce hare-haren Amurka da Isra'ila a ƙasar sun kashe fiye da Iraniyawa dubu ɗaya a tsawon kwana 12 da aka kawashe ana yaƙin.
Amurka da Isra'ila dai sun ce ba za su bari Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.
Sai dai Teheran ta dage cewa shirin nikiliyarta na zaman lafiya ne kawai.
Hukumar agajin gaggawar Hamas ta ce aƙalla Falasɗinawa 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon harbin bindiga daga sojojin Isra’ila yayin da suke jiran karɓan abinci a arewacin Gaza.
Hukumomin lafiya a Gaza sun kuma ce wasu fiye da 300 sun jikkata.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce sun yi harbin gargaɗi ne ga mutanen da suka taru kusa da motocin ɗaukar kayan agaji, amma ba su da tabbacin an samu asarar rai daga harbin da suka yi.
Asibitin al-Shifa a birnin Gaza ya ce an kai masa gawarwakin mutum 35, sai dai daga baya ya ce adadin ya ƙaru zuwa 48, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP
A wani labarin kuma, wasu asibitoci a Gaza sun shaida wa BBC cewa mutum shida sun mutu a kusa da cibiyar raba agaji ta Gaza da ke Rafah.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da tsawaita wa'adin shugaban hukumar kwastam ta ƙasar, Bashir Adeniyi.
Cikin wata sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Tinubu ya tsawaita wa'adin Adeniyi - wanda zai ƙare ranar 31 ga watan Agusta mai zuwa - da shekara guda.
Sanarwar ta ce tsawaita wa'adin zai bai wa Adeniyi damar ƙarasa aiwatar da sauye-sauye masu muhimmanci da hukumar ke gudanarwa ƙarƙashin mulkin Tinubu.
“Shugaban ƙasa na da ƙwarin gwiwar tsawaita wa'adin zai ƙarfafa ayyukan hukumar wajen tsara manufofin kasuwanci da karɓar haraji da tabbatar da tsaron kan iyakoki'', in ji sanarwar.
A watan Octoban 2023 ne Tinubu ya naɗa Adeniyi a matsayin shugaban hukumar kwastam ta Najeriya.
Kafin nan ya riƙe mukamin a matsayin shugaban riƙo bayan saukar tsohon shugaban hukumar Hameed Ali.
Jami'ai a China sun ce mummunar ambaliyar ruwa ta kashe mutum 31 da ke zaune a gidan gajiyayyu a wajen birnin Beijing.
Hotunan da aka yaɗa sun nuna tawagar jami'an agajin gaggawa na amfani da rigunan shiga ruwa a ƙoƙarin kuɓutar da mutanen da suka maƙale a gidan gajiyayyun da ke gundumar Miyun.
Da dama cikin waɗanda suka mutun ba sa iya tafiya, balle su tsira da rayukansu.
Jami'ai a yankin sun ce lamarin ya munana, kuma za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki domin kauce wa faruwar hakan a nan gaba.
Kafofin yaɗa labaran China sun ce akwai kimanin mutu 77 a cikin gidan lokacin da lamarin ya faru, lamarin da ya sa kusan mutum 40 suka maƙale.
Kimanin mutum 44 ne suka mutu sakamakon ambaliyar da ta auka wa Beijing a lokacin da China ke fama da zafin bazara.
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara yi wa ɗaliban jami'o'in ƙasar gwajin shan ƙwayoyi a wani mataki da daƙile yaɗuwar ta'ammalai da ƙwayoyin.
Ma'aikatar ilimin ƙasar tare da haɗin gwiwar hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar NDLEA ne za su jagoranci aiki, kamar yadda wata sanarwa da hukumar NDLEAn ta fitar.
Hakan na zuwa ne bayan ganawar shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa.
Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta'ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren ƙasar.
Buba Marwa ya tabbatar wa BBC cewa gwajin ƙwayar zai shafi duka ɗaliban jami'o'in da sabbin da za su shiga.
Yayin da yake jawabi a wajen ganawar, Buba Marwa ya ce za su mayar da hankali ne kan makarantun ƙasar, waɗanda ya ce akwai miliyoyin yara da ke ƙarƙashin kulawar ma'aikatar ilimin ƙasar.
Buba Marwa ya ce rashin daƙile ta'ammali da miyagun ƙwayoyi daga wajen ƙananan yara ya taimaka wajen jefa matasan ƙasar cikin ayyukan ta'addanci da fashin daji da sauran miyagun laifuka.
Kenya ta ayyana matakin taƙaita sayar da barasa a faɗin ƙasar.
Shirin - mai cike da taƙaddama - ya ƙunshi ƙara yawan mafi ƙanƙantar shekarun da za a yarje wa masu shan barasar daga 18 zuwa 21.
Haka nan matakin zai haramta sayar da barasar a manyan kantunan da wuraren cin abinci da otal-otal.
Wasu ƴanƙasar dai sun yi gargaɗin cewa matakan za su iya shafar fannin martaba baƙi a ƙasar.
Jami'an ƙasar sun ce za a ɓullo da matakan ne da nufin kare matasa daga cutar da kawunansu ta hanyar shan barasar.
Gwamnatocin Kenya da suka gabata sun yi yunƙurin taƙaita shan barasar da ake sarrafawa a ƙasar, da aka fi sani da Chag'aa.