Mutum 80 da aka sace a jihar Kaduna sun koma gida
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce mutum 80 daga cikin masu ibada da aka sace sun koma gidajensu lafiya, makonni bayan aukuwar lamarin.
Mutanen na daga cikin mutum 177 da aka yi garkuwa da su daga coci uku a Kurmin Wali, wani yanki dake Kajuru a arewacin jihar Kaduna.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mansur Hassan, ya shaida wa BBC cewa mutanen sun tsere ne a ranar da aka sace su, a lokacin da ’yan bindigar ke ƙoƙarin kwashe su zuwa wani wuri.
Ya ce bayan tserewar, sun ɓuya a wasu ƙauyuka na kusa tsawon makonni, inda suka jira har sai sun ga yanayin wurin ba matsala kafin su koma gida.
DSP Mansur ya ce an tantance mutanen tare da kuma duba lafiyarsu sannan daga bisani aka haɗa su da iyalansu.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutum 86 da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutanen.
Harin na Kurmin Wali na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke addabar Najeriya, musamman a jihohin arewa, inda ake fama da hare-haren ’yan bindiga da sace-sacen mutane da kashe-kashe.
Hukumomi sun sha bayyana cewa suna ƙara tsaurara matakan tsaro da haɗa kai da al’umma domin daƙile irin waɗannan hare-hare.