Nan da wata shida za a kammala ginin majalisar dokokin jihar Rivers - Ibas

Asalin hoton, Ibok-Ete Ekwe Ibas
Shugaban gwamnatin riƙon-ƙwarya na jihar Rivers, Ibok Ibas ya ce nan da wata shida za a kammala sake gina majalisar dokokin jihar.
Ibas ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a harabar majalisar a ranar Asabar, inda ya ce ya lura akwai buƙatar kammala ginin.
Ya buƙaci ɗan kwangilar da ke aikin da ya ƙara ƙaimi wajen kammala ginin kamar yadda aka amaince a yarjejeniyar kwangilar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa, daga cikin aikin da aka ba shi akwai tabbatar da majalisar jihar ta dawo da ƙarfinta.
"Na ga yadda ɓangaren zartasta yake, yanzu abin da ake buƙata shi ne inganta ɓangaren majalisa. Kuma ba za su yi aiki cikin natsuwa ba, sai sun samu wurin aiki mai kyau," in ji Ibas, wanda ya samu rakiyar, shugaban ma'aikatan jihar, Dokta George Nwaeke.














