Aƙalla mutum shida sun mutu a wani harin ƙunar-baƙin-wake a Pakistan
Aƙalla mutum shida ne suka mutu a wani harin ƙunar-baƙin-wake da aka kai masallacin wata makarantar Islamiyya a yankin arewa maso yammacin Pakistan inda aka san jagororin Taliban na karatu a can.
Shugaban makarantar, Hamid ul Haq, na daga cikin waɗanda suka rasu a harin.
Ba wata ƙungiya zuwa yanzu da ta fito ta ɗauki alhakin kai harin.
Waɗanda suka ga harin sun gaya wa BBC, ɗaruruwan jama'a sun taru a babban a masallacin makarantar.
An kai harin ne a masallacin Dar-ul-Uloom Haqqania bayan sallar Juma'a
Shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, da Taliban sun yi Allah-wadari da harin.