Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 28/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjbir, Annur Muhammad, Isiyaku Muhammed, Umar Mikail da Ahmad Bawage

  1. Farashin mai ya sauka a kasuwannin duniya saboda harin Isra'ila a Iran

    Farashin mai ya yi ƙasa a kasuwannin duniya bayan da Isara'ila ta mayar da martani hare-hare a ƙasar Iran ranar Asabar. Da farko dai an samu hauhawar farashin man ne saboda fargabar da ake da ita na cewa Isra'ila za ta iya kai hare-hare kan wuraren samar da man fetur na Iran.

    Sai dai kuma bayan hare-haren martanin, sai farashin man ya sauka da kashi huɗu cikin ɗari.

    Tun da farko, Iran, ta yi alƙawarin mayar da wani martanin wanda a cewarta daidai da wanda ya dace na hare-haren da Isra'ilar ta kai kan sansanin soji da cibiyoyin samar da makamai na ƙasar.

    Zaman tankiya a tsakanin ƙasashen biyu ya ƙara tsananta ne bayan Iran ta harba makamai a Isra'ila a matsayin martani da kashe shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah da Isra'ilar ta yi, wanda tun a lokacin Isra'ilar ta ƙuduri aniyar mayar da martani.

    Tun a lokacin ne Amurka take ta nanata matsayarta ta cewa ba ta so Isara'ila ta kai hari a sansanonin nukiliyar Iran.

  2. Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa kan rashin wutar lantarki a arewa

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin jin daɗinsa kan rashin wutar lantar a mafi yawan jihohin Arewa.

    Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce, "Abin takaici ne a ce mafi yawan yankunan Arewa suna zaune cikin duhun rashin wutar lantarki saboda tangarɗa a layin lantarkin 330kV wanda ya ɗauko wuta daga Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ne yake ba jihohin Kano da Kaduna, da layin da yake ba Bauchi da Gombe da wasu jihohin arewa maso gabas wuta.

    "Matsalar ta ƙara ta'azzara ce saboda yanayin tsadar man fetur da dizel da ake ciki a Najeriya, wanda ya tilasta wa kamfanoni da kasuwanci da dama suka durƙushe.

    Sannan lokacin da aka ɗauka ba a magance matsalar ba, ya nuna cewa akwai matsala a ɓangaren makamashin Najeriya," in ji shi, inda ya ƙara da cewa akwai buƙatar a ɗauki mataki domin guje wa sake aukuwar lamarin, ta hanyar nemo wasu hanyoyin makamashin.

    "Ina ba jihohin da ƴan kasuwa shawarar su zuba kuɗi a wasu hanyoyin samar da makamashin domin rage ta'allaƙa da hanyar makamashi guda ɗaya," in ji Kwankwaso.

  3. Ademola Lukman, ɗan Afirka ɗaya da ke takarar Ballon d'Or a bana

    An zaɓi Ademola Lookman cikin waɗanda za su yi takarar lashe Ballon d'Or ta bana ta karo 68.

    Ɗn wasan ɗan Najeriya shi ne ɗan Afirka ɗaya tilo da ke cikin ƴan takarar lambar karrama gwarazan ƴan wasan ƙwallon ƙafa na duniya.

  4. NLC ta caccaki IMF bisa nesanta kanta da cire tallafin man fetur

    Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya ta caccaki Asusun Lamuni bisa maganar cewa ba ita ba ce ta shawarci gwamnatin Najeriya ta cire tallafin man fetur.

    A wata sanarwa da NLC ta fitar a ranar Lahadi, wanda shugabanta Joe Ajaero ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta soki IMF bisa shawarwarin da take bayarwa a matsayin hanyoyin farfaɗio da tattalin arziki, waɗanda a cewarta su ne suka jawo wahala da tsayar komai cak a Najeriya da sauran ƙasashen da suke bin irin shawarwarin kamar yadda Channels ta ruwaito.

    Tun da farko, a wani taron manema labarai na IMF da bankin duniya da aka yi a Washington DC, darakta yankin Afirka na IMF, Abebe Selassie, ya ce cire tallafin man fetur mataki ne da gwwamnatin Najeriya ta ɗauka a cikin gida.

    "Wannan maganar ta IMF cewa a cikin gida ne aka ɗauki matakin cire tallafin mai, amma sai ba ta bayyana irin rawar da suka takawa wajen jula akalar dokokin ƙananan ƙasashe ba. Duk da ƙoƙarin da IMF ke yi nesanta kanta da cire tallafin, mu mun san ita ce kan gaba wajen kira da a cire tallafin man fetur domin inganta tattalin arzikin irin waɗannan ƙasashen.

    "IMF na so ta nesanta kanta ne saboda matsalolin da suka biyo baya, amma ai ƴan Najeriya ba wawaye ba ne. Mun riga mun san yadda matakan da shawawarinsu suka jefa Najeriya da ma wasu Afirka cikin damuwa," in ji ƙungiyar.

  5. EFCC za ta sa ido kan kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

    Hukumar EFCC ta ce za ta ƙarfafa bibiya tare da bin diddigin yadda ƙananan hukumomi suke kashe kuɗaɗensu a daidai lokacin da ake tunanin cin gashin kansu zai fara aiki daga watan Nuwamba, inda ake tunanin za a fara tura musu kuɗadensu kai-tsaye.

    Tura kuɗaɗen kai-tsaye na cikin yunƙurin tabbatar da cin gashin kan ƙananan hukumomin guda 774 a Najeriya, lamarin da shugaban ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi na Najeriya, Hakeem Ambaliya ya bayyana wa jaridar Punch cewa suna farin ciki.

    A ranar 11 ga watan Yulin bana ne dai Kotun Ƙolin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Garba Lawal, ta yanke hukuncin cewa ba daidai ba ne gwamnoni su riƙa karɓa tare da kula da kuɗaɗen ƙananan hukumomi, inda ta buƙaci akanta-janar na ƙasar ya tabbatar ana tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu kai-tsaye.

  6. Mutum bakwai sun rasu bayan rushewar gini a Abuja

    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu sakamakon ruhsewar wani gini a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

    Muƙaddashin darakta-janar na hukumar bada agajin gaggawa ta Abuja FEMA, Abdulrahman Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara wajen ginin da ya rushe a kan titin hanyar tafiya filin jirgin sama.

    Ya ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar a sanadiyar wasu da suka shiga ginin, wanda hukumar kula da ingancin gine-gine ta Abuja take rusawa domin cire ƙarafa, kamar yadda Channels ta ruwaito.

    Ya ce bayan waɗanda suka rasu, akwai wasu mutum da suke jinya a asibiti, sannan ya gargaɗi mutane su guji jefa rayukansu cikin hatsari ta hanyar shiga cikin gine-ginen da aka rusa.

  7. 'An kashe mutum 124 a mako ɗaya a Sudan'

    Wata babbar jami'ar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rahotannin kashe-kashe, ciki har da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula a jihar Gezira da ake zargin dakarun RSF da yi akwai ɗaga hankali.

    Jawabin na Clementine Nkweta-Salami ya zo ne bayan wata ƙungiyar fafutika a ƙasar Sudan ta ce aƙalla mutum 124 ne dakarun RSF suka kashe a cikin mako ɗaya.

    Sai dai ita RSF ta ce ba ka tai hare-hare kan fararen hula, inda ta nanata cewa tana kai hare-haren ne kan sojoji da masu ƴanbindiga.

    Yaƙin na Sudan wanda ya kwashe sama da wata 18 zuwa yanzu, ya ci dubban mutane, kuma ya raba sama da mutum miliyan 11 da muhallansu.

    Yanzu jihar Gezira ce ta zama filin daga daga makon jiya bayan wani kwamandan RSF, Abu Aqla Kayka ya koma ɓangaren sojoji.

  8. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.