Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 28/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjbir, Annur Muhammad, Isiyaku Muhammed, Umar Mikail da Ahmad Bawage

  1. Dubban mutane sun fito zanga-zanga don adawa da sakamakon zaɓen Georgia

    Dubban masu zanga-zanga ne suka hallara a wajen majalisar dokokin Georgia da ke Tbilise domin nuna adawa da abin da suka kira kwacen nasara da aka yi musu a zaɓen ƙasar da aka yi ranar Asabar.

    Masu zanga-zangar sun riƙa wake-wake da taken ƙasar da kuma ɗaga tutar ƙasar da ta Tarayyar Turai da ta Ukraine a yayin da shugabar ƙasar Salome Zourabichvili ke gabatar da jawabi a gare su.

    Ta shaida musu cewa kada su ba ri gwamnati ta kwace musu kuri'unsu da kuma makomarsu.

    Tuni ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bi sahun ƙasashen ƙungiyar Tarayyar Turai wajen yin kira kan a gudanar da bincike a game da rahotannin tafka maguɗi a zaɓen ƙasar da ya gabata.

  2. Labarai da dumi-dumi, Emiliano Martinez ya lashe kyautar Yashin - Ta gwarzon mai tsaron raga

    Emiliano Martinez ya lashe kyautar Yashin - ta gwarzon mai tsaron raga na 2024.

    Wannan ce shekara ta biyu a jere da yake lashe wannan kyauta - yana buga kwallo a Aston Villa kuma ɗan asalin ƙasar Argentina.

  3. Muna kira ga gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-ɓaci kan lantarki - ACF

    Kungiyar tuntubar juna ta dattawan arewacin Najeriya, ACF ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren wutar lantarki a daidai lokacin da yankin arewacin ƙasar ke ci gaba da kasancewa cikin duhu sakamakon rashin wuta.

    Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na ƙasa na ƙungiyar, Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ta yi zargin cewa dagan-gan gwamnati ta banzatar da harkar lantarki a yankin domin ƙara jefa harkokin kasuwanci cikin matsi.

    ACF ta bayyana mamakin cewa me ya sa arewa wadda ke samar da wutar lantarki mai yawa a ƙasar, amma kuma a ke kasawa a ba ta kaɗan.

    "Cikin mako ɗaya da ya gabata, sassan jihohin arewacin Najeriya da dama na fuskantar matsalar rashin wutar lantarki, abin da ya janyo harkokin kasuwanci da na yau da kullum suka kusa durkushewa, ga kuma ƙaruwar ɓacin-rai tsakanin al'umma," in ji ƙungiyar.

    ACF ta ce abin yana tayar da hankali matuka duba da irin sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki a Najeriya (TCN) ya fitar cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar saboda matsalolin tsaro da ake fama da su.

    Ta ce bai kamata a ce jihar Legas kaɗai tana da ƙananan tashoshin samar da lantarki har guda takwas ba yayin da ɗaukacin jihohin arewa, waɗanda ke da sama da rabin al'ummar Najeriya ke da tashoshi guda uku kaɗai a Jos da Kaduna da kuma Kano.

    Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa lamarin babbar barazana ce ga tsaron ƙasar.

    Don haka ta yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da abin ya shafa da su gaggauta ayyana dokar ta-ɓaci kan matslar ta rashin lantarki, kafin matsalar ra rikiɗe zuwa tashin hankali.

  4. Fiye da kashi ɗaya bisa uku na bishiyoyi na barazanar karewa a doron ƙasa - Masana

    Dubban masana kimiyya sun yi gargaɗin cewa fiye da kashi ɗaya bisa uku na wasu bishiyoyi na barazanar karewa a doron ƙasa.

    An gabatar da wannan rahoto ne a wani taron Majalsar Ɗinkin Duniya da aka yi kan sauyin yanayi a Colombia.

    Bishiyoyi na da matukar amfani a rayuwar ɗan'adam, suna kuma taimakawa wajen tsaftace iskar da ake shaka da kuma zuke gurɓatacciyar iska.

    Kazalika bishiyoyi na zama gida ga dubban tsuntsaye da ma dabbobin da ke shayarwa.

    Haka kuma miliyoyin mutane sun dogara a kan bishiyoyi wajen gudanar da rayuwar yau da kullum.

    Wannan barazana ta gushewar wasu nau'in bishiyoyi yana afkuwa a kowace ƙasa, in ji masanan.

  5. Labarai da dumi-dumi, Lamine Yamal ya lashe kyautar matashin ɗan wasa na 2024

    Lamine Yamal ya lashe kyautar matashin ɗan wasa na 2024.

    Ya taka rawar gani a Gasar Euro 2024 wadda ƙasarsa ta Sifaniya ta lashe, ciki har da shan kwallo mai kayatarwa a wasan kusa da karshe.

    Dama dai an yi hasashen cewa Lamine ne zai lashe wannan kyautar saboda irin haskakawa da ya yi a ƙungiyarsa ta Barcelona.

    Ya kasance ɗan wasa mafi ƙankantan shekaru da ya lashe wannan kyauta - yana da shekara 17.

  6. Isra'ila ta kai hare-hare birnin Tyre na Lebanon

    Kafar yaɗa labaran Lebanon, ta ce Isra'ila ta kaddamar da jerin hare-hare ta sama a birnin Tyre da ke kudancin kasar bayan sabon umarnin kwashe mutane daga wurare da dama da aka bayar.

    Rahotanni sun ce hare-haren sun faɗa kan gwamman gidajen jama'a a yankin.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan wuraren da 'yan Hezbollah suke a yankin.

    Tun da farko rahotanni sun ce hare-haren da Isra'ilar ta kai garin na Tyre ya yi sanadin rasa ran mutum bakwai.

  7. Na damu da batun rashin lantarki a arewa - Tinubu

    Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwarsa kan rashin wutar lantarki da arewacin Najeriya ke ci gaba da fuskanta.

    Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkar yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce abin damuwa ne matuka ganin yadda ƴan yankin ke ci gaba da kasancewa cikin duhu kuma hakan na ƙara kassara ɓangaren tattalin arziki.

    Tinubu ya ce yanzu yana jagorantar ƙoƙari da ake yi wajen ganin an gyara matsalar ta rashin lantarki.

    Ya buƙaci ministan lantarki da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kammala aikin gyara turakun wuta da aka lalata da nufin mayar da wuta ga jihohin arewa.

    "Ina cikin damuwa ainun kan rahotannin lalata wayoyin lantarki da sauran abubuwa da suka janyo rahin wuta," in ji Tinubu.

    Tinubu ya yi kira ga kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya da su ƙoƙarta wajen ganin lantarki ta koma domin rage wa al'uma raɗadin da suke ciki.

    Ya ce gwamnati ba za ta lamunci ci gaba da yin zagon ƙasa da kuma lalata turakun wutar lantarki ba.

  8. 'Aika sojojin Koriya ta Arewa zuwa Rasha alamace cewa Putin na tsaka mai wuya'

    Shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO, ya ce tura sojoji da Koriya ta Arewa ta yi yankin Kursk na Rasha don su yaƙi takwarorinsu na Ukraine, alamace da ke nuna cewa shugaba Putin na cikin halin ka-ka-ni-kayi.

    Har yanzu ba a tantance adadin sojojin da Koriya ta Arewa ta tura zuwa Rasha ba, ko da yake an kiyasta cewa za su iya kai wa tsakanin 2,000 zuwa 12,000.

    Mark Rutte, ya ce hakan kuma ya nuna cewa akwai hannun Pyongyang a cikin yakin dumu-dumu wanda kuma zai iya ƙara rura wutar rikicin da ake yi.

    Ya ce alaƙar ta kut-da-kut da ke tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa barazana ce ga harkar tsaron nahiyar Turai da Asiya.

    Shugaban na NATO, ya yi wannan jawabin ne bayan bayanan da suka samu daga hukumar leƙen asirin Koriya ta Kudu.

  9. An ceci wasu ƴan mata ƴan Najeriya da aka yi safarasu zuwa Ghana

    An ceto wasu ƴan mata ƴan Najeriya da aka tafi da su ƙasar Ghana.

    Shugabar hukumar ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana hakan a shafinta na X.

    Abike ta rubuta cewa, "an ceto wasu ƴan matan a Ghana. Godiya da uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu bisa ƙoƙarin da ta yi na tabbatar da dawo da yaran gida, da shugaban ƴan ƙabilar Ibo mazauna Ghana Cif Callistus da ofishin jakadancin Najeriya a Ghana da ƴansanda ƙasa da ƙasa a Ghana da sauran waɗanda suka taimaka."

  10. Fiye da mutum 46,000 ne suka rasa muhallansu a Sudan sakamakon faɗa - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fiye da mutum 46,000 ne suka rasa muhallansu a Sudan sakamakon ƙaruwar faɗan da ake yi a jihar Al Jazirah.

    Ofishin da ke kula da ayyukan jin-kai a majalisar ya ce mutanen da ke zaune a ƙauyuka aƙalla 30 sun bar gidajensu inda suka koma jihohin da ke makwabtaka da su don kaucewa hare-haren da dakarun ƙungiyar RSF ke kai wa.

    Ƙungiyoyin agaji sun yi gargaɗin cewa waɗanda suka rage na cikin haɗarin gaske domin za su iya fuskantar cin zarafi ko kuma su rasa ransu.

  11. Gwamnatin tarayya na duba wasu hanyoyin samar da lantarki ga arewacin Najeriya

    Ministan wutar lantarki a Najeriya Adebayo Adelabu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakai na laluɓo wasu hanyoyin samar da lantarki ga jihohi da ke arewacin Najeriya.

    Adelabu ya ce gwamnatin za ta yi haka ne domin rage wa ƴan yankin raɗaɗin rashin wutar da suke ciki sakamakon lalata layukan bayar da hasken wuta a faɗin yankin.

    Ministan na magana ne bayan wata ganawa da ya yi da shugaba Bola Tinubu a yau Litinin, inda ya ce da farko ana sa ran amfani da wata karamar tashar bayar da lantarki ta Ikot Ekpene wadda ta fito daga Calabar domin kai lantarki yankin arewa, sai dai layin ya lalace.

    "Muna ci gaba da ƙoƙarin ganin mun gyara layin. Kuma idan kuka tuna a taron majalisar zartaswa da ta gabata, ma'aikatar wutar lantarki ta buƙaci a gyara tare da inganta layin bayar da wuta ta Shiroro, wanda shi ke samar da wuta a faɗin arewa," in ji ministan.

    Adelabu ya ƙara da cewa matsalar ta rashin wuta ta shafi jihohi 17 a faɗin arewacin Najeriya.

    "Mun tattauna abin da ya janyo matsalar, wanda hakan ya faru ne sakamakon lalata layukan bayar da wuta na tashar samar da wuta ta Shiroro," in ji shi.

  12. An kashe sojojin Chadi 40 a kusa da tsakaninta da Najeriya

    Fadar shugaban ƙasar Chadi ta ce aƙalla sojoji 40 ne aka kashe musu a wani hari da aka kai a sansanin sojojin ƙasar da ke Kaya, a yankin da ke kusa da tsakanin ƙasar da Najeriya.

    Wasu waɗanda ba a sani ba ne suka kai harin a ranar Lahadi, kamar yadda sanarwar ta faɗa ba tare da bayyana waɗanda ake zargi da harin ba.

    Sai dai a yankin an sha fama da hare-haren Boko Haram.

    Shugaban ƙasar, Mahamat Deby ya ziyarci yankin domin gane wa idonsa, "da kuma jinjina wa sojojin da suka rasu, tare da ƙarfafa gwiwar waɗanda suka raunata."

    Sannan ya ƙaddamar da shirin aikin soji na musamman na (HASKANITE) domin fatattakar maharan.

  13. Bobrisky zai fuskanci wasu sababbin tuhume-tuhume

    Fitaccen wanda ya ce ya sauya halittarsa zuwa mace, Idris Okunaye wanda aka fi sani da Bobrisky yana fuskantar wasu tuhume-tuhume.

    Bobrisky, wanda fitacce ne a kafofin sadarwa ya daɗe yana jawo ce-ce-ku-ce, wanda ake tunanin yanzu zai fuskanci wata sabuwar tuhuma kan zargin da ake masa na zaman gidan yari na tsawon wata shida bisa zargin zargin da ya yi jami’an hukumar yaƙi da da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa EFCC da jami’an hukumar gidan yari cin hanci don a janye tuhumar da ake masa kan liƙi da kuɗin Najeriya, wato naira a wani biki.

  14. Gwamnonin Arewa suna taro a Kaduna domin tattauna matsalolin yankin

    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ƙarƙashin gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya tana zama a jihar Kaduna domin tattauna matsalolin da suka dabaibaye yankin.

    Taron, wanda da ake gudanarwa na kwana biyu ya samu halartar sarakunan yankin, ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad III, da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar C.G Musa da sauran su.

    A jawabin, gwamnan na Gombe, ya ce, "zan fara ne da miƙa jajenmu zuwa ga waɗanda ambaliyar Maiduguri ta shafa, da sauran jihohin arewa, da kuma waɗanda fashewar tanka a Jigawa ta shafa, da kuma waɗanda rashin tsaro ya shafa ta hanyoyi daban-daban.

    "Manyan matsalolin da muke fuskanta a yanzu su ne rashin tsaro da garkuwa da mutane da rikicin manoma da makiyaya da ta'ammuli da miyagun ƙwayoyi da matsalar almajiri da talauci da rashin aikin yi da yawaitar yara waɗanda ba sa zuwa makaranta, sai dai duk da haka, haɗin kanmu ne babban makaminmu na fuskantar waɗannan matsalolin," in ji shi, inda ya ƙara da cewa ana samun nasara a yaƙi da rashin tsaro da ake yi a yankin.

    "Sai dai ya kamata a ƙara ƙaimi ne a kan wannan nasarar da ake samu domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

    "Zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a watan Agusta ta zama wata manuniya ga dukkan jagororin arewa. Lallai akwai buƙatarmu ƙara dagewa wajen biyan buƙatun matasan domin hana su shiga harkokin assha. Dole mu fita da hanyoyin rage talauci da samar da aikin yi da sauran abubuwa."

    Ya ƙara da cewa, "yanzu haka da muke zaune, jihohinmu na arewa babu wutar lantarki saboda wasu ɓata-gari sun lalata tare da sace wasu turakun lantarkin, wanda hakan ke ƙara bayyana halin da matasan yankin suke ciki. Lallai ana rayuwa cikin matsin tattalin arziki musamman a yankin Arewa. Don haka dole mu yi wani abu cikin gaggawa."

    Ya ce arewacin Najeriya na da ƙasar noma, wanda a cewarsa idan aka haɓaka, zai rage talauci da haɓaka tattalin arzikin yankin.

    "Idan muna so mu ci nasara, dole mu tallafa wa manoma sannan mu samar da dabarun noma na zamani, sannan mu tabbatar da tsaro a yankin," in ji.

  15. NDLEA ta kama waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Legas

    Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA a Legas sun kama wasu da ake zargi da tarin ganyen wiwi da tramadol da sauran miyagun ƙwayoyi na biliyoyin naira.

    Jami’an hukumar sun kai samame a wurrare daban-daban ciki har da tashoshin ruwa da jiragen sama da wani wurin ibada.

    Wannan ba shi ba ne karon farko da NDLEA ɗin take kamawa tare da gabatar da waɗanda aka kama bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

  16. Masar ta buƙaci a tsagaita wuta a Gaza domin musayar fursunonin yaƙi

    Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi ya bayar da shawarar dakatar da buɗe wuta tsawon kwana biyu a Gaza domin musayar ƴan Isra'ila huɗu da aka yi garkuwa da su, da wasu fursunonin Falasɗinawa.

    Wannan na zuwa ne yayin da ake sa ran komawa tattaunawar tsagaita wuta kan yaƙin Gaza a yau Litinin, ƙarƙashin jagorancin Amurka da Qatar.

    Tun bayan harin Hamas na 7 ga Oktoban barane - wanda daga lokacin ne Isra'ila ke luguden wuta a Falasɗinu - ƙungiyar take riƙe wasu ƴan Isra'ila da suka yi garkuwa da su.

    Bayan kashe shugabannin Hamas da dama, firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk da nasarar da suka samu a kan Hamas, ba za su daina yaƙi ba, sar waɗanda Hamas ɗin ta yi garkuwa da su, sun kuɓuta sun koma gida.

  17. Dangote ya zuba jarin N460bn a harkar motoci masu amfani da gas

    Kamfanin siminti na Danoge wato Dangote Cement plc, ya zuba jarin naira biliyan 460 a ɓangaren samar da motoci masu amfani da iskar gas a Najeriya.

    Kamfanin ya ce baya ga shiga harkokin kasuwancin ɓangaren, yana kuma so ne ya taimaka wajen rage illolin sauyin yanayi.

    Manajan darakta na kamfanin simintin, Arvind Pathak ne ya bayyana hakan, inda ya ce kamfanin zai koma amfani da motocin iskar gas 100 bisa 100 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    A watan Oktoba ne kamfanin ya karɓi manyan motoci guda 1,500 masu amfani da gas, sannan kuma yake dakon wasu guda 1,600, inda a cewar kamfanin, zuwa ƙarshen shekara, motocinsu masu amfani da iskar gas za su kama guda 3,100.

    Pathak ya ce, "A cikin shekarar 2026 ce muke so motocin Dangote kacokam su koma masu amfani da iskar gas. Domin tabbatar da hakan, mun zuba jari domin faɗaɗa tashoshin shan iskar gas domin tabbatar da cewa tashoshin shan gas ɗin sun yawaita yadda ya kamata," kamar yadda ya bayyana.

  18. Manchester United ta kori Erik ten Hag

    Ƙungiyar Manchester United ta Ingila ta kori kocinta, Erik ten Hag daga aiki.

    A shekarar 2022 ce ƙungiyar ta naɗa kocin wanda ɗan ƙasar Netherlands ce, inda ya karɓi ragamar aikin daga kocin da ya yi riƙon ƙwarya Ralf Rangnick.

    Ten Hag ne kocin ƙungiyar na biyar tun bayan ritayar Sir Alex Ferguson a 2013.

    Sai dai tun bayan da ya fara aiki ne sakamakon wasannin ƙungiyar ke kwan-gaba-kwan-baya.

    A sanarwar da Manchester United ta fitar, ta ce tsohon ɗan wasan gaban ƙungiyar Ruud van Nistelrooy ne zai yi riƙon ƙwarya.

    Erik ten Hag ya lashe kofuna biyu a shekara biyu a ƙungiyar, daga ciki akwai doke Manchester City da Man U ta yi da ci biyu da ɗaya a wasan ƙarshe na kofin FA, wanda shi ne kofin farko da ƙungiyar ta lashe bayan shekara shida.

  19. Zan kori baƙi da ba a taɓa irin sa ba a Amurka - Trump