Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/10/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/10/2024

Taƙaitattu

  • An fara raba kaya a zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kano
  • Masu zaɓe sun fara fita rumfunan zaɓe
  • Abubuwa bakwai kan zaɓen ƙananan hukukomin jihar Kano
  • An fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano
  • Jami'an Karota ne ke bayar da tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Kano
  • Zaɓen Kano: Kwankwaso ya kaɗa ƙuri'arsa
  • An fara ƙirga ƙuri'a a wasu mazaɓun Kano

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Asuba ta gari.

  2. Labarai da dumi-dumi, NNPP ta lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomi 44 a Kano

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Kano KANSIEC ayyana ƴan takarar jam'iyyar NNPP a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomi 44 da na kansiloli 484 da aka gudanar a jihar yau Asabar.

    Shugaban hukumar zaɓe a jihar, Farfesa Sani Lawan Malunfashine ya bayyana haka bayan kammala tattara sakamakon zaɓen.

    Jam'iyyu shida ne dai suka shiga zaɓen da aka yi ta kai ruwa rana saboda umarnin kotuna daban-daban da ke cewa kada a yi zaɓen da kuma wadda ta ce a yi.

  3. Majinyata na tsananin buƙatar kulawa a asibitocin Gaza - WHO

    Farmakin sojoji "a ciki da wajen" cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza da kuma "karancin" magunguna na janyo cikas wajen ba wa marasa lafiya kulawa, in ji shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

    Cikin wata sanarwa, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi nuni da abubuwan da suka faru a asibitin Kamal Adwan da ke arewacin zirin Gaza.

    Jami’an kiwon lafiya na yankin "sun sanar da mu cewa an kawo karshen ƙawanyar da aka yi wa asibitin Kamal Adwan, amma da sauran rina a kaba,” kamar yadda ya rubuta.

    "An tsare ma'aikata maza 44, inda aka bar ma'aikata mata ne kaɗai da daraktan asibitin da kuma likita namiji ɗaya domin kula da majinyata kusan 200 da ke cikin tsananin buƙatar kulawa," in ji Dr Tedros.

    A baya Dr Tedros ya ce hukumar ta WHO ta kasa ji daga asibitin sakamakon harin da Isra'ila ta kai yankin Jabalia.

    Ya ƙara da cewa abin takaici ne rahotannin lalata wurare da kuma kayan aiki a asibitin.

  4. 'Najeriya na asarar dala biliyan 26 duk shekara saboda ƙarancin lantarki'

    Najeriya na asarar dala biliyan 26 a duk shekara sakamakon ƙarancin wutar lantarki.

    Wannan na kunshe ne cikin wani sabon rahoton kasuwanci na Afirka da aka fitar.

    Sai dai ya ce asarar ba ta shafi kuɗaɗen da ake kashewa kan na'urorin samar da wutar lantarki ba.

    Rahoton ya ce 'yan kasuwa suna kashe kusan dala biliyan 22 a duk shekara kan fetur don magance tasirin ƙarancin wutar lantarki. Wannan yana ƙara taɓarɓara al'amura.

    Ya bayyana samar da wutar lantarki a matsayin babban kalubale ga harkokin kasuwanci a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.

    Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun lalacewar babban layin wuta na ƙasa a 'yan kwanakin nan.

    A cikin wannan watan kaɗai, an samu ɗaukewar wutar lantarki a sassa da dama na Najeriya bayan lalacewar babban layin, abin da ya hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasar ta danganta da lalacewar transifoma.

  5. 'Dakarun RSF sun kashe aƙalla mutum 124 a jihar El-Gezira'

    Wata ƙungiyar rajin tabbatar da dimokraɗiyya a Sudan ta ce dakarun kungiyar RSF sun kashe mutum aƙalla 124 a jihar El-Gezira.

    Ƙungiyar Wad Madani, ta ce bayan waɗanda mayakan RSF ɗin suka kashe akwai kuma wasu sama da 100 da suka jikkata lokacin da suka kai hari ƙauyen Al-Sireha da ke arewacin jihar, a jiya Juma'a.

    Wannan dai ɗaya ne daga cikin munanan hare-hare a rikicin Sudan na wata 18 - da ke nuna ƙaruwar cin zarafin farar hula.

    Shugaban rundunar sojin Sudan Janar Abdel Fattah Al-Burhan, ya zargi dakarun na RSF da kisan kiyashi da kuma kawar da wata al'umma a kan farar hula.

    Sai dai RSF ta musanta dukkanin zargin, inda ta ce ta yi arangama da mayaƙan sa-kai ne da ƙungiyoyin kabilu da ke ɗauke da maƙamai waɗanda ke marawa sojojin ƙasar ta Sudan baya.

  6. Na damu matuka kan yaɗuwar rikici a Gabas Ta Tsakiya - Guterres

    Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ya ce ya damu matuka kan ci gaba da yaɗuwar rikici a Gabas Ta Tsakiya bayan hare-haren da Isra'ila ta kaddamar kan Iran, a cewar mai magana da yawunsa.

    "Guterres na ƙara nanata buƙatarsa ga dukkan ɓangarori da kada su ɗauki matakin soji, ciki har da a Lebanon da Gaza, a kuma yi ƙoƙari wajen daƙile afkuwar yaƙi a yankin baki-ɗaya da kuma komawa hanyar diflomasiyya," in ji mai magana da yawun Guterres a cikin wata sanarwa.

  7. Kwastam ta kama fatar jaki 180 a jihar Kebbi

    Jami'an hukumar kwastam a jihar Kebbi sun ce sun kama fatar jaki 180 da ake yunƙurin yin fasa-ƙwaurinta.

    Kwamandan rundunar a jihar Kebbi, Iheanacho Ojike, shi ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.

    Ya ce sauran kayaki da suka kwace sun haɗa da litar man fetur har guda 16,300 da tufafi da kuma katan-katan guda 74 na wasu magunduna daban-daban wanda kuɗin fitonsu ya kai sama da naira miliyan 300.

    Iheanacho ya ce an yi samu nasarar kama kayan ne bisa irin ƙoƙari da jami'an hukumar suke yi wajen kakkaɓe masu aikata ɓarna.

    Kwamandan hukumar ya ce wasu mutane na amfani da lokacin tsadar man fetur wajen safararsa zuwa waje.

    Ya ƙara da cewa an kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a fasa kwaurin kayakin.

    Ya kuma gargaɗi masu fasa kwauri da su daina domin jami'ansu a shirye suke wajen cafke su.

  8. Ƙasashen Larabawa sun yi Alla-wadai da harin Isra'ila kan Iran

    Ƙasashen Larabawa irinsu Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Qatar da kuma Masar sun mayar da martani kan harin da Isra'ila ta kai wa Iran cikin daren jiya.

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta ce ta yi Alla-wadai da hare-haren Isra'ila kan Iran, inda ta yi kira da "a kai zuciya nesa domin kaucewa yaɗuwar rikici".

    Saudiyya ma ta yi Alla-wadai da harin, inda ta kwatanta shi da matsayin saɓa wa "dokokin ƙasa da ƙasa", kuma ta buƙaci "dukkan ɓangarori su kai zuciya nesa da kuma rage barazanar yaɗuwar tashin hankali".

    Qatar ta yi kakkausar suka kan harin da Isra'ila ta kai, inda ta kwatanta shi da "saɓa wa" dokokin ƙasa da ƙasa, ta kuma buƙaci "dukkan waɗanda abin ya shafa su guji tayar da hankali".

    Masar ta ce ta damu matuka kan yaɗuwar rikici a Gabas Ta Tsakiya, ciki har da hare-haren Isra'ila kan Iran, inda ta yi Alla-wadai da dukkan matakai da ke kawo barazana ga ɗorewar zaman lafiya a yankin.

  9. CAF ta bai wa Najeriya nasara kan Libya a wasan da ba a fafata ba

    Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Afrika CAF ta bai wa Najeriya maki uku da ƙwallo uku kan Libya, a wasan da ƙasashen biyu ba su buga ba, bayan da aka zargi jami'an Libya da karkatar da jirgin 'yan wasan Najeriya zuwa wani filin jirgi a ƙasar.

    Tun da farko an tsara karawa tsakanin ƙasashen biyu domin neman gurbin shigar gasar Afirka ta 2025.

    A hukuncin da ta sanar a shafinta na Intanet, CAF ta bayyana cewa an sami hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya da laifin karya sashe na 31 na dokokin gasar cin kofin nahiyar Afrika da kuma sashe na 82 da 151 na dokokin CAF.

    Haka kuma hukumar ta CAF ta ci tarar hukumar ƙwallon ƙafar Libya dala 50,000.

    Hukuncin na CAF na zuwa ne kwanaki kaɗan, bayan shugaban hukumar Patrice Motsepe, ya ce hukumar ta himmatu wajen ganin tabbatar da daidaito a harkar ƙwallon ƙafa a nahiyar.

    Matakin ya kawo ƙarshen yunƙurin neman gurbin shiga gasar da Libya ke yi, inda ta ƙare da maki ɗaya kacal a wasanni huɗu, yayin da Najeriya wanda ta zo ta biyu a gasar da ta gabata, ke da maki 10, kuma ta kusa tabbatar da gurbinta a gasar da ake gudanarwa bayan shekara biyu-biyu.

  10. Ana tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Kano bayan rufe rumfuna

    Jami'an hukumar zaben jihar Kano na ci gaba da tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar a yau Asabar.

    A wasu rumfunan zaɓen an kammala zaɓen tun da safe, bayan da a wasu wuraren aka samu ƙarancin fitowar masu zaɓe.

    Jam'iyyar APC mai hamayyar jihar dai ba t shiga zaɓen ba, haka ita ma rundunar 'yan sandan jihar ba ta shiga za ben ba saboda umarnin kotun tarayya da ya hanata shiga zaɓen.

    Jami'an hukumar Karota da na Vigilante ne dai suka bayar da tsaro a lokacin zaɓen

  11. Yadda Isra'ila ta harba maƙamai masu linzami a Tehran

    Wannan bidiyo ne da ke nuna yadda Isra'ila ta yi ruwan maƙamai masu linzami kan Tehran, babban birnin Iran, a wani hari da ta kai ƙasar.

    Kamfanin dillancin labarai na Iqna ya ce an kai hari kan wasu sansanonin soji a yamma da kuma kudu maso yammacin birnin Tehran.

    An rawaito wani babban jami'in Iran na cewa za su mayar da zazzafan martani a lokacin da ya dace.

  12. Sojojin Iran sun ce harin Isra'la ya kashe dakarunsu biyu

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ambato rundunar sojin ƙasar ne cewa harin da Isra'ila ta kai ƙasar cikin dare ya kashe dakarunta biyu.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar, IRNA ya wallafa sanarwar sojin da ke cewa: ''Dakarun Jamhuriyar Musulunci da ke aikin tsaro da kare mutanen Iran, sun sadaukar da dakarunsu biyu da ke ƙoƙarin kare ƙasarmu daga gwamnatin Yahudawa da ke aikata miyagun laifuka''.

  13. Biden ya gargaɗi Isra'ila ta kauce wa kai hari cibiyar nukiliya da rijiyoyin man Iran

    Gwamnatin shugaba Biden na Amurka ta ce Isra'la na da damar kare kanta tare da mayar da martani kan harin da Iran ta kai mata a farkon watan da muke ciki.

    To sai dai mista Biden ya faɗa wa Isra'ila cewa ba ya goyon bayan ta kai hari kan tashar makaman nukiliyar Iran, saboda fargabar hakan zai haifar da ƙaruwa da faɗaɗar yaƙin.

    Haka kuma ya ce Amurka ba za ta goyi bayan kai wa rijiyoyin man Iran hare-hare ba.

    "Idan da ni ne Isra'ila zan kai hari ne kan wasu abubuwan, amma ba rijiyoyin manta ba'', kamar yadda ya faɗa ranar 4 ga watan Oktoba.

    Isra'ila ta ce hare-haren da ta kai wa Iran, ta kai su ne kan sansanonin sojinta.

  14. Gwamnan Kano ya kaɗa ƙuri'arsa

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ƙananna hukumomin jihar da ke guda.

    Abba Kabir ya kaɗa ƙuri'ar ne a rumfar zaɓensa ta Chiranci a mazaɓar Diso ta ƙaramar hukumar Gwale.

    Yayin da yake jawabi bayan kaɗa ƙuri'ar, gwamnan ya ce zaɓn na gudana cikin kwanciyar hankali.

    Jam'iyyar APC mai hamayya a jihar dai ba ta shiga zaɓen ba

  15. 'Yansanda sun fito domin ''tabbatar da tsaro a Kano''

    Runduar 'yansandan jihar Kano ta ce jami'anta sun fito domin tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, a shafinsa na Facebook ya ce ''kamar yadda muka fito yau domin tabbatar da tsaro kamar yanda muka saba, muna rokon Allah (SWT) Ya cigaba kare al'ummar Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya daga waɗanda ba sa son zaman lafiya''.

    Tun da farko rundunar 'yansandan jihar ta ce ba za ta bayar da tsaro a lokacin zaɓen ba bisa umarnin kotu, to amma Kiyawa ya ce za su fita aikin da suka saba na bayar da tsaro a faɗin jihar.

    Jami'an Karota da na Vigilantee ne dai ke bayar da tsaro a rumfunan zaben.

  16. An fara ƙirga ƙuri'a a wasu mazaɓun Kano

    Bayanan da BBC ta samu daga Kano na nuna cewa an fara ƙirga ƙuri'u a wasu mazaɓu da ke jihar bayan rufe kaɗa ƙuri'ar.

    Da ma dai bayanai sun nuna cewa ba a samu fitowar masu kaɗa ƙuri'a yadda ya kamata ba a wasu sassan jihar.

    Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da yadda jam'iyyun adawa kamar APC da PDP suka ƙaurace wa zaɓen da kuma abubuwan da suka gabaci zaɓen inda har jami'an tsaron gwamnatin tarayya suka yi barazanar ƙauracewa shiga harkokin zaɓen.

    Wata babbar kotun jiha ce dai a ranar Juma'a ta bayar da umarnin cewa hukumar zaɓen jihar ta gudanar da zaben saɓanin hukuncin wata babbar kotun tarayya da ke Kano da ta rushe hukumar tare da haramta mata gudanar da zaɓen.

  17. Zaɓen Kano: Kwankwaso ya kaɗa ƙuri'arsa

    Jagoran Jamiyyar NNPP Na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya kaɗa ƙuri'a a mazaɓarsa ta Kwankwaso, da ke karamar hukumar Madobi.

    Kwankwaso ya kuma ce zaɓen na tafiya yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba.

    Jam'iyyar APC mai hamayya a jihar dai ba ta shiga zaɓen ba.

  18. Jami'an Karota ne ke bayar da tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Kano

    Jami'an hukumar kiyaye dokokin tuƙa ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ne ke samar da tsaro a rumfunan zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

    Tun da fako dama rundunar 'yansandan jihar ta ce ba za ta shiga zaɓen ba, bisa umarnin kotun tarayya da ta buƙaci kada su shiga cikin wani hukunci da ta yanke cikin makon nan, kodayake babbar kotun jihar ta bayar da wani hukuncin da ya ce jami'an 'yansandan su shiga zaɓen.

    A yanzu dai jami'an KAROTA na 'yan Vigilante ne ke bayar da tsaro alokacin zaɓen.

    Kuma kawo yanzu babu labarin wani tashin hankali ko hayaniya.

  19. An fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano

    Al'ummar jihar Kano sun fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke gudana a yau Asabar.

    Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa duk da cewa an samu fitowar masu zaɓe a wasu rumfunan musamman na cikin birnin Kano, a wasu rumfunan musamman da ke wajen birnin, akwai ƙarancin masu zaɓen a wasu rumfunan.

    Hakan dai watakila ba ya rasa nasaba da rashin shigar manyan jam'iyyun hamayyar jihar, APC da PDP cikin zaɓen.

    Wani dalilin kuma da wasu ke gani na rashin fitar zaɓen shi ne fargaba kasancewar jami'an 'yansanda sun ce ba za su shiga don bayar da tsaro a lokacin zaɓen ba.

  20. Abubuwa bakwai kan zaɓen ƙananan hukukomin jihar Kano

    A yau Asabar ne dai, jihar Kano ke bin sahun sauran jihohin ƙasar 36 wajen gudanar da zaɓen ƙananan hukumominta bayan kwashe kwanaki ana kai ruwa rana.

    To sai dai ba kamar a wasu jihohi da dama zaɓen ƙananan hukumomin na Kano na cike da taƙaddama.

    Ga wasu abubuwa da ya kamata ku sani dangane da zaɓen na ƙananan hukumomin jihar Kano