Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 30/10/2024
Usman Minjibir, Annur Muhammad da Isiyaku Muhammed
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da riƙe muƙamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai koma ƙasar.
Kafin naɗa shi a muƙamin, Oluyede ne kwamandan runduna ta 56 da ke Jaji a jihar Kaduna.
Tun a makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa Janar Lagbaja yana jinya a wani asibiti a ƙasar waje bayan ta musanta rahotonnin da ke cewa ya rasu, tana mai cewa Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim ne ya maye gurbinsa a matakin riƙon ƙwarya.
Daga baya hedikwatar tsaro ta Najeriya ta musanta batun, inda ta ce "babu wani batun muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa" a tsarin aikinta.
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin ministoci bakwai da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aike mata domin tantancewa.
A yau Laraba ne majalisar ta yi zaman tantancewar bayan an fasa yin sa a ranar Talata.
Majalisar ta jingine jadawalin ayyukanta na yau ɗin domin tantance su cikin sauri.
An fara ne da Nentawe Yilwatda, wanda zai maye gurbin Betta Edu a matsayin ministan ma'aikatar agaji da yaƙi da talauci.
Daga baya kuma aka tantance sauran kamar haka:
Dubban mutane ne ke tserewa birnin Baalbek da ke gabashin Lebanon bayan gargaɗin da Isra'ila ta yi wa mazauna yankin da su fice daga gidajensu.
Rundunar sojin Isra'ila ta shaida wa mazauna wajen da kuma wadanda ke zaune a kauyukan da zagayen birnin cewa tana shirin kaddamar da hare-hare a kan Hezbollah.
Rahotanni sun ce hanyar fita daga birnin ta cika makil da ababen hawan da suka kwashi mutane don barin garin.
Baalbek, wanda gari ne da Hezbollah ke da karfi a can sannan kuma gari ne da ke da fitattun wuraren ibada na zamanin mulkin Rumawa, kuma an ayyana shi a matsayin ɗaya cikin wuraren tarihi na duniya da ke karkashin hukumar UNESCO ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Fiye da mutum miliyan ɗaya a Lebanon sun rasa muhallansu sakamakon yaƙin da Isra'ila ke yi da Hezbollah.
Waɗanda suka rasu a sanadiyar ambaliyar ruwa a yankin Valencia na Spain sun ƙaru zuwa 62, bayan da farko an ruwaito cewa mutum 51 ne suka rasu.
An yi mamakon ruwan ne na sa'a takwas a yankin gabashin Sifania, wanda ya jawo ambaliyar ruwan, wadda ta yi sanadiyar rasuwar mutane 62, sannan gommai suka ɓace.
Bayan haka kuma, ambaliyar ta shafi iyalai 155,000, inda suke zaune yanzu haka ba tare da lantarki ba.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ɗage sauraron ƙarar zargin almundahanar da EFCC ke yi wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, zuwa 21 ga watan Janairun 2025.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a zaman kotun na ranar Laraba, lauyan EFCC, Kemi Pinheiro SAN, ya ce yana da shaidu biyu da zai gabatar, sannan ya buƙaci kotun ta ci gaba da karɓar shaidu ba tare da wanda ake zargi ba ya amsa ko ya musanta zargin da ake masa ba.
Pinheiro ya ƙada da cewa, "haƙƙin amsa laifi ko musantawa ba dole ba ne, dama ce da za a iya ƙwacewa," in ya ce wanda suke ƙara ya yi watsi da damarsa.
A nasa ɓangaren wanda ake ƙara, lauyansa, Michael Adoyi ya ce bai amince da wannan ba, inda ya ce buƙatar lauyansa masu ƙara ta ci karo da wani hukuncin kotun da ake dako.
A ƙarshe sai alƙalin kotun, mai shari'a Nwite ya ce ba zai yiwu ba a yanke hukuncin shari'ar a bana, sai ya ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa 21 ga watan Janairun 2025.
Ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa IPMAN, ta ce mambobinta ba sa samun loda fetur a matate man fetur ta Dangote duk da cewa sun biya naira biliyan 40 ga kamfanin NNPCL.
Shugaban IPMAN, Abubakar Garima ne bayyana haka a tashar Channels, inda ya ce sun yi mamaki da suka ji Dangote yana cewa dillalan man fetur ba sa zuwa matatarsa sayen mai.
"Idan zai sayar da mai kai-tsaye, za mu saya saboda dole sai mun biya, za a ba mu man. Yanzu haka akwai kuɗinmu naira biliyan 40 a wajen NNPCL, amma ba ma samun kayan. Kwanan nan wasu mambobinmu da NNPCL ta tura matatar Dangote, inda motocinsu suka kwashe kwana huɗu a can ba tare da sun samu man ba."
A ranar Talata ce dai Alhaji Aliko Dangote ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ya bayyana wa manema labarai bayan ganawar cewa yana litar mai sama da miliyan 500 a ajiye, amma dillalan man ba sa sayen fetur ɗin.
A ƙarshe, shugaban IPMAN, ya yi kira ga Dangote da ya duba farashin man matatarsa, sannan ya kwatanta da farashin man na ƙasashen waje. "Shin farashin ya haura na farashin da ake samu daga ƙasashen waje ko ɗaya ne? sannan wane lokaci fetur ke ɗauka kafin ya isa ga dillalin."
Wasu mazauna yankin Shiroro da ke jihar Neja sun ce ƴanbindiga sun daɗe suna kai hari domin lalata layin wutar lantarki na Shiroro-Kaduna 330kV na ɗaya da na biyu.
Lalacewar layin lantarkin ne dai ya jefa mafi yawancin jihohin arewa cikin rashin wutar lantarki, lamarin da ya tsananta, har ya jefa mutanen jihohin cikin ƙunci.
Mazauna yankin sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa layin wutar ya taso ne daga dam ɗin Shiroro ya ratsa ta yankin Chiri, wanda ya daɗe yana fama da matsalar rashin tsaro a ƙaramar hukumar Munya, sannan ya bi ta Sarkin-Pawa da Kafin-Koro na ƙaramar hukumar Paikoro.
Wani basarake a yankin ya ce inda layin ya ratsa duk yanki da ƴanbindiga suke bi, wanda a cewarsa dole ma'aikatan kamfanin rarraba lantarki su sha wahalar zuwa gyara saboda fargabar ƴanbindigar za su iya kawo musu hari suna tsaka da aikin.
Rahotanni na cewa kamfanin NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur a Najeriya, inda farashin ya koma naira 1,025 a jihar Legas, sannan ya koma naira 1,050 a Abuja.
Wannan ƙarin na zuwa ne kimanin mako uku bayan gidajen man sun ƙara farashin man a Legas daga naira 855 zuwa 998, sannan aka ƙara farashin a sauran jihohin.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga NNPCL ɗin a game da wannan ƙarin farashin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a wani gidan man NNPCL a titin Lagos-Abeokuta, an mayar da farashin man zuwa naira 1,025 daga naira 998, sannan kuma gidan man Mobil ya koma sayar da man a naira 1,070, Bovas naira 1,090.
Yayin da ake ƙasa da mako ɗaya gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Amurka, Kamla Harris ta shaida wa magoya bayanta a Washintong DC cewa suna da zaɓi tsakanin ƴanci da hargitsi.
Da take jawabi a daidai wajen da Donald Trump ya shaidawa magoya bayaNsa cewa su yi zanga-zanga a shekarar 2021, Kamala ta bayyana abokin karawar na ta na jam'iyar Republican da wanda ba daidai yake ba, tana mai cewa ya ƙosa ya yi ramuwa.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen Harris dai ya ce wannan ne taro da mafi girma da ta taɓa yi, wanda mutane sama da dubu saba'in da biyar suka halarta.
Mai shari'a Joyce Abdulmalik na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya umarci babban bankin Najeriya CBN da ya dakata da bai wa jihar Rivers kasonta daga asusun gwamnatin tarayya na wata-wata.
Mai shari'a Abdulmalik ya ce kuɗaɗen kason da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara yake karɓa daga gwamnatin tarayya tun daga watan Janairu zuwa yanzu ya saɓa doka, kuma dole a dakatar, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Alƙalin ya ce gabatar da kasafin kuɗin da gwamna Fubara ya yi a gaban ƴan majalisar jihar guda huɗu kacal ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Wannan ya sa alƙalin ya buƙaci babban bankin Najeriya da akanta-janar na ƙasar da bankin Zenith da bankin Access da su tabbatar Fubara bai ci gaba da amfani da kason jihar na wata-wata ba.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi gargaɗi kan abin da da zai biyo baya idan Isra'ila ta dakatar da ayyukan hukumar kula da ƴangudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya Unrwa, yayin da ake ci gaba da buƙatar neman kai agaji a arewacin Gaza.
Mai magana da yawun ma'aikatar, Matthew Miller ya ce dokar ka iya yin tasiri kan manufofin Amurka.
A nasa ɓangaren, shi ma sakatare-janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya rubutu wasiƙa zuwa ga Firaiministan Isra'ila inda ya tuna masa dokar da ta yi tanadin haƙƙin samarwa mutanen da ke yankin kayan buƙatu.
Mai magana da yawun sakatare-janar ɗin ya ce wasiƙar ta tuna masa ne da dokokin ƙasa da ƙasa. Ya ce sakatare-janar ya sake jaddada cewa hukumar ita ce babbar hanyar da ake kai agajin da ake buƙata ga yankin Falasɗinawa.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur da ake samu a Najeriya kan dillalan man da ya ce ba su saya daga gare shi.
Dangote ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da kwamitin shugaban ƙasa kan sayar da ɗanyen man fetur a Naira ga kamfaninsa.
Sannan a wani ƙarin bayani da ya yi, wanda tashar Channels ta ruwaito, ya ce, "mun ƙiyasta cewa Najeriya na buƙatar lita miliyan 30 zuwa 32 a kullum. Wannan ba matsala ba ce saboda yanzu haka muna da lita miliyan 500 a tankinmu, wanda ke nufin ko ba mu tace wani man ba, muna da man da zai wadatar da Najeriya na sama da kwana 12," in ji Ɗangote.
Ya ƙara da cewa a shirye matatarsu take ta samar da lita miliyan 30 ga ƴan Najeriya.
"Ina so NNPCL da sauran dillalan mai su daina shigo da man fetur, su zo wajenmu su saya. Amma idan suka zo suka saya man a matatarmu, za a daina ƙarancin man da ma dogon layi a gidajen mai."
Shugaban Lardin Valencia na ƙasar Sifaniya ya ce an gano gawawwaki bayan da mamakon ruwan sama ya janyo ambaliyar ruwa a yankin.
Sai dai Carlos Mazón bai bayyana adadin gawarwakin da aka gano ba, ko kuma inda aka gano su ba, inda ya nanata cewa ambaliyar, wadda mamakon ruwan ya jawo ce ta yi sanadiyar mutuwar mutanen.
A jihar Kano, har yanzu tsugune ba ta ƙare ba, duk da kammala zaɓen ƙananan hukumomi tare da rantsar da sabbin shugabannin, saboda rikicin shari’a.
Hukumar zaɓen Kano ta ce jam’iyyar NNPP ce ta lashe duk shugannin ƙananan hukumomi 44 da kansiloli 484, to sai dai har yanzu ba a rantsar da shugaban karamar hukumar Kumbotso ba.
Ɗaya daga cikin ƴan takarar kujerar ne ya garzaya babbar kotun jihar saboda sauya sunansa da wani, abin da ya sa kotu ta yi hukuncin da ake ganin shi ne ya hana rantsar da sabon shugaban.
Ana gobe zaben shugabannin ƙananan hukumomi a Kano wato ranar 25 ga watan nan na Oktoba ne wata babbar kotun jiha ta yi hukunci, bayan Ali Musa Ɗanmaliki na jam’iyyar NNPP ya kai ƙarar jam’iyyar da kuma hukumar zaɓen jihar, gaban babbar kotun jihar saboda sauya sunansa da Abdullahi Ghali Shitu a matsayin wanda zai yi takarar.
Kuma bayan kotu ta saurari kowanne ɓangare ne, sai ta yi hukuncin da ya warware duk wani sauyi da aka yi tare da tabbatar da shi Ali Musa Ɗanmaliki a matsayin ɗan takara.
Kuma a haka aka shiga zaɓen ana jani-in-jaka tsakanin mutanen biyu, sannan bayan an sanar da sakamako aka rantsar da shugabanin ba tare da rantsar da na Kumbotso ba.
Tuni dai bangaren Abdullahi Ghali Shitu wadda shi ne jam’iyyar NNPP tace ta tsayar suka ɗaukaka ƙara game da hukuncin babbar kotun.
Ranar 31 ga wannan watan da muke ciki ne ɓangaren da ake ƙarar za su koma kotun don a saurari roƙonsu na a jingine hukuncin.
Shugabar shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a iya fuskantar mummunan yanayi na jin ƙai a Sudan idan har ɓangarorin da yake yaƙi da juna ba su tsagaita wuta ba.
Sindi Muken ta shaida wa BBC cewa miliyoyin al'umma ka iya mutuwa saboda yunwa.
Sindi ta ce yanzu haka mutane sama da miliyan ashirin da biyar ke fuskantar ƙaracin abinci a Sudan ɗin.
Ta kuma roƙi hukumomi da su bada damar shigi da fice kan iyakokin ƙasar, inda da nuna damuwa kan yiyuwar toshe iyakokin ƙasar a wata mai kamawa.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.
Ku kasance tare da mu.