Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/11/25

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/11/25

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Kotun Najeriya ta ɗaure jagoran ISWAP shekara 20 a gidan yari

    Wata babbar kotu da ke Abuja babban birnin Najeriya ta yanke wa ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar ISWAP da ake zargi da kitsa kai hari a ƙasar hukuncin shekara 20 a gidan yari.

    Kotun ta kama Hussaini Isma'ila da laifukan da ake zarginsa da aikatawa na kai hare hare a sassa daban daban na jihar Kano, da ke arewacin kasar, bayan da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gurfanar da shi a gaban kotun.

    Kotun ta kama Hussaini wanda aka fi sani da maitangaran da kai hari shelkwatar rundunar yan sandan Kano da ke Bompai a shekarar 2012, da wasu ofisoshin yansanda da ke unguwanni Kabuga da unguwa uku da na kasuwar waya da Farm centre, inda mutanen da dama suka mutu, wasu suka jikkata.

    An fara shariar ne tun bayan kama shi a ranar 31 watan Agustan 2017 a garin tsamiya babba da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

    Sai ai shariar ta fuskanci jinkiri saboda ɗaukaka ƙara da kuma sharia cikin sharia da aka yi ta yi kan wasu laifukan da ake zargin ya aikata.

    Hukumar tsaro ta DSS da ta gurfanar da shi ta gabatar da shaidu biyar waɗanda ake ganin sun gamsar da alkalin, ciki har da mutanen da suka shaida kai hare haren.

    Tun da farko dai wanda ake zargin ya musanta tuhume tuhumen da ake yi masa, kafin daga bisan ya amince da su, abinda ya sa lauyansa ya nemi a yi masa sassauci, saboda a cewar sa ya yi nadama don haka ne ma ya amince don gudun ɓata wa kotu lokaci.

    Mai shari'ar Emeka Nwite ya kama Maitangaran da laifi, inda ya yanke masa hukuncin shekaru ashirin, ya kuma umurci shugaban hukumar kula da gidajen yari ta kasar ya ajiye Maitangaran a duk gidan yari da ya so, kuma a sanya shi a wani shiri na gyaran hali da kuma canza masa aƙida.

  2. Manyan sojojin Najeriya biyar da Boko Haram ta hallaka

    A ranar Talata ne rahotonni suka fara ɓulla cewa mayaƙan ƙungiyar Islamic State of West Africa Province (Iswap) ta kashe Birgediya Janar Musa Uba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Kisan nasa ya tayar da muhawara game da yadda ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da Iswap ke kashe manyan jami'an sojin Najeriya, duk da cewa ba shi ne na farko da ya mutu a filin daga ba.

    Bayanai sun nuna cewa Janar Uba ne babban jami'i na biyu mafi girman muƙami da 'yanbindigar suka kashe tun shekarar 2021.

    Karanta cikakken labarin a nan:

  3. Za mu tsoma baki kan rikicin Sudan - Trump

    Shugaba Donald Trump ya ce zai yi ƙokarin taimakawa wajen kawo ƙarshen yaƙin Sudan bayan bukatar da yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman ya mika masa.

    Da yake magana da a wani taron zuba jari tsakanin Amurka da Saudiyya, Mista Trump ya ce bai yi tunanin shiga batun yakin Sudan ba, sai da Yariman ya nemi taimakonsa.

    Gwamnatin mulkin sojan Sudan ta mayar da martani cikin gaggawa, inda ta ce a shirye take ta yi aiki tare da Amurka da Saudiyya domin kawo zaman lafiya a kasar.

  4. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa na kai-tsaye, barkanmu da Hantsin yau Alhamis.

    Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma faɗin duniya.

    Za ku iya bibiyar mu a shafukan mu na sada zumunta kamar Facebook da Instagram da Youtube da Whatsapp da kuma X, domin tafka muhawara a kan labaran da muke wallafawa da kuma kallon bidiyo.