Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/06/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/06/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida

  1. Kalli tarihin jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei

    Sunan Ayatollah Ali Khamenei na ci gaba da amo a ƴan kwanakin nan saboda yaƙin Iran da Isra'ila, ko wane ne shi?

    Jagoran addinin Iran Ali Khamenei na riƙe da madafun iko mai ƙarfin gaske - yana da ikon hawa kujerar na-ƙi a kan duk wani matakin ƙasar, sannan yana da ikon naɗa wanda yake so a wata kujerar mulkin ƙasar.

  2. 'Sai bayan babban taron APC Tinubu zai zaɓi matamakinsa a zaɓen 2027'

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa sai bayan babban taron jami'ar ne Shugaba Tinubu zai zaɓi wanda zai zama mataimakinsa a zaɓen 2027.

    Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.

    A baya-bayan nan, rashin jituwa na neman ɓullowa a APC kan wanda zai yi wa Tinubu mataimaki, bayan da gwamnonin APC suka amince da shugaban ƙasar a matsayin ɗan takarar jam'iyyar a 2027.

    A ƙarshen mako ne dai aka kusa bai wa hamata iska a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar na shiyyar arewa maso gabas, bayan da wasu ƴan jam'iyyar suka zargi wasu jagorin jam'iyyar da rashin ambatar sunan Kashim Shettima a lokacin da suke jawabin amincewa da Tinubu a matsayin ɗan takarar.

    To sai dai tun bayan faruwar lamarin, ba a ji ta bakin fadar shugaban ƙasar ba, lamarin da ya sa wasu ke ganin akwai shirin janye Kashim ɗin daga takarar 2027.

    To amma Bayo Onanuga ya musanta wannan zargi yana mai cewa lokaci ne bai yi ba.

    “A tsarin takarar shugaban ƙasa, ana fara tsayar da ɗan takara, daga baya sai a zaɓi wanda zai zama mataimakinsa. Haka aka yi lokacin Buhari, an fara tsayar da shi, daga baya ya zaɓi mataimakinsa. Ba a yin su duka lokaci guda,” in ji Onanuga.

    A lokacin da yake gwamnan Legas dai, sau kusan uku Tinubu yana sauya mataimaki, abin da ya sa wasu ke ganin zai yi amfani da wancan salo a wannan karon.

    To amma Onanuga ya ce wannan hasashen mutane ne kawai.

    “Wannan hasashe ne kawai. Eh, lokacin yana gwamna akwai wasu matsaloli. A wa’adin farko, shi da mataimakiyarsa Kofo ba su jitu ba, hakan ya sa ta bar aiki. Femi Pedro ne ya maye gurbinta. A wa’adinsa na biyu kuma ya ci gaba da aiki da Pedro, sai dai daga baya Pedro ya sauya sheƙa saboda yana so ya tsaya takarar gwamna, wannan ne dalilin barinsa." in ji shi.

    Ya ƙara da cewa: “Don haka, ba daidai ba ne a ce Tinubu yana da ɗabi’ar sauya mataimakansa.

  3. 'Ba za mu tattauna da Amurka ba har sai Isra’ila ta daina kai mana hari'

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce ƙasarsa ba za ta shiga wata tattaunawa da Amurka ba har sai Isra’ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa, in ji rahoton kafar yaɗa labarai ta gwamnatin ƙasar, IRNA.

    “Akwai saƙonni da dama daga Amurka suna neman mu shiga tattaunawa, amma mun bayyana a fili cewa babu wani gurbi na tattaunawa har sai wannan hare-haren ya tsaya,” in ji Araghchi.

    “Ba mu da wani shiri na tattaunawa da Amurka kasancewar tana da hannu a wannan laifi,” in ji shi.

    Ana sa ran Araghchi zai gana da wasu ministocin harkokin waje na Turai a Geneva yau — zama na farko da Iran ke yi da ƙasashen yamma kai tsaye tun bayan da Isra’ila ta fara sabon rikici makon da ya gabata.

  4. Kalli yadda motoci ke ƙonewa bayan harin da Iran ta kai wa Isra'ila

    Wani bidiyo ya nuna yadda wuta ke ƙona wasu motoci a kusa da ofishin Microsoft da ke Beersheba da ke Isra'ila bayan harin da Iran ta ƙaddamar a kudancin Isra'ila.

    Jami'an kashe gobara da ma'aikatan lafiya sun kai ɗauki domin bayar da agaji.

    Rahotonni sun ce mutum biyar ne suka jikkata sakamakon harin.

    Da alama Iran na harin cibiyar fasahar zamani ta Gav-Yam, wanda jami'an Iran suka bayyana cewa shi suka hara a harin jiya da ya faɗa kan asibitin Soroka da ke kusa da ginin.

  5. Yadda al'ummar Filato suka yunkuro don magance matsalar 'yan bindiga da ta addabe su

    Da alama wasu 'yan Najeriya sun zaburo domin magance wa kansu matsalar ƴan bindiga da ta addabi yankunansu.

    Al'ummar wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato sun yi haɗin gwiwa da sojoji inda suke kai wa ƴan bindiga hari har maɓoyarsu, a maimakon su jira ƴan bindigar su kawo masu hari sannan su kare kansu.

    A irin wannan hari da suke kai wa ne suka samu nasarar halaka ƴan bindiga da dama a baya bayan nan, ko da yake wasu daga cikin ƴan sa kan suma sun samu raunuka.

  6. Ministan harkokin wajen Iran zai gana da takwarorinsa na Turai

  7. Iran da Isra'ila sun ci gaba da musayar wuta a cikin dare