Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/06/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/06/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Asabar idan Allah ya nuna mana.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kai wa Iran hare-hare

    Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan Iran, tana mai ikirarin samun nasara sama da mako guda da soma yaƙin.

    Jakadan Isra'ila a Majalisar Ɗinkin Duniya, Daniel Meron da ke halartar taron Geneva ne ya shaida hakan, a daidai lokacin da ake luluben hanyoyin diflomasiya domin samar da maslaha.

    Ya nemi ministocin ƙasashen wajen Turai da ke ganawa da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, su bukaci Iran ta soke shirinta na nukiliya.

    Aragchi, ya ce hare-haren Isra'ila kan ƙasarsa rashin imani ne tsagwaronsa. Kuma ya zama dole Iran ta kare kanta.

  3. Ba gajiyawa ba ce ta sa muke sasanci da ƴanbindiga – Gwamnatin Sokoto

    Sokoto

    Asalin hoton, Ahmed Aliyu

    Gwamnatin jihar Sokoto ta ce ba gajiyawa ba ce ta sa ta ɗauki matakin tattaunawa da ƴanbindiga waɗanda suka miƙa wuya tare ajiye makamai da kansu domin sasanci, lamarin da gwamnatin ta bayyana da yunƙuri ne na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta dabaibaye jihar.

    Gwamnatin ta bayyana haka ne a wani martani da ta mayar kan jawabin wani mai suna Basharu Altine Guyawa, wanda ya soki matakin gwamnatin na sasanci da ƴanbindiga, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    A wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan jihar Ahmed Aliyu kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman mai ritaya, ya ce ba gajiyawa ba ce ta sa suke tattaunawar.

    "Mun ga wani jawabi da wani mai suna Mr Basharu Altine Giyawa ya yi, inda ya suki matakin gwamnatin jihar Sokoto na amfani da hanyoyin sasanci domin kawo ƙarshen harkokin ƴanbindiga da rashin tsaro a jihar.

    "Duk da cewa muna mutunta ra'ayin kowa, amma yana da kyau mu bayyana da dalilin da ya sa gwamna Ahmed Aliyu ya amince da bin wasu hanyyoyi irn su sasanci da tattaunawa da tsofaffin ƴanbindiga. Ko a baya shi kansa Giyawa ya bayyana shirinsa na shiga tsakani domin samun sasancin."

    Sanarwar ta ƙara da cewa, "ba gajiyawa ba ce ta sa gwamnatin ke sasanci, kuma ba sakaci ba ne wajen neman adalci. Kawai mun ɗauki matakin a ciza, a hura ne domin magance matsalar," in ji hi.

  4. Gaza na dab da faɗawa cikin fari - Unicef

    UNICEF

    Asalin hoton, Getty Images

    Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa Gaza na gab da faɗawa cikin fari, wanda asusun ya ce mutane suka ƙirƙira.

    Wannan gargaɗin na zuwa ne kimanin wata biyu bayan yankewar ruwa a zirin na kimanin wata biyu.

    Kakakin asusun, James Elder ya ce kusan rabin hanyoyin ruwan sha na zirin ba sa aiki, saboda sun lalace a sanadiyar yaƙin da ake a yankin, wanda hakan ya jefa ƙananan yaran yankin cikin ƙishin ruwa mai tsananin gaske.

    Asusun ya fitar da wanna gargaɗin ne bayan wata hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kusan ƙananan yara 5,000 ne suke fama da rashin abinci mai ginaa jiki.

  5. Yadda Iraniyawa suka yi zanga-zangar goyon bayan ƙasarsu bayan sallar Juma'a

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Orano mai haƙo uranium ya ce ba zai amince da ƙwace kamfaninsa na Nijar ba

    Orano

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Kamfanin Orano mai haƙo ma'adinin uranium ta ƙasar Faransa ta ce ba za ta amince da ƙwace kamfanin Somair mallakinsa da ke aiki a Jamhuriyar Nijar.

    Orano ya bayyana haka ne a ranar Juma'a a matsayin martani ga Jamhuriyar Nijar, bayan gwamnatin sojin ƙasar ta sanar da matakin ƙwace kamfanin tare da mayar da shi mallakinta a ranar Alhamis.

    Wannan na zuwa ne bayan watanni ana kai-komo kan matsayin kamfanin tsakanin ƙasar ta Nijar da asalin kamfanin da ke Faransa tun bayan juyin mulki da aka yi a ƙasar a shekarar 2023, inda sojoji suka hamɓarar da gwamnati, suka ɗare karagar mulki.

  7. Ministocin ƙasashen Turai sun gana da ministan harkokin wajen Iran

    Yayin da yaƙin Isra’ila da Iran ya shiga mako na biyu, inda ƙasashen biyu ke ci gaba da kai wa juna hare-hare, ministocin harkokin wajen ƙasashen Turai na wata ganawa da takwaransu na Iran, a birnin Geneva, na Switzerland domin kawo ƙarshen yaƙin.

    Ganawar na zuwa ne bayan da Shugaba Trump na Amurka ya ce nan da makonin biyu zai yanke shawara kan ko ƙasarsa za ta shiga yaƙin kai-tsaye ko kuma a'a.

    Ya ce wa'adin wata dama ce ta zama kan teburin sulhu domin kawo ƙarshen yaƙin.

  8. Iran ta sake kai hare-haren makamai masu linzami a Haifa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta sake harba makami mai linzami arewacin Isra'ila, lamarin da ya jikkata mutane sama da 20.

    Sojojin Isra'ila sun ce makamai masu linzami 20 aka harba musu, wanda galibi suka fada a yankin Haifa da ke gabar teku.

    Akwai wata mata mai shekara 51 da ta mutu saboda bugun zuciya a wuraren da ake bai wa mutane mafaka a Karmiel.

  9. Antonio Guterres ya nemi a yi sulhu tsakanin Isra'ila da Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na tattaunawa kan yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da Iran.

    Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya fada wa taron da ake gudanawar a New York cewa duniya na gab da faɗawa cikin yaƙi.

    Mista Guterres ya roƙi ɓangarorin da ke rikici da juna da masu mara musu baya su rungumi zaman lafiya.

    Ya ce cigaba da ruruwar wannan yaƙi na iya jefa duniya cikin bala'in da zai shafi kowa.

  10. Ƴan hamayya a Najeriya na neman rajistar sabuwar jam'iyyar ADA

    El Rufa'i da Atiku

    Asalin hoton, El Rufa'i/X

    Jagororin jam'iyyun hamayya na Najeriya a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam'iyyar da za su yi amfani da ita domin fafatawa da jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

    Tuni NNCG ta miƙa takardar neman rajistar jam'iyya ga Hukumar INEC a hukumance, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Wasiƙar wadda suka aika zuwa ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa tare a ranar 20 ga Yunin.

    A wasiƙar, sun rubuta cewa, "muna neman INEC ta amince da buƙatarmu ta yi wa ƙungiyarmu ta All Democratic Alliance ta zama jam'iyyar siyasa."

    Taken jam'iyyar dai shi ne 'Adalci ga kowa' sannan masara ce tambarinta.

    Daga cikin na gaba-gaba wajen yunƙurin samar da haɗaka da za ta fuskanci jam'iyyar APC mai mulki akwai tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Ribas Rotimi Amaechi da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da tsohon shugaban majalisar dattawar ƙasar, Sanata David Mark da Umar Arɗo da sauransu.

  11. Rikici kan fili ya yi ajalin mutum 14 a Filato

    Bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a arewa ta tsakiyar Najeriya sun ce aƙalla mutum 15 ne aka kashe a wani sabon hare-haren da suka wakana a tsakanin ɓangarori biyu kan rigimar fili.

    Ƙauyuka biyu na Magu da Tangur ne aka kai wa hare-haren da tsakar dare.

    Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum 200 ne aka kashe a wasu hare-haren daban a jihar Benue da ke maƙwabtaka a jihar ta Filato.

    A ranar Laraba ce shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci jami'an tsaron ƙasar su fatattaki mahara tare da magance matsalar tsaro a yankin.

    Rikicin yankin dai wani rikici da ne da ya samo asali tsakanin manoma da makiyaya tun tsawon lokaci, inda manoma suke zargin dabbobin makiyaya suna musu ɓarna, zargin da makiyayan suka daɗe suna ƙaryatawa.

  12. Gwamnatin Netherland ta mayar wa Najeriya kayayyakin tarihi 199 da aka sace a 1897

    Tarihi

    Asalin hoton, Wereldmuseum

    Gwamnatin ƙasar Netherland ta mayar wa Najeriya wasu kayayyakin tarihi 119 da aka sace lokacin da Birtaniya ta ci daular Benin da yaƙi a 1897.

    Waɗannan na ɗaya daga cikin kayayyaki mafiya yawa da aka mayar wa Najeriya tun bayan mamaye tsohuwar daular.

    Kayayyakin da aka mayar dai sun haɗa wani tsuntsu na tagulla, da kan mutum-mutumi na icce, da kuma mutum-mutumin wani jarumin sarki da aka yi da tagulla da zakara da dai sauransu.

    An dai kawo kayan tarihin na daular Benin ɗin ne daga gidan ajiye kayan tarihin na Wereland da ke ƙasar ta Netherland.

    Kodayake za a yi bikin miƙa kayayyakin a hukumance a gobe Assabar a Legas, an miƙa wasu daga cikin kayayyakin ga Oba na Benin a birnin Benin jiya, a wani mataki na an nuna mayar da kayan zuwa tushensu.

    Da yake karɓar kayayyakin daga tawagar gwamnatin Netherlands, basaraken ya ce mayar da kayan tarihin ga masarautar wata muhimmiyar nasarar ce ta fuskar hulɗar diflomasiyya da ta al’adu tsakanin Netherland da Najeriya.

    Ita kuwa jagorar tawagar kana shugabar gidan tarihin na Wereland, Ms. Marieke Van Bommel, ta jaddada manufar gwamnatin ƙasarta ta mayar dukkanin kayan tarihin da aka sata zuwa inda aka sato su inda ta ce ƙasarta ta kwashe shekara fiye da 100 tana ajiye da waɗannan kayayyakin na Benin guda 119 da suka mayar.

    Za a yi bikin miƙa kayayyakin na gobe ne a babban gidan ajiye kayan tarihi na ƙasa da ke Legas a gaban idon wakilan gwamnatocin ƙasashen biyu da kuma na masarautar Benin ɗin.

  13. 'Isra'ila ta kashe mutum 20 wajen karɓar abincin tallafi a Gaza'

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu aikin ceto a Gaza sun ce sojojin Isra'ila sun kashe mutum 43, ciki har kusan 20 da ake kashe a wurin karɓar kayan tallafin abinci.

    Wakilin BBC ya ce sojojin Isra'ila na cigaba da matsa wa Falasdinawa da ke fitowa karɓar abinci a sansanin da gidauniyar tallafawa al'umma a Gaza ke rabon tallafi, inda suke amfani da jirage marasa matuƙa da tankoki suna buɗe wuta kan mutane.

    A wani yanki na daban a Gazan, ƙungiyar agaji ta Falasdinawa Red Crescent, ta ce aƙalla mutum 11 aka kashe a wani gini da aka kai wa hari a Deir al-Balah.

    Isra'ila ba ta ce komai ba kan waɗannan hare-hare kawo yanzu.

  14. Mahara sun kashe sojojin Nijar 34

    Nijar

    Asalin hoton, ORTN

    Aƙalla sojoji 34 ne wasu mahara da ake zargin masu ikirarin jihadi sun kashe a Jamhuriyar Nijar, sannan suka jikkata wasu mutum 14.

    An kai harin ne a garin Banibangou, wanda ke kan iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso, inda ake tunanin akwai mahara masu ikirarin jihadi da suke da alaƙa da ƙungiyar Al Qaeda.

    Ma'aikatar tsaron Nijar ta yi Allah-wadai da harin, wanda ta bayyana da "na rashin hankali,".

    Ma'aikatar ta ce "an kai harin ne a ranar Alhamis 19 ga watan Yuni. Wanda hari ne na dabbanci da aka kai a garin Banibangou, wanda wasu mahara waɗanda baƙi ne suka kai a babura sama 200," kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin ƙasar sun kashe "gomman maharan," a lokacin da suke musayar wuta, sannan ta tura ƙarin jami'a zuwa yankin.

    A yanzu haka dai Nijar da Burkina Faso da Mali suna ƙarƙashin mulkin soji ne waɗanda suka ƙwace mulki bayan hamɓarar da zaɓaɓɓun shugabannin ƙasar, sannan suka kafa ƙawancen tsaro.

    Sai dai duk da ƙawancen, har yanzu ƙasashen yankin suna fama da rikice-rikice a ƴan watannin da ake ciki.

  15. Ministocin Turai za su gana da Iran

    Ga wasu hotunan ministocin harkokin waje na Birtaniya da Tarayyar Turai da Faransa da Jamus suna tattaunawa a Geneva kafin ganawarsu da takwaransu na Iran.

    Ƙasashen Turai na fatan gabatar da wata shawara ta diflomasiyya ga Iran a yau domin rage zafin yaƙin da ke faruwa tsakaninta da Isra'ila.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  16. Gwamnatin Nijar na son ƙwace kamfanin haƙar Uranium na Orano

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Shugabannin mulkin soja na Nijar sun ce za su ƙwace kamfanin haƙar uranium na cikin gida mai suna Somaïr, wanda yawancin hannun jarinsa mallakin Faransa ne, a wani sabon mataki da ke ƙara tsananta rikicin diflomasiyya da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Somaïr yana ƙarƙashin ikon kamfanin Orano ne mallakin Faransa, wanda shugabannin Nijar ke zargi da aikata wasu “ayyuka marasa kishin ƙasa.”

    Tun bayan karɓar mulki a shekarar 2023, shugabannin sojin sun bayyana cewa suna son ƙarin ikon mallakar albarkatun ma’adinai na ƙasar, tare da nisantar Faransa wadda ita ce tsohuwar mai mulkin mallaka yayin da suke ƙara kusanci da Rasha.

    Nijar ce ta bakwai a duniya wajen samar da uranium, kuma tana da ingantattun ma’adinai mafi daraja a nahiyar Afirka.

    “Wannan ƙwace kamfanin zai ba da damar gudanarwa mai tsafta da dorewa, wanda zai ba 'yan Nijar damar cin gajiyar arzikin ma’adinai yadda ya kamata,” in ji wata sanarwa daga gwamnatin soji.

    Kamfanin Orano bai fitar da wata sanarwa ba tukuna.

    A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, Orano – wanda gwamnatin Faransa ke mallaka – ya shigar da ƙara kan matakin da gwamnatin Nijar ta ɗauka.

  17. Haɗin gwiwar jamia'n tsaro ya kama 'ƴan daba' 398 da makamai a Kaduna

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da kama mutum 398 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin wata babbar samame da aka ƙaddamar domin kawar da masu aikata laifi a fadin jihar.

    Wannan farmaki da aka gudanar cikin kwanaki tara na farko, na ƙarƙashin wani rundunar haɗin gwiwa ta musamman da gwamnatin jihar ta kafa, inda rundunar ‘yan sanda ce jagora

    Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 18 ga Yuni, inda ya ce samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka kai ga ckama waɗanda ake zargi a wurare daban-daban na jihar.

    Cikin wadanda aka kama har da wani sanannen jagoran ‘yan daba mai suna Mathew Adamu wanda aka ƙwace bindiga a tare da shi.

    Haka kuma an kama wani shahararren mai safarar miyagun ƙwayoyi, Adamu Umar, wanda za a miƙa shi ga hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanarwa.

    Rundunar ta kuma yi nasarar ƙwato wasu makamai masu haɗari da miyagun ƙwayoyi da kuma wayoyin salula guda 29 da aka sace a samamen

    Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ya umarci rundunar ta musamman su ci gaba da zage damtse.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Sojojin Isra’ila sun sake kashe Falasɗinawa 23 a kusa da cibiyar bayar da agaji

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An sake samun asarar rayuka a Gaza, inda shaidu da ma’aikatan lafiya suka ce sojojin Isra’ila sun buɗe wuta kan tarin mutane da suka hallara a kusa da cibiyar bayar da agaji, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa da dama.

    Wani jami’i a asibitin Nuseirat ya tabbatar da cewa sun karɓi gawarwaki 23 da kuma mutane fiye da 100 da suka jikkata.

    Sojojin Isra’ila ba su fitar da wani bayani ba tukuna kan harin.

    A wani hari na daban, wani ma’aikaci na ƙungiyar agajin Red Crescent na Falasɗinawa ya ce mutum 11 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani harin jirgin sama da Isra’ila ta kai kan wani gida a yankin al-Ma’sar da ke yammacin Deir al-Balah.

  19. Iran ta kai hari kan cibiyar ƙere-ƙere a Isra'ila

    Wani gini d aya lalace

    Asalin hoton, EPA

    Harin makami mai linzami da Iran ta harba ya faɗa kan wata cibiyar ƙere-ƙere da ke birnin Beersheba a kudancin ƙasar.

    Gine-gine da dama sun lalace, yayin da rahotonni suka ce mutum bakwai sun samu raunuka.

    Cibiyar na kusa da asibitin Soroka da Iran ta kai wa hari a ranar Alhamis.

    A nata ɓangare rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai gomman hare-hare a Iran, ciki har da abin da ta kira cibiyar ƙera makamai masu linzami na Iran din.

    Haka kuma Isra'ilar ta ce ta kai hari shalkwatar cibiyar binciken soji ta Iran, sai dai babu alƙaluman rasa rai ko jikkata.

  20. Ƴan ƙungiyar asiri sun kashe mutum biyu a kwalejin fasaha ta Anambra

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar ƴan sanda a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum biyu tare da sace wasu biyu bayan wani hari da ake zargin ‘yan ƙungiyoyin asiri ne suka kai a Oko, ƙaramar hukumar Orumba ta Arewa.

    Rundunar ta ce an kuma ceto wasu mutum biyu, ciki har da wata mace wadda yanzu haka take karɓar magani a asibiti.

    A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Tochukwu Ikenga ya fitar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:40 na dare a ranar Laraba, 19 ga Yunin 2025, a mahaɗar da ake kira Total Junction da Tipper Junction da ke garin Oko, inda wasu mahara a kan babur ake zargi sun buɗe wuta.

    Harin ya jikkata mutum huɗu.

    Jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin kwamandan yankin Aguata tare da haɗin guiwar sojoji da rundunar ruwan Najeriya da hukumar tsaro ta NSCDC da jami’an bijilante sun gaggauta zuwa wurin kuma sun karɓe iko da yankin.

    "An samu nasarar ceto mutum biyu — ɗaya daga cikinsu mace ce — waɗanda yanzu haka suna karɓar kulawa a asibiti." in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, "Shaidu sun bayyana wa ‘yansanda cewa maharan sun bayyana ba zato ba tsammani, lamarin da ya haddasa firgici ga mazauna yankin da masu wucewa."

    Rundunar ‘yansanda ta jihar ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankali tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙokari don kamo waɗanda suka kai harin.