Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Aisha Babangida da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Babu ƙanshin gaskiya cewa sojojinmu na yin murabus - Rundunar sojin Najeriya

    Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai na baya-bayan nan da ke nuna cewa jami'anta sun yi murabus daga aikinsu ne saboda cin hanci da rashawa, da rashin ɗa’a, da kuma rashin walwala.

    A makon nan ne dai wasu kafofin watsa labaran Najeriya suka yi ta naƙalto wani rahoto da ke nuna yadda sojoji fiye da guda 1000 suka yi murabus bisa zarge-zargen rashin jin daɗin aiki da rashawa da cin hanci "da ya yi wa aikin katutu".

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana waɗannan iƙirari a matsayin karya da kuma yunƙurin ɓata mata suna da gangan.

    A cewar rundunar, rahotannin an yi su ne domin haifar da saɓani da kuma ɓata tarbiyar jami’anta.

    Sanarwar ta kara da cewa: "Batun cewa sojoji na yin murabus daga muƙamansu saboda rashin jin dadin rayuwa, da cin hanci da rashawa ba gaskiya ba ne."

    Rundunar ta fayyace cewa jami’anta suna da ‘yancin yin murabus daga muƙamansu bisa raɗin kansu, bisa ga ka’idojin da aka tsara a cikin ƙa’idojin Hidima na Hafsa da Sojoji.

    Rundunar Sojin ta kuma bayyana ci gaba da jajircewarta na jin dadin ma’aikatanta a ƙarkashin jagorancin babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

    Daga ƙarshe rundunar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su tantance bayanai kafin a buga su don hana yaɗa labaran da ba su da tushe da makama.

  2. Kwankwaso ba shi da wani muhimmanci a siyasar Najeriya - PDP

    Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan kalaman da sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 ya yi wanda ya yi iƙirarin cewa jam’iyyar PDP ba ta da wani tasiri a siyasar Najeriya, inda ya ce jam’iyyar ta mutu.

    A ranar Asabar ne dai Sanata Kwankwaso yayin buɗe ofishin jam'iyyar NNPP na jihar Katsina, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam'iyyar PDP da APC mai mulki da jefa kanta cikin abin da ya kira ''halaka''.

    A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa Debo Ologunagba ya fitar a ranar Lahadi, PDP ta bayyana Kwankwaso a matsayin "mara muhimmanci a siyasar Najeriya" tare da zargin sa da son kai.

    Ologunagba, ya soki kalaman Kwankwaso, inda ya nuna cewa jam’iyyar NNPP a karkashin shugabancin Kwankwaso na ƙoƙarin gina kanta ne a jiha ɗaya kacal, yayin da kuma jam’iyyar PDP har yanzu na da tasiri a faɗin jihohi 13 da ke da gagarumin wakilci a majalisar dokokin ƙasar.

    Sanarwar ta ce “Rabi’u Kwankwaso ba shi da wani tasiri a siyasar Najeriya a yau idan aka yi la’akari da yadda yake fafutukar ganin ya jagoranci wata jam’iyya mai suna NNPP wadda ita ma ke fafutukar ganin ta gina kanta a jiha ɗaya kawai."

    “Abin da za a fi mayar da hankali a nan shi ne yadda Sanata Kwankwaso ya nuna tsananin son kai, wanda hakan ke nuna cewa shi ba shugaba ba ne."

    PDP ta ce abin mamaki ne yadda Kwankwaso, wanda suka bayyana a matsayin dan siyasar da ya gaza, zai ayyana jam’iyyar da ke da ƙasa baki daya a matsayin ta mutu.

    PDP ta kara zargin Kwankwaso da fifita burinsa na siyasa fiye da jin dadin ‘yan Najeriya.

    "Shugaba na gaskiya zai mayar da hankali ne wajen magance matsalolin da ke addabar ƙasar maimakon yin kalamai masu kawo raba kan jama’a." sanarwar ta ƙara da cewa.

    Da yake karin haske kan matsalar tattalin arzikin da ake fama da shi a halin yanzu, Ologunagba ya jaddada cewa ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali a karkashin gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

    "Kwankwaso ya fi mayar da hankali kan burinsa na zama shugaban kasa yayin da ‘yan Najeriya ciki har da na jiharsa ta Kano ke fama da yunwa da ƙunci."

    "Sama da mutane miliyan 150 ne suka fada cikin talauci, inda miliyoyi suka rasa abin dogaro da kai, yayin da hauhawar farashin kayayyaki da man fetur suka yi tashin gwauron zabi." in ji sanarwar.

    PDP ta kara da cewa siyasar Kwankwaso ta samo asali ne tun lokacin da ya ke jam’iyyar, kuma abin takaici ne yadda ya ci gaba da mayar da hankali kan burinsa a irin wannan mawuyacin lokaci da kasar ke ciki.

  3. Za a kashe $600m wajen yaƙi da cutar mpox a Afirka

    Hukumar lafiya ta Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta aikewa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da tan 14 na kayan aikin asbiti domin yaƙi da yaɗuwar cutar ƙyandar biri, da aka yiwa laƙabi da mpox.

    Kayan aikin da aka bai wa Congo sun haɗa da kayan kare ma'aikatan lafiya daga kamuwa da cutar a yayin aikin su da kuma sauran magunguna da kayan aiki.

    Hukumr lafiya ta duniya ta ce nan da makonni masu zuwa za ta ƙara turawa ƙasar ƙarin kayan yaƙi da cutar da Majalisar Dinkin Duniya ta ƙaddamar da dokar ta ɓaci a kan yaƙi da ita, a ranar 14 ga watan Ogustan bana.

    Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ce ƙasar da aka fi samun yaduwar cutar mpox a Afirka.

    Haka nan kuma, cibiyar yaƙi da yaɗuwar cutuka ta Afirka da haɗin gwiwar hukumar lafiya ta duniya ta sanar da shirin kashe $600m wajen hana yaɗuwar cutar mpox a ƙasashe 14 na Afirka da aka samu ɓullar cutar.

    Daraktar shiyyar Afirka ta hukumar lafiya ta duniya, Dr Matshidiso Moeti ta ce matakin yana da muhimmanci wajen hana yaɗuwar cutar a nahiyar cikin gaggawa.

    Ta ce aikin zai gudana ne daga watan Satumban 2024 zuwa Fabrairun 2025.

  4. Amurka ta zargi Venezuela da mulkin kama karya

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya ce mafakar siyasar da dan takarar shugabancin kasar Venezuela ya nema a Sifaniya kai-tsaye na nuna irin mulkin kama karya na gwamnatin Venezuela.

    Mista Blinken ya ce, Edmundo Gonzalez shi ne mafi dacewa da mulkin demokuradiya a Venezuela. Mista Gonzalez dai ya alkawarta cigaba da fafutika, a wani sako da ya fitar bayan isar sa birnin Madrid.

    Ya nemi mafaka a Ofishin jakadancin Sifaniya da ke Caracas bayan bada sammacin kama shi kan zaben watan Yuli.

    Mista Blinken shi ne babban jami'in gwamnati a baya-bayanan da ke alla-wadai da yanayin da ak jefa Gonzalez.

  5. An kashe mutane 21 a sabbin hare-haren Sudan

    Akalla mutane 21 suka rasa rayukansu a hare-haren sama da aka kaddamar cikin dandazon mutane da ke cin kasuwa a yankunan kudu maso gabashin Sudan.

    Kungiyar liktoci ta Sudan ta ce dakarun RSF ne suka kai harin a birnin Sennar.

    Sannan Akwai gwamman mutanen da aka jikkata. Wannan rikici tsakanin sojoji da rundunar mayakan RSF ya tilastawa fararan-hula da dama tserewa daga yankunan Jihar Sennar baya ga wadanda yaƙin ke kashewa.

  6. Ƙarancin abinci mai gina jiki ya kashe yara 700 a Afghanistan

    Ma'aikatar lafiya a Afghanista ta ce yara 700 ne suka mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki da ke haddasa wasu cututtuka, a asibiti da ke wani yanki guda a cikin watanni shida da suka wuce.

    Wani jami'in Taliban ya shaidawa BBC cewa aƙalla a kullum ana samaun yara uku da ke mutuwa a asibitin Jalalabad, sannan a duk yara biyar da aka kai asibitin to yaro guda ne ke samun kulawa.

    Tun bayan ƙwace mulki da Taliban tayi harkar lafiya da abinci mai gina jiki ya koma karkashin kungiyoyin agaji, sai dai a bana abin ya ragu sosai saboda janye tallafi da ƙasashe suka yi.

    Sannan ta kuma ce yanayi ne da ya yi ƙamari sosai a yankuna daban-daban na ƙasar, inda ake samun ƙaruwar yaran da basa samun abinci, lamari da yanzu haka ke barazana da haddasa cututtuka ga yara sama da miliyan 3 da dubu ɗari biyu.

  7. Sallama

    Masu bin shafin kai-tsaye na BBC Hausa barkanmu da safiyar Litinin.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.