Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/09/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/09/2025.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonni kenan a wannan shafi na ranar Asabar.

    Muna nan tafe wasu sababbi gobe da safe.

    Kafin lokacin, Umar Mikail ne ke fatan za mu kwana lafiya.

  2. An hana tawagar Isra'ila shiga gasar tsere a Italiya

    Masu tseren keke a Italiya

    Asalin hoton, EPA

    An hana wata tawagar Isra'ila shiga fitacciyar gasar nan ta tseren keke mai tarihi da ake yi a Italiya mai suna Giro d'Italia, wadda za a yi a mako mai zuwa.

    Masu shirya gasar sun ce akwai haɗari sosai ga masu tseren da kuma sauran jama'a idan har aka bari kamfanin Isra'ila Israel-Premier Tech ya shiga saboda fargabar masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa za su iya kawo cikas.

    An ɗauki matakin ne bayan masu zanga-zangar sun hallara a wata gasar tseren ta Vuelta a España, inda suka jawo kammala wani zagayen da wuri ba yadda aka saba ba.

  3. Dubban 'yan Hezbollah na macin tunawa da Hassan Nasrallah a Lebanon

    Masu tunawa da Hassan Nasrallah a Lebanon

    Asalin hoton, Reuters

    'Yan kungiyar Hezbollah da magoya baya a yankunan waje na kudancin babban birnin Lebanon, Beirut, suna tarukan cika shekara ɗaya da kisan jagoran kungiyar Hassan Nasrallah da Isra'ila ta yi.

    Shirin taron ya janyo ƙarin zaman ɗar-ɗar a ƙasar ta Lebanon, wadda gwamnatinta ta yi alkawarin raba Hezbollah da makamanta kamar yadda yarjejeniyarta da Isra'ila ta tanada, wadda aka ƙulla domin kawo karshen yakinsu a shekarar 2024.

    Amma a wani jawabi da ya yi kan taron, jagoran kungiyar na yanzu Naim Qassem ya jaddada cewa, ko alama Hezbollah ba za ta amince da mikawa ko zubar da makamanta ba, yana mai cewa a shirye suke su ci gaba da yaƙi da Isra'ila.

    Duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka yi a watan Nuwamban bara, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kusan a kullum kan wuraren da take kira na Hezbollah ne.

  4. 'Yansandan Abuja sun kama buhuhunan wiwi da 'dillalan ƙwaya' 11

    Buhuhunan tabar wiwi da 'yansandan Najeriya suka ce sun kama

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen birnin Abuja ta ce ta kama mutum 11 da zargin safarar miyagun ƙwayoyi a wasu samame da ta kai a wasu lokunan birnin.

    Wata sanarwa a shafukan sada zumunta ta ce samamen sun kai ga gano buhun tabar wiwi 68.

    "Kamen wani ɓangare ne na yunƙurin daƙile ayyukan safara na gungun 'yanƙwaya da kuma rage aikata laifukan da shan ƙwaya ke haifarwa a birnin," in ji SP Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar a Abuja.

  5. Ma'aikatan jinya sun fara yajin aiki a jihar Zamfara

    Wani ma'aikacin jinya a Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ma'aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya reshen jihar Zamfara ta sanar da shiga yajin aiki na kwana shida a matsayin gargaɗi.

    Shugaban ƙungiyar National Association of Nurses and Midwives (NANM), Sani Shehu, ya faɗa yayin wani taron manema labarai ya ce sun ɗauki matakin ne domin jawo hankalin gwamnatin jihar kan sabon tsarin albashinsu.

    Ya ce duk da gwamnatin ta amince da sabon tsarin albashi na na ma'aikatan lafiya wato Consolidated Health Salary Structure (CONHESS), ta ƙi aiwatar da tsarin albashin likitoci na Consolidated Medical Salary Structure (CONMESS).

    Matakin nasu zuwa ne bayan ƙungiyar ta yi yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai daga 11 ga watan Satumba, wanda aka dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi musu.

    Shugaban ƙungiyar yanzu za su ci gaba da yajin aikin domin cika kwana shidan - daga Asabar zuwa Talata mai zuwa.

    Idan ba a biya musu buƙatunsu ba ma'aikatan jinyar za su shiga yajin aikin sai baba ta gani, Sani Shehu.

  6. PENGASSAN ta umarci mambobinta su katse wa matatar Dangote mai da gas

    Matatar Dangote

    Asalin hoton, Dangote Refinary

    Ƙungiyar manyan ma'aikata a fannin makamashin gas a Najeriya ta PENGASSAN ta bai wa mambobinta umarnin katse wa matatar mai ta Dangote iskar gas nan take.

    Petroleum and Natural Gas Senior Staff Association of Nigeria (PENGASSAN) ta ce ta ɗauki matakin ne saboda zargin matatar da korar ma'aikatanta da suka shiga ƙungiyar, kamar yadda kafar Channels TV ta ruwaito.

    Wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya fitar ta kuma umarci shugabannin rassanta da su katse duk wani bututun mai da ke samar wa matatar ɗanyen man fetur, da ma hana yi wa jiragen ruwa lodi.

    Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin "wanda ya zama dole domin kare 'yancin ma'aikata da tsarin mulki ya ba su na shiga ƙungiya".

    A jiya Juma'a ne matatar Dangote ta bayyana korar ma'aikata sama da 1,000, waɗanda ta bayyana da "masu yi mata zagon ƙasa". Sai dai wasu daga cikinsu da BBC ta zanta da su sun musanta zargin.

  7. Kun san abin da ya sa tekun Masar ke cin baƙi duk shekara?

    Kogi

    Asalin hoton, Getty Images

    A wajen karshen watan da ya gabata wani mummunan lamari ya faru a bakin tekun Abu Tlat da ke yankin Al-Ajami, a yammacin birnin Iskandiriya na kasar Masar, inda dalibai mata shida da wani dalibin namiji daya suka mutu wasu kuma suka jikkata.

    Lamarin ya faru ne a lokacin da tawagar dalibai daga jihar Sohag a daya daga cikin makaratun koyar da aikin otal suka je wajen atisaye.

    Bayanai sun nuna cewa igiyar teku ce ta ja daliban yayin da masu lura da su a lokacin suka kasa yin komai su cece su.

    Yasser Abdul Majeed, mahaifin Fares, daya daga cikin daliban da ruwan ya ci, ya ce : ''Ina duba Facebook kawai sai na ga labarin abin da ya faru daya daga cikin abokan karatunsu ya sa labarin, daga nan sai na kira shi, inda ya gaya min cewa ai ya rasu.''

  8. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 55 a Gaza - Asibitin Al Awda

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Wani ƙaramin asibiti a Gaza ya ruwaito cewa hare-haren Isra'ila daga safiyar yau zuwa lokacin haɗa wanan rahoton sun kashe aƙalla mutum 55.

    Ma'aikatan asibitin na Al Awda sun ce daga cikin waɗanda aka kashe har da mutum tara ƴan gida ɗaya da suke rayuwa a sansanin gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar Zirin Gaza.

    Mutane dai suna ci gaba da arcewa daga birnin Gaza saboda luguden wuta da sojojin Isra'ila ke yi a birnin a yunƙurin ƙasar na kutsawa yankin.

    A jibi Litinin ne ake sa ran Shugaban Amurka Donald Trump zai gana da Firaministan Isra'ila Benjemin Netanyahu - wanda ya nanata ƙudurinsa na "ƙarasa aikin da ya fara na murƙushe Hamas a jawabinsa na Majalisar Ɗinkin Duniya.

  9. Amurka za ta soke bizar Shugaban Colombia saboda halartar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa

    Gusta

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka ta ce za ta soke bizar shugaban Colombia Gustavo Petro bayan da ya halarci wata zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a birnin New York.

    Cikin wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce Mista Petro ya bukaci sojojin Amurka da su bijirewa umarni, da tada zaune tsaye.

    Sanarwar ta ce za a soke bizar tasa ne saboda yin kalaman da kasar ta ce ba su kamata ba, kuma suna iya tayar da hankali.

    Shugaban na Colombia yana Amurka ne don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya kuma tuni ya yi jawabi mai zafi ga taron shugabannin duniya.

  10. Sabon Olubadan ya buƙaci Tinubu ya amince da kafa jihar Ibadan

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Sabon Sarkin Yarbawa na Ibadan, wato Olubadan, Oba Rashidi Adewolu Ladoja ya yi kira ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya amince da kafa jihar Ibadan.

    Oba Rashidi ya bayyana haka ne a jiya Juma'a a lokacin da yake jawabin karɓar sandar mulki a birnin na Ibadan, inda ya ce samar da jihar na cikin manyan buƙatun mutanensa.

    "Majalisar masarautar Ibadan na da saƙo zuwa gare ka, shugaban ƙasa. Suna so ne aa kafa jihar Ibadan," in ji shi kamar yadda tashar Channels mai zaman kanta ta ruwaito.

    Yana tsaka da jawabin ne sabon babban sarkin ya ce mutane su miƙe domin "godiya" ga Tinubu tun kafin ma ya amince da buƙatar tasu.

    "Ina da yaƙinin cewa idan har Shugaba Tinubu zai amince da kafa sabuwar jiha daga Oyo, lallai na san Ibadan ce. Don haka muna kira da ka ɗauki wannan matakin cikin gaggawa, idan so samu ne ma kafin zaɓen 2027," in ji Oba.

    A taron wanda ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya, Tinubu ya taya sabon sarkin murna, "yau rana ce ta murna da tarihi. Ina taya ka murna bisa jajircewar da ka daɗe kana nunawa," in ji Tinubu.

    A ƙarshen jawabin ne Tinubu ya ƙara jan hankalin ƴan Najeriya, inda ya ce su ƙara haƙuri, sun kusa fara sharɓar ribar sauye-sauye da ya kawo a game da tattalin arziki.

  11. Shugaban Iran ya yi Allah-wadai da ƙaƙaba wa ƙasarsa takunkumi

    Iran

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya yi Allah-wadai da sake ƙaƙaba wa ƙasarsa takunkumi, lamarin da ya ce babu adalci a ciki.

    Ya yi martanin ne a yayin wata zantawa da manema labarai a birnin New York, yayin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kaɗa ƙuri'ar sake ƙaƙabawa ƙasarsa takunkumin da aka jingine a baya.

    Yunƙurin China da Rasha na jinkirta dawo da takunkuman ya fuskanci tangarɗa bayan Iran ta samu ƙuri'u huɗu kacal daga jimillar 15 da mambobin kwamitin suka kaɗa.

  12. Babbar lauyan Amurka ta buƙaci ƙarin tsaro ga jami'an shige da fice

    Trump

    Asalin hoton, EPA

    Babbar lauyar gwamnatin Amurka Pam Bondi, ta bayar da umarnin tura jami’an gwamnatin tarayya don kare jami’an shige da fice na ICE a fadin kasar, bayan wani hari da aka kai masu a Texas wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda.

    Ta kuma yi kira da a gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi da shirya kai harin da ma kan sauran jami'an tsaro na tarayya.

    A ranar Larabar da ta gabata ne wani dan bindiga ya bude wuta a wata cibiyar jami'an shige da ficen na ICE, lamarin da ya janyo mutuwar mutum guda, da kuma jikkatar wasu karin mutane biyu a Dallas.

    Babu wani wani daga cikin jami'an da ya mutu, ko ya ji rauni, amma FBI ta yi imanin cewa an kai harin ne saboda kyamar ayyukan jami'an.

    Dan bindigar ya kashe kansa a wurin.

  13. Matar da FBI ke nema ruwa a jallo ta mutu a Cuba

    Cuba

    Asalin hoton, Newsday RM via Getty Images

    Gwamnatin Cuba ta ce Joanne Deborah Byron, daya daga cikin matan Amurka da ake nema ruwa a jallo, ta mutu a Havana tana da shekaru saba'in da takwas a duniya.

    Hukumar tsaro ta FBI ta yi alkawarin ba da ladan dala miliyan daya ga duk wanda ya taimaka da bayanan da za su kai ga kama yar fafutukar da ake zargi da aikata ta’addanci da kuma tserewa daga gidan yari.

    Assata Shakur, kamar yadda wasu da dama suka san ta mamba ce ta wata kungiyar fafutukar yancin bakar fata da ake kira Black Leberation Army, mai tsananin kyamar tsatstsauran ra'ayin fararen fata.

    Wakilin BBC ya ce an same ta da laifin kisan wani dan sanda a shekarar 1973, amma daga baya ta arce daga kurkuku inda take zaman daurin rai da rai, kana ta tsere zuwa Cuba, don neman mafaka.

    Gwamnatin Cuban ta ce ta mutu ne sakamakon rashin lafiya.

  14. Ƙungiyar agaji ta MSF ta dakatar da ayyukanta a Gaza saboda hare-haren Isra'ila

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar agaji ta MSF ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukanta a birnin Gaza saboda hare-haren da Isra'ila ke kai wa.

    Kungiyar ta ce sojojin Isra'ilar sun kewaye cibiyoyin kula da lafiyarta, yayin da bai wuce kasa da kilomita guda tankokinsu, su kara inda suke ba.

    Dama dai Isra'ila ta bukaci Falasdinawa da su fice daga birnin na Gaza, wanda ta bayyana a matsayin tungar karshe ta Hamas.

    Sai dai hukumar lafiya ta duniya ta ce dubban mutanen ba za su iya fita ba, ciki har da dubu goma sha biyar da ke asibiti.

    Shugaban hukumar ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesu, ya ce hare-haren da ake kaiwa da kuma kewaye cibiyoyin kiwon lafiyar sun sa ayyukan ceton rayuka sun tsaya ciki.

  15. Mutum 10 sun rasu a wajen haƙo zinare a Zamfara

    Zamfara

    A Najeriya, ana can ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wani wurin hakar ma'adinai da ya rufta da mutane da dama, a kauyen Kadauri na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

    Zuwa yanzu dai an ciro gawarwakin mutum goma, wasu hudu zuwa biyar kuma suka tsira da munanan raunuka.

    Alhaji Bello Muhammad Ja-Baka, shi ne shugaban karamar hukumar ta Maru, ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin, inda ya ce ƙasa ce ta zaftare sanadiyar mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.

    "Su kuma aikin haƙo zinaren ba bisa ƙa'ida ba, ba su yi la'akari da yanayin ruwan ba sai suka ci gaba da aiki, hakan ya sa ƙasar ta rufta da su," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa ana ci gaba da tuna ƙasar da tunanin akwai wasu a ciki.

    Ya ce gwamnati a shirye take da tabbatar duk masu aikin haƙo zinare sun samu lasisi a wajen gwamnati da kuma wajen jami'an tsaro.

  16. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga nan sashen Hausa na BBC.

    A yau ma za mu ɗaura daga inda muka tsaya a labaran da muke kawo muku na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.