Yadda dajin Kainji ke neman zama maɓoyar ƙungiyoyin ƴanbindiga a Najeriya
A farkon watan Fabrairun shekarar 2026 ne mahara sama da 100 suka yi dirar mikiya sanye da kayan sojoji a ƙauyukan Woro da Nuku da ke jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya a Najeriya, inda suka kashe sama da mutum 75.
Sun dira a ƙauyukan ne da yammacin ranar Talata a daidai lokacin da manoman ƙauyukan suke komawa gida daga gonakinsu.
Babban abin da ya ja hankali shi ne yadda maharan suka aika da wasiƙar zuwa garin domin "wa'azi", sannan suka shiga, suka yi aika-aikarsu, sannan suke fice ba tare da fuskantar matsala ba.
Bayan harin ne gwamnatin Najeriya ta zargi mayaƙan Boko Haram da kai harin, duk da cewa ƙungiyar ba ta ɗauki alhaki ba, duk da cewa ta fi gudanar da ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya.
A lokacin ne mutane suka fara tambayar wai daga ina maharan suka taso, kuma su wane ne su?