Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/12/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Haruna Kakangi

  1. Kotun Koriya ta Kudu ta ba da umarnin kama shugaban ƙasa da aka tsige

    Kotu a Koriya ta Kudu ta bayar da sammancin kama Shugaban Ƙasa Yoon Suk Yeol, wanda majalisa ta tsige da dakatar da shi sakamakon kokarin da ya yi na sanya dokar soji a ƙasar.

    Masu bincike sun buƙaci a bayar da sammanci ne bayan ya ƙi amsa gayyatar da aka yi masa domin amsa tambayoyi.

    Ba a faɗi lokacin da za a kamo shi ba, sai dai wakilin BBC a birnin Seoul ya ce ana fatan wannan barazana ta iya tilasta wa Mista Yoon gabatar da kansa.

    Wasu 'yan kasar na ta tsokacin cewa tuntuni ya kamata a kama shugaban bayan ya ayyana batun kafa dokar soji.

    Lauyansa dai ya ce sammacin kama shugaban ya saba doka da 'yancinsa na ɗan'adam.

  2. Maraba

    Ma'abota BBC Hausa, barkamu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Talata.

    Umar Mikail ne zai kawo rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da maƙwabtanta bisa kulawar Haruna Ibrahim Kakangi.

    Mu je zuwa.