Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/12/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Haruna Kakangi

  1. Kaso 90 na al'ummar Puerto Rico na zaune cikin duhu sakamakon katsewar layin wutar

    Puerto Rico

    Asalin hoton, Getty Images

    Kusan kashi 90 cikin 100 na al'umar Puerto Rico na zaune babu wutar lantarki, sakamakon katsewar da babbar tashar raba lantarkin kasar ta yi.

    Kamfanin LUMA da ke raba lantarkin wato LUMA Energy, ya ce alamu sun nuna an samu matsalar ne sakamokon lalacewa da wata ta karkashin kasa ta yi.

    Kamfanin makamashi na Zimbabwe ya sanar da zai dauki kwanaki 2 kafin komai ya daidaita. A bangare guda kuma, an fara kawo wutar lantarkin a asibitoci da wuraren taruwar jama'a a birnin San Juan da sauran.

    A ɓangare guda shugaban ƙasar Pedro Pierluisi, ya ce yana buƙatar cikakken a bincike da lalubo maganin matsalar nan ba da jimawa ba.

  2. Ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na MDD ya yi gargadi kan kisan yara a Gaza

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin hukumar kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nuna damuwa kan munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa asibitoci a zirin Gaza da ke ƙara jefa Falasdinawa cikin mummunan yanayi.

    Hukumar ta ce an yi wa asibitoci ƙawanya tare da kashe mutane ciki har da majinyata.

    Da ma dai ma'aikatar lafiya da Hamas ke tafiyar da ita, ta ce jarirai na mutuwa a zirin Gaza saboda cinkoso a sansanonin 'yan gudun hijira.

    Hamish Young wanda jami'in hukumar da ke kula da ilimin ƙananan yara ne Majalisar Ɗinkin Duniya ne, UNICEF, ya ce "adadin yaran da suka mutu a Gaza daga fara yaƙin nan kawo yanzu sun haura dubu 15, wannna lamari ne mai tada hankali."

    Ya ƙara da cewa "wata damuwar ita ce ana tsananin sanyi a halin yanzu, ga ruwan sama da ake shekawa kamar da bakin ƙwarya, ina za mu kai yaran nan."

  3. Ahmad al-Sharaa ya gana da shugabannin Ƙurdawa da Kiristoci kan makomar Syria

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagoran ƴantawaye kuma shugaban riƙo a Syria Ahmad al-Sharaa ya yi wata tattaunawa da wakilan mabiya addinin Kirista da Kurdawa, a ƙoƙarin da yake yi na samar da gwamnatin riƙo ta haɗin kan ƙasa baki ɗaya.

    Dukkan tsirarun addinan marasa rinjaye sun nuna damuwa kan kasancewar sabbin shugabannin Syria bisa kasancewarsu masu ikirarin jihadi a baya.

    Sai dai Ahmad al-Sharaa ya bayyana cewa ƙungiyar 'yantawayen Kurdawa ta SDF, za ta rikiɗe zuwa rundunar sojin ƙasar.

    Wannan ne karon farko da Sharaa ke ganawa da wakilai ko shugabannin Kurdawa tun bayan 'yantawayen sun hamɓarar da mulkin Basharul Assad.

  4. Zimbabwe ta haramta aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar

    Emmerson

    Asalin hoton, Getty Images

    A hukumance ƙasar Zimbabwe ta kawo karshen yanke hukuncin kisa, bayan shugaba Emmerson Mnangagwa ya rattaɓa hannu kan dokar.

    A yanzu za a maye gurbin hukuncin kisa da zaman kaso na har abada, kuma mutane kusan 60 ne za su fara cin gajiyar dokar a ƙasar.

    An shafe gwamman shekaru ana ta kai ruwa rana kan batun hukuncin kisa, amma kotuna suka ci gaba da yanke hukuncin da suka haɗa da samun mutum da laifin kisan kai da cin amanar ƙasa da ayyukan ta'addanci.

    Kungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi maraba da wannan doka da ta ce mai cike da tarihi ce.

  5. Mun kama ɓatagari fiye da 2000 a 2024 - ƴansandan Kano

    COMMISSIONER OF POLICE KANO

    Asalin hoton, FACEBOOK/ABDULLAHI HARUNA KIYAWA

    Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta ce ta kama masu aikata laifuka su 2,425 da kuma ceto mutane 55 da akayi ƙoƙarin safararsu, ko garkuwa da su ko kuma sace su a shekarar 2024.

    Kwamishina ƴansandan jihar, Salman Dogo Garba ya bayyana hakan yayin da yake ƙarin haske ga manema labarai kan muhimman nasarorin da rundunar ta samu a ƙoƙarinta na yaƙi da laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.

    ''A farkon shekarar nan, an samu matsalolin tsaro a kananan hukumomi 44 na jihar da suka haɗa da barazanar shigowar ƴanbindiga, garkuwa da mutane da sata a kauyuka da ke ƙananan hukuumomi 17 da ke iyaka da jihohin Kaduna, Katsina, Jigawa da kuma Bauchi.'' a cewar shi.

    Sai kuma dawowar munanan ayyukan ƴan daba, shaye shaye da kuma wasu muggan laifuka a ƙananan hukumomi takwas da ke birnin Kano, sai kuma rikicin manoma da makiyaya a ƙananan hukumomi 19 da ba sa iyaka kuma ba sa cikin birni.

  6. Hotunan bikin karrama gwarazan gasar rubutun gajerun labarai ta matasan Kano

    .

    Asalin hoton, KSCB

    .

    Asalin hoton, KSCB

    .

    Asalin hoton, KSCB

    .

    Asalin hoton, KSCB

    .

    Asalin hoton, KSCB

    .

    Asalin hoton, KSCB

    .

    Asalin hoton, KSCB

  7. Yadda aka gabatar da bikin karrama gwarzan gasar rubutu ta matasa a Kano

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
  8. Tokyo da Seoul sun shiga sabuwar shekara

    Japan da Koriya ta kudu su ne ƙasashen baya-bayan nan da suka kaɗa kararrawar shigar sabuwar shekara, wadda ke nuna farkon shekarar 2025 a ƙasashen.

    A Japan, mutane sun yi tururuwa a wurin ibada na Tokudai-ji da ke Tokyo domin kaɗa kararrawar maraba da sabuwar shekara.

    Kamar yadda muka ruwaito tun da farko, bikin sabuwar shekara a Koriya ta kudu za a yi shi lami a wannan shekarar saboda mutuwar mutane 179 sakamakon hatsarin jirgin sama na Jeju Air samfurin Boeing 737 da akayi a ranar 29 ga watan Disamba.

    Gwamnatin babban birnin Seoul ta ce za tayi taronta na shekara shekara na kaɗa kararrawa ba tare da bukukuwa ba.

  9. Angelina Jolie da Brad Pitt sun cim ma matsaya kan rabuwar aurensu

    Angelina Jolie da Brad Pitt

    Asalin hoton, PA Media

    Angelina Jolie da Brad Pitt sun cim ma matsaya game da rabuwar aurensu bayan shekara takwas da mutuwar auren.

    Tsofaffin ma'auratan da suka ɗaura aure a 2014 na da 'ya'ya shida, kuma suna cikin mafiya shahara a duniya - har ma ana yi musu laƙabi da 'Brangelina'.

    Jolie ce ta nemi saki a 2016 saboda abin da ta ce "matsalar da ba za ta gyaru ba". Daga baya wasu takardun kotu suka nuna cewa tana zargin Pitt ne da cin zarafinta da kuma biyu daga cikin 'ya'yanta a cikin jirgi.

    Ba a tuhumi Pitt ba bayan 'yansanda sun gudanar da bincike kuma ya musanta lamarin.

  10. Hare-haren Isra'ila kan asibitocin Gaza ka iya zama laifukan yaƙi - MDD

    Kamal Adwan

    Asalin hoton, Reuters

    Ofishin hukumar kare haƙƙin dan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya nuna damuwa kan munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa asibitoci a Zirin Gaza na ƙara jefa Falasdinawa cikin mummunan yanayi.

    Ta ce hakan ka iya zama laifukan yaki da take hakkin ɗan'adam.

    Wakiliyar BBC ta ce rahoton na MDD ya yi bayanin yadda sojojin Isra'ila ke kai hari asibitocin Gaza da yi masa ƙawanya - babu abinci ko magunguna.

    Wannan na zuwa ne a lokacin da iyalan daraktan Asibitin Kamal Adwan suka yi kira ga al'ummar duniya su taimaka wajen ganin Isra'ila ta sako Dr Hussam Abu Safiya.

    Dakarun Isra'ila sun tsare da likitan ne tun ranar Juma'a a samamen da suka kai.

  11. MDD ta nemi Taliban ta janye haramci kan aikin mata a ƙungiyoyin agaji

    Shugaban sashen kare haƙƙi na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya nemi gwamnatin Taliban a Afghanistan ta janye matakin hana mata aiki a ƙungiyoyin agaji.

    Volker Turk na mayar da martani ne ga wata wasiƙa da ministan tattalin arziki na Afghanistan ya wallafa wadda ta jaddada matakin da aka ɗauka shekara biyu da suka wuce.

    Cikin wata sanarwa, Mista Turk ya ce ganin yadda rabin al'ummar Afghanistan ke zaune cikin talauci, ƙungiyoyin agaji na taka muhimmiyar rawa wajen tseratar da rayuka.

  12. 'Yan Australia sun shiga sabuwar shekara

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bukukuwan sabuwar shekarar

    Babu daɗewa agogo ya ce ƙarfe 12:00 na dare a birnin Sydney na Australia, abin da ke nufin sun tsunduma shekarar 2025.

    Australia

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Tinubu na cikin mutanen da suka fi tsara manyan laifuka da rashawa a 2024 - OCCRP

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu na cikin na gaba-gaba a jerinn mutanen da suka fi tsara manyan laifuka da kuma aikata cin hanci da rashawa, a cewar rahoton cibiyar kula da aikata manyan laifuka da rashawa ta duniya.

    CIbiyar Organized Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP) kan nemi 'yanjarida da ƙwararru da ɗaiɗaikun mutane su kaɗa ƙuri'a wajen zaɓen mutanen da suka fi aikata tsararrun laifkuka a ɓangaren cin hanci da rashawa duk shekara.

    Tinubu ne ya zo na uku a jerin, yayin da tsohon Shugaban Syria Bashar al-Assad ya zo na ɗaya "saboda abubuwan da suka faru a ƙasar a baya-bayan nan," in ji OCCRP.

    Sai dai zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ko Tinubu kansa ba su ce komai ba game da sakamakon ƙuri'ar.

    Duk da cewa shi ne ya fi kowa yawan ƙuri'u, Shugaban Kenya William Ruto ne ya zo na biyu bayan ya samu ƙuri'a sama da 40,000.

    Sama da shekara 10 kenan ana fitar da sakamakon ƙuri'ar, inda a wannan karon aka bai wa Shugaban Ƙasar Equatorial Guinea "lambar zambo ta wanda bai taɓuka komai ba" (lifetime non-achievement award) a matsayin shugaban da ya fi kowa daɗewa a kan mulki a duniya.

  14. Hisbah ta fara kwashe yaran da ke gararamba kan titunan Kano

    ...

    Gwamnatin Kano ta fara kwashe 'dubban' yara da ke rayuwa a kasuwanni da ƙasan gadoji a Kano, babban birnin jihar.

    Gwamnatin ta fara ɗaukar matakin ne a jiya Litinin, inda ta samar da wani sansanin ajiyewa da kuma tantance yaran.

    Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa ya ce "mun samu rahoton akwai ɗaruruwa ko kuma dubban ƙananan yara da ba su haura shekara 15 ba waɗanda suke kwana a ƙarƙashin gadoji da cikin tashoshi da kuma kasuwanni."

    "Ci gaba da rayuwarsa a waɗannan wurare zai iya haifar da matsala ta tsaro da ta zamantakewa a nan gaba," in ji Daurawa.

    Shugaban na hukumar Hizba ya ce alƙaluman da suke da su sun nuna cewa akwai irin waɗannan yara masu gararamba a kan tituna sama da 5000.

    Ya kuma bayyana cewa za a tara yaran da aka kwashe ne a wata cibiya, inda za a tantance su, sannan a san matakan da za a ɗauka.

    Kano ce jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ke da yawan ƙananan yara waɗanda ba su zuwa makaranta.

    Yaran da Hisbah ta ajiye a sansanin alhazai na jihar Kano

    Asalin hoton, Kano State Hisbah

    Bayanan hoto, Yaran da Hisbah ta ajiye a sansanin alhazai na jihar Kano

    Duk da cewa jihar na daga cikin waɗanda suka sanya hannu kan dokar kare hakkin yara a Najeriya, amma har yanzu akwai dubban yara da ke tallace-tallace ba tare da zuwa makaranta ba, yayin da wasu yaran kuma ke barace-barace a kan tituna da sunan neman ilimin addini.

    Sheikh Daurawa ya ce bayan kammala tantance yaran, da inda suka fito, za a sanya wasu daga cikinsu makaranta yayin da za a koya wa wasu sana'a.

    Ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar gurfanar da wasu iyayen da aka tsinci yaran nasu na gararamba kan titi, a gaban kotu.

    "Wanda ya yi sakaci ya bar ɗansa yana yawo a kan titi duk da cewa yana da halin ɗaukar nauyinsa, to za mu gurfanar da shi a gaban kotu".

    Sai dai ya ce yaran da ba su da iyaye ko waɗanda rikici ya tarwatsa - gwamnatin za ta ɗauki matakin gyara musu rayuwa ta hanyar ba su ilimi da koya musu sana'a.

  15. An shiga sabuwar shekara a Newzealand

    Newzealand

    Tuni al'ummar New Zealand suka shiga sabuwar shekara ta 2025, har ma mazauna birnin Auckland sun fara biki kamar yadda sua saba.

    Newzealand
  16. Ukraine ta ce ta kakkaɓo jiragen Rasha marasa matuƙa 16

    Jiragen Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin sama ta Ukraine ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami shida cikin 21 da Rasha ta harba da tsakar dare.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Rasha ta yi amfani da jirage marasa matuƙa 40 wajen kai wa Ukraine ɗin hari, kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na Telegram.

    Ta ƙara da cewa ta yi nasarar harbe 16 daga cikin jiragen, sai kuma 24 da suka kasa kai wa inda aka aika su.

  17. Amurka na zargin China da yi mata kuste a ma'aikatar baitil mali

    Wasu masu kutse da ke samun goyon bayan gwamnatin China sun kutsa kwamfutocin ma'aikatar baitil malin Amurka a farkon watan nan, a cewar hukumomi a Amurka.

    Ma'aikatar baitil malin ta bayyana kutsen da "babban al'amari" bayan ta sanar da 'yanmajalisa abin da ya faru cikin wata wasiƙa.

    Ta ce masu kutsen sun iya ganin bayanai na ma'aikata da wuraren da zamansu, da ma wasu bayanan da ba na sirri ba.

    Hukumar ta gwamnatin Amurka ta ce tana aiki da hukumar tsaro ta FBI domin gudanar da bincike kan ɓarnar da lamarin haifar.

    China ta musanta hannu a kutsen, amma shi ne karo na baya-bayan nan da ake samun abin kunya a ɓangare tsaron Amurka.

  18. Akwai yiwuwar Man United ta koma ƙasan teburi - Amorim

    Amorim

    Asalin hoton, EPA

    Shekara 50 kenan rabon da Manchester United ta faɗi daga gasar Premier League.

    Man United na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka zarta kowacce samun nasara a Ingila da ma duniya baki ɗaya, kuma mun saba ganin kulob ɗin yana shiga tsaka mai wuya a lokuta daban-daban.

    Sai dai a wannan karon lamarin ya sha bamban. A daren da ya gabata ne Newcastle ta doke Man United 2-0 har gida.

    Bayan kammala wasan da Newcastle ɗin ta ɗaiɗaita United a minti 30 na farko, mai horarwa Ruben Amorim ya fara tunanin faɗawa "relegation zone" - wato komawa ƙasan teburi.

    Da sashen BBC Sport ya tambaye shi game da ko suna ƙoƙarin guje wa faɗawa ƙasan teburin a yanzu, Amorim ya amsa da cewa: "ina akwai yiwuwar hakan. Dole ne mu faɗa wa magoya bayanmu gaskiya."

    Sakamakon wasan ya sa United ta koma ta 14 a teburi da tazarar maki bakwai tsakaninta da 'yan ukun ƙarshe.

  19. Silame: Harin bam kan fararen hula a Sokoto ya wuce gona da iri - ACF

    Silame

    Ƙungiyar tuntuɓa ta dattawan arewacin Najeriya ta bayyana harin da ya kashe fararen hula a yankin Silame na jihar Sokoto a matsayin "abin da ya wuce gona da iri".

    A ranar 25 ga watan Disamba ne bamabamai suka kashe aƙalla mutum 10 a ƙauyuka biyu, inda suka zargi rundunar sojin Najeriya da jefa musu makaman bisa kuskure yayin da take kai wa 'yan ƙungiyar Lakurawa hare-hare.

    Sai dai rundunar ta musanta tana mai cewa bamabaman da Lakurawan suka dasa ne suka tashi da mutanen.

    Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), ta shawarci rundunar sojin Najeriyar da ta "sake dabara game da yaƙi da matsalar tsaro", kamar yadda kakakin ƙungiyar Farfesa Tukur Baba ya bayyana cikin wata sanarwa.

  20. Rundunar 'yansanda a Katsina ta ce ta kashe 'yanfashi 40 a 2024

    Aliyu Musa

    Asalin hoton, Katsina State Police

    Kwamashinan 'yansanda na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Aliyu Musa, ya ce rundunarsu ta kashe 'yanfashin daji 40 daga farko zuwa ƙarshen shekarar 2024.

    Da yake magana yayin wani taron manema labarai na ƙarshen shekara a birnin Katsina ranar Litinin, kwamashinan ya ce sun kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su 319, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Kazalika a cewarsa, sun kama aƙalla mutum 916 a wannan tsakanin.

    "Mun samu nasarar ɗaiɗaita gungun miyagu da dama, mun ƙwato makamai, mun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan mun yi nasarar gurfanar da wasu da dama a gaban kotu," in ji shi.