Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 07/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail da Isiyaku Muhammed

  1. Trump ya yi barazanar kara wa China harajin kashi 100

    Shugaba Donald Trump, na Amurka, ya yi barazanar zafafa yaƙin kasuwanci da ke tsakaninsu da China, ta hanyar kakaba karin harajin kashi 50 cikin 100 na kayayyakinsu, muddin Beijing ba ta jingine shirinta na mayar da martani ba.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump, ya ce zai kawo karshen duk wata yarjejeniya da ke tsakaninsu, muddin China ba ta yi biyayya ba.

    Wannan harajin da Trump ke shirin sanya wa China zai haura kashi 100 cikin 100.

    A mako mai zuwa ne haraje-harajen da China ta sanya ita ma kan kayayyakin Amurka za su soma aiki.

  2. Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugabannin duniya su dauki matakin dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Shugabannin manyan hukumomi shida na Majalisar Dinkin Duniya, sun roki shugabannin duniya su dauki matakan gaggawa cikin hikima domin dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, domin a samu damar shigar da kayan agaji kamar abinci da magunguna ga mabukata.

    Makonni uku da suka gabata Isra'ila ta koma kai hare-hare da kuma datse duk wata dama ta kai agaji da man fetur, yayin da Hamas ta ƙi yar da a tsawaita matakin farko na yarjejeniyar da suka cimma.

    A birnin Alkahira, shugabannin Faransa da Masar da Jordan sun bukaci a gaggauta dawo da tsagaita wuta a zirin Gaza.

  3. Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen ƙasar

    A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta bayyana Hausa a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar yayin da sauran harsuna ta ayyanasu a matsayin na magana.

    Kazalika an kuma bayyana harshen Ingilishi da Faransanci a matsayin harsunan aiki.

    To sai dai kuma ba dukkanin 'yan kasar ne ke maraba da wannan mataki ba.

    An kiyasta cewa akwai mutum miliyan 18 da ke jin harshen hausa a Jamhuriyar Nijar, abin da ake ganin wannan ne ya sanya gwamnatin kasar ta ayyana shi a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar.

    To sai dai kuma ba dukkanin 'yan kasar ne wannan mataki ya yi wa dadi ba, inda wasu ke cewa ya kamata a yi nazari sosai a kai.

    Harshen Hausa shi ne ke matsayin na uku a Afirka inda kasashe da dama a Afirka a ke samun masu jin harshen.

    Akwai dai masu jin harshen Hausa a kasashe kamar Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi da Sudan da Benin da Togo da Gabon da kuma Burkina Faso.

  4. Najeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar yaƙi da miyagun ƙwayoyi

    Najeriya da Saudi Arabiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimta domin karfafa yaki da hada-hadar kwayoyi.

    A ranar Litinin Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta Najeriya da kuma Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Saudiyya GDNC, suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Riyadh.

    Cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ya ce kasashen biyu sun amince su kara karfafa yaki da fataucin miyagun kwayoyi a dukkan iyakokinsu.

    Da ya ke magana a wajen sanya hannu kan yarjejeniyar, shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, mai ritaya, ya ce dukkan kasashen sun jima suna yin hadaka da bangarori daban daban.

    Marwa, wanda ya samu rakiyar darakta a sashen bincike da gudanarwa na hukumar, Ahmed Ningi, ya ce dukkan kasashen na da kyakkyawar alaka a tarihi.

    Ya ce," A yau rana ce ta musamman mai matukar muhimmanci ga dukkan kasashen biyu."

    " Yau rana ce da ta kara kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu, musamman hukumomin da ke yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi." in ji Marwa.

    Da ya ke bayani a game da muhimmancin yarjejeniyar, Marwa, ya ce hada-hadar da miyagun kwayoyi ta zamo babban kalubale a duniya wanda ke bukatar daukar kwakkwaran mataki.

    Ya ce a duk inda ake ta'ammali da kwayoyin masu illa to akwai babbar barazana ga al'ummar da ke wajen.

  5. Ƙananan yara na karya ƙa'idar tsawon lokacin amfani da waya a China

    Wani bincike da kafar yada labaran China ta yi ya bankado hanyoyi da dama da yaran kasar China ke tsallake dokokin da ake sanyawa na rage yawan lokacin da suke amfani wayoyin hannu.

    Gwamnatin kasar ta takaitawa yara 'yan kasa da shekara 18 sa'oin da suke amfani da wayoyin hannu.

    Kafar yada labaran ta gano wasu kamfanoni da ke sayarwa da yara bayanai na karya wadanda ke ba su damar kwashe tsawon lokaci suna amfani da wayoyin hannunsu.

    Wani kamfani mai suna Tencent, da ke samar da manhajar wasanni a wayoyin salula, ya ce ya toshe irin wannan manhajar da aka kaddamar a bara domin maganin irin yaran da ke amfani da ita don kayyade musu lokacin da ya kamata su rinka amfani da wayoyinsu na salula.

  6. Saudiyya ta ayyana ranar da masu aikin Umrah za su fice daga kasar

    Ma'aikatar aikin Hajj da Umrah ta Saudi Arabiya ta kebe ranar 1 ga watan Dhul Qada, wadda ta zo dai-dai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ya shiga kasar domin yin Umrah ya fice.

    Ma'aikatar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa.

    Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi dai-dai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita.

    Ma'aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har ya wuce lokacin da kebe, to ko shakka babu ya saba ka'ida sannan kuma zai fuskanci hukunci.

    Daga nan ta bukaci mutane da ma kamfanonin da ke shirya zuwa aikin Umrah da su kiyaye da wadannan lokuta da aka kayyade.

    Ma'aikatar ta yi gargadin cewa duk wani jinkiri na barin mutane kasar za a dauke shi kamar karya doka.

    Ta ce duk kamfanin da aka samu da kin bayyana mutanen da suka ki koma wa kasashensu to za a ci tararsu riyar dubu 100.

  7. Gwamnonin APC sun kai wa Muhammadu Buhari ziyara

    Kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya karkashin jagorancin shugabanta gwamnan Imo Sanata Hope Uzodinma, ta kai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyarar ban girma a gidansa da ke Kaduna.

    Bayan shugaban kungiyar, sauran gwamnonin da suke cikin tawagar ma su ziyarar sun hada da gwamnan Kaduna da na Gombe da Kwara da Nasarawa da Ebonyi da Kebbi da Edo da Kogi da Ondo da Ekiti da kuma Benue.

    Sauran 'yan tawagar sun hadar da mataimakin gwamnan Jigawa da ministan kasafin kudi da tsare-tsare.

  8. Ana alhinin kisan kiyashin Rwanda bayan shekara 31

    Rwanda na gudanar da bikin zagayowar kisan kiyashin da aka yi wanda aka rasa rayukan akalla mutum dubu 800 yawancinsu 'yan kabilar Tutsi.

    An fara kisan ne a ranar 7 ga watan Aprilun 1994, bayan da aka harbo jirgin da shugabannin Rwanda da Burundi suke ciki lamarin da ya yi sanadin mutuwarsu.

    Masu tsattsauran ra'ayi daga kabilar Hutu sun dora alhakin harbo jirgin a kan 'yan kabilar Tutsi.

    Shugaba Paul Kagame, wanda shi ne jagoran kungiyar Rwandan Patriotic Front ta 'yan kabilar ta Tutsi shi ne ya kaddamar da bikin tunawa da kisan kiyashin ta hanyar sanya furanni a wurin da aka ware domin tunawa da kashe-kashen da aka yi.

  9. Algeria ta janye jakadunta daga Nijar da Mali

    Ƙasar Algeria ta yi wa jakadunta da ke Jamhuriyar Nijar da kuma Mali kiranye sannan ta kuma jinkirta tura jakadanta zuwa Burkina Faso a matsayin martani kan matakin da ƙasashen uku suka ɗauka na janye jakadunsu daga ƙasar ta Algeria.

    A makon da ya gabata ne sojojin Algeria suka kaɓo wani jirgi maras matuƙi mallakin ƙasar Mali bayan ya karya ƙa'idojin sararin samaniyarta a kusa da garin Tin Zaoutine da ke kan iyakar ƙasashen biyu.

    Mali ta sha zargin Algeria da bai wa ƴan tawayen Azbinawa mafaka a kan iyakar ƙasashen.

    A wata sanarwa mai ƙunshe da kausasan kalamai, ma'aikatar harkokin waje ta Algeria ta ce ba za ta ɓata lokacinta wajen mayar da martani kan zargin da Mali ke yi mata na taimaka wa ta'addanci ba.

  10. Ambaliya ta kashe mutum 33 a Kongo

    Ruwa kamar da bakin ƙwarya ya kashe aƙalla mutum 33 a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, a cewar hukumomi.

    Mazauna yankin na ta yunƙurin guduwa ta cikin ruwan, da ninƙaya, ko kuma a kwale-kwale.

    Birnin na da mazauna miliyan 17, wanda ke da maƙotaka da kogin Kongo - ɗaya daga cikin mafiya girma a duniya.

    Ana yawan yin ambaliya, babu daɗewa kogin ya yi cika fiye da kmairsa cikin shekara 60.

    Wasu ɓangarorin birnin na fama da zaizayewar ƙasa, abin da shugaban ƙasar ya ce sauyin yanayi na ƙara ta'azzara lamarin.

    Ruwa ya share gidaje da yawa a yammacin Kinshasa ranar Juma'a zuwa wayewar garin Asabar.

  11. Ƙasashen Turai na ta shirin ramuwa kan Amurka game da ƙarin haraji

    Ministocin kasuwanci a Turai na ta fitar da sanarwa a fusace kan matakan da za su ɗauka, yayin da suka isa Luxembourg domin gudanar da taro kan halin da suke ciki.

    Ministan Faransa ya ce su ma daga bangarensu ba za su sassauta ba wajen ƙaƙaba haraje-haraje kan kusan komai na Amurka.

    Sai dai ministan da ke wakiltar Ireland ya yi gargadin cewa wannan mataki nasu musamman kan abubuwa da suka jiɓanci fasaha na iya sake ta'azzara yanayin da ake ciki.

    Italiya kuma na ganin Turai ta ɗage batun sanya harajin zuwa makonni biyu nan gaba.

    Wakilin BBC ya ce gabannin taronsu a Luxembourg, ministocin na ganin kamar gwamnatin Amurka na son amfani da ƙarfinta na kasuwanci da ta kankane wajen cin moriyar ƙananan ƙasashe.

  12. Farashin ɗanyen fetur ya yi mummunar faɗuwa a kasuwar duniya

    Farashin ɗanyen man fetur samfurin Brent - wanda aka fi yawan ƙayyade farashi da shi a duniya - ya yi faɗuwa mafi muni cikin shekara biyar.

    Faɗuwar da kusan kashi 3.2 cikin 100 - zuwa dala 63.49 kowace ganga - ta faru ne a yau Litinin da misalin ƙarfe 11:00 agogon Najeriya da Nijar.

    Rabon ya yi irin faɗuwar tun watan Afrilun 2021.

    Shi ma samfurin West Texas Intermediate (WTI) ya faɗi zuwa kashi 3.58, kamar yadda kamfanin labarain na Reuters ya ruwaito.

    Faɗuwar farashin ta faru ne sakamakon sanarwar da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar ta ƙaƙaba wa dukkan ƙasashen duniya ƙarin harajin shifgar da kaya ƙasarsa.

    Hakan ya sa samfurin Brent ya faɗi da kashi 10.9 cikin 100, yayin da shi ma WTI ya faɗi da 10.8.

  13. 'Yansanda sun turnuƙe masu zanga-zanga da hayaƙi mai sa hawaye a Abuja

    'Yansandan Najeriya sun fatattaki masu zanga-zangar neman shugabanci nagari a Abuja babban birnin ƙasar ta hanyar harba musu hayaƙi mai sa hawaye.

    Masu zanga-zangar ƙarƙashin jagorancin Omoyele Sowore sun sha taƙaddama da 'yansanda a kan titi kafin daga baya su ci gaba da macinsu.

    Sai dai lamarin ya sauya salo ne a unguwar Maitama da ke ƙwaryar birnnin Abuja, inda masu zanga-zangar suka fara guje-guje bayan turnuƙe su da hayaƙin.

  14. Kuɗaɗen crypto sun ragargazo saboda ƙarin harajin Trump

    Kuɗaɗen intanet na cryptocurrency akasari na cin gashinsu ne daga babbar kasuwar hada-hadar kuɗi - amma yanzu sun fuskanci matsala kamar sauran.

    Ya zuwa ƙarfe 09:45 agogon Najeriya, farashin Bitcoin ya faɗo da kashi 7 cikin 100 inda ake kasuwancinsa kan dala 76,605. Tun da farko a ranar Litinin ya yi faɗuwa mafi muni cikin wata biyar.

    Ethereum, na biyu a daraja, shi ma ya fuskanci faɗuwa da kashi 18 cikin 100 a safiyar Litinin, inda shi ma XRP ya fuskanci irin wannan faɗuwar.

    Kuɗaɗen cryopto sun samu tagomashi cikin gaggawa bayan nasarar da Donald Trump ya yi a matsayin shugaban Amurka. Ya ja hankalin masu zuba jari da alƙawurran "mayar da Amurka babban birnin crypto" da kuma kafa rumbun ajiyar kuɗaɗen na gwamnati.

  15. Mene ne buƙatun masu zanga-zangar Take it Back a Najeriya?

    Ƙungiyar Take it Back da Omoyele Sowore ke jagoranta ba baƙuwa ba ce a harkokin zanga-zanga a Najeriya.

    Ita ce ta ƙirƙiro zanga-zangar nan ta ReveolutionNow da aka yi a wasu sassan Najeriya a shekarun baya da zimmar "yaƙi da rashin shugabanci nagari".

    A wannan karon ma, masu zanga-zangar na ɗauke da wasu kwalaye da ke cewa "a kawo ƙarshen mummunan shugabanci".

    Wasu kwalayen kuma na neman a soke dokar laifuka ta intanet wato cybercrime act.

    Kazalika, wasu ɗauke da ƙyallaye masu neman 'yancin faɗin albarkacin baki.

  16. 'Yansanda na tarwatsa masu zanga-zangar Take it Back a Najeriya

    Wasu matasa a ƙarƙashin ƙungiyar Take It Back Movement sun fara gudanar da zanga-zanga a wasu a jihohin Najeriya da babban birnin tarayya Abuja.

    Cikin jihohin da ake gudanar da zanga-zangar yanzu haka akwai jihohin Legas da Oyo da Rivers, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Omoyele Sowore - wanda shi ne ɗantakarar jam'iyyar AAC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 - shi ne shugaban ƙungiyar Take it Back kuma ya fito a zanga-zangar.

    Matasan sun fito zanga-zangar ce duk da shawarar da rundunar ƴansanda ta ba su cewa su dakatar da yunƙurinsu saboda ranar ta dace da ranar 'yansanda ta ƙasa.

    Rahotanni na cewa matasan sun fito a ƙarƙashin gadar Ikeja da ke Legas, inda suka ratsa unguwannin birnin jihar suna raira waƙoƙi.

    Rahotanni daga Fatakwal sun ce ƴansanda na harba hayaƙi mai sa hawaye tare da tarwatsa masu zanga-zangar.

  17. Zimbabwe za ta soke haraji kan kayayyakin Amurka

    Shugaban ƙasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya sanar da cewa zai dakatar da haraji kan kayayyakin da ake shiga ƙasar da su daga Amurka domin "gyara alaƙa" da gwamnatin Donald Trump.

    Wannan matakin na Zimbabwe na zuwa na kwanaki kaɗan bayan Trump ya ƙaƙaba harajin kashi 18 na kayayyakin da ake shiga da su Amurka daga Zimbabwe.

    "Mun ɗauki wannan matakin ne domin faɗaɗa cinikayyar kayayyakin da ake shigo da su Zimbabwe daga Amurka, sannan mu ƙara samar da dama domin shigar da kayayyakin Zimbabwe zuwa Amurka," kamar yadda Mnangagwa ya bayyana a shafinsa na X.

    Zimbabwe ba ta cika ga maciji da Amurka ba, tun a lokacin da ƙasar ta ɗabbaƙa dokar mallakar ƙasa kimanin shekara 25, da kuma batun zargn ƙasar da tauye haƙƙin ɗan'adam.

    Cinikayya tsakanin ƙasashen biyu ya kai dala miliyan 111.6 a 2024, kamar yadda alƙaluman gwamnatin Amurka suka nuna.

  18. Jihohi 23 ke fama da cutar sanƙarau a Najeriya - NCDC

    Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya wato NCDC, ta bayyana cewa jihohi 23 ne ke fama da cutar sanƙarau a ƙasar.

    Hukumar ta ƙara da cewa aƙalla mutum 315 ne suka kamu da cutar a jihohin Kebbi da Sokoto da Katsina, waɗanda kuma su ne sahun gaba a jerin jihohin da ke fama da wannan cuta.

    Gwamnatocin jihohin dai sun bayyana ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar a wasu matakai da suka ɗauka a jihohin nasu.

  19. Ƙungiyar tuntuɓa ta arewa ta buƙaci a biya diyyar waɗanda aka kashe a Filato

    Ƙungiyar tuntuɓa ta arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana rashin jin daɗinta kan hare-haren da ke faruwa a jihar Filato ta arewacin Najeriya, inda a kwanakin baya aka kashe mutane da dama, ciki har da ƙananan yara da mata.

    A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na ƙungiyar, Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta-ɓaci a yankunan da ke fama da hare-haren na ƴanbindiga.

    "A bayyana yake mutanen jihar na cikin tsananin tashin hankali, wanda kuma ya zo a daidai lokacin da rayuwa ta yi tsada. Dole ne a kawo ƙarshen kashe-kashen nan, sannan dole a tabbatar an dawo da zaman lafiya a jihar," in ji ƙungiyar, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Ƙungiyar ta kuma yi kira da a ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri, sannan a ƙara ƙarfafa jami'an tsaro wajen bibiya tare da kama masu laifi, "sannan su yi bincike domin a hukunta waɗanda aka samu da laifi."

    Haka kuma ACF ta buƙaci a tabbatar da biyan diyya ga wadanda suka rasa ƴanuwansu, sannan a tallafa wa waɗanda suka jikkata.

    A ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi su ƙarfafa malaman addini da masu riƙe da sarautun gargajiya da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki domin taimakawa wajen sulhunta ɓangarori.

  20. Japan za ta taimakawa kamfanonin da harajin Amurka ya shafa

    Firaministan Japan, ya ce gwamnatinsa za ta tallafa wa kamfanonin da sabon harajin Amurka ya shafa tare da ɗaukar matakai na daƙile rasa ayyukan yi.

    Japan na ɗaya daga cikin manyan masu shigar da kayayyaki zuwa Amurka, kuma Firaministan ya ce yana ci gaba da neman sassauci daga Washington.

    Ministan kuɗi na Koriya ta Kudu ya ce yana shirin ɗaukar matakai na tallafi ga ɓangarorin tattalin arzikin da suka fi fuskantar hatsari daga harajin na Amurka.