Hezbollah ta rasa wasu sansanoninta bayan yaƙi ya karya logon ƙungiyar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 9

A bara, ranar 17 ga watan Satumba da misalin karfe 3:30 wani ma'aikacin lafiya mai suna Adam ya ce ya samu sako a na'urar shi ta sadarwa a lokacin da ya zo aiki a wani asibiti da ke Lebanon.

Hezbollah ce ta raba abubuwan sadarwan ga dubban mambobinta, ciki har da Adam, inda ya ce ta nan ne suke samun bayani kan abubuwa na gaggawa ko bala'i idan za su faru.

"Na'urar ta fara kaɗawa ba ƙaƙƙautawa, kuma a allonta an rubuta "gaggawa", in ji Adam, wanda ba ya so ya yi amfani da sunanshi na asali saboda dalilai na tsaro.

Shugaban ƙungiyar ta Hezbollah ne ya tura sakon. Kawai ina zaune sai na ji na'urar ta fashe.

Adam ya nuna min bidiyon ɗakin a cikin wayarsa, wanda wani abokin aikinsa ya ɗaua mintuna kaɗan bayan samun tsira.

Jini ya yi ta kwarara a ƙasa. "Na yi ƙoƙarin birgima a ƙasa har zuwa bakin kofa saboda na kulleta lokaci da nake sauta tufafina," in ji shi.

Fashewar ta ɓula wani wuri a kan kujerar. Na lura da wani abu a ƙasa. "Yatsa ta ce," a cewarsa.

Hezbollah dai tana da mayaƙa gwaraza, kuma ƙasashe da dama irinsu Birtaniya da Amurka sun ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci a duniya.

Amma a Lebanon, ta kasance babbar ƙungiyar siyasa wadda take da wakilai a majalisar ƙasar.

A can Lebanon, zama ɗan Hezbollah ba yana nufin mutum mayaƙi ba ne. Yawanci ma ba sa yin faɗa.

Adam ya faɗamin cewa bai taɓa yin faɗa ba. Alal misali, mutane na iya aiki a hukumomin ƙungiyar da dama da suka haɗa da asibitoci da kuma masu ayyukan gaggawa.

Hezbollah ta yanke shawarar bai wa mambobinta wasu na'urorin sadarwa na musamman maimakon irin wayoyi da aka saba gani wanda take fargabar cewa Isra'ila, babbar abokiyar gabarta, za ta yi amfani da su wajen tattara bayanan sirri a kan ƙungiyar.

Sai dai, Isra'ila ta daɗe tana tsarawa yadda za ta kutsa musu ta hanyar amfani da na'urorin:

A ce sun tsara kai hari kawai suna jiran lokaci ya yi - kuma abin da ya faru kenan a ranar da abin suka fashe.

A lokacin fashewar na'urorin, Adam mai shekara 38 ya rasa ɗan yatsunsa biyu.

Idonsa na ɓangaren dama ba ya gani, wanda aka maye masa gurbi da gilashin ido.

Ya nuna min hotonsa a kan gadon asibiti, wanda aka ɗauka jin kaɗan bayan fashewar - inda fuskarsa ta ƙone ta cika da jini, inda aka ɗaure masa da bendeji.

Duk da irin raunuka da ya ji, Adam ya ci gaba da kasancewa cikin Hezbollah. Na tambaye shi yanda ya ji idan ya kalli kansa.

"Ina cikin yanayi mai kyau" ya faɗa cikin Turanci. Ya faɗamin cikin Larabci cewa; "Saboda mun yi imanin cewa raunuka jarrabawa ce daga Allah.

Girmama abin da muke ji don yin faɗa kan gaskiya."

Sai dai ƙarfin ƙungiyar ya ɗan ragu tun bayan da Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai da kuma mamaye Lebanon, wanda ya biyo da fashewar na'urori da kuma tarin kalubale.

A can gida, akwai rashin gamsuwa tsakanin wasu magoya bayanta kan rashin kuɗaɗen sake gina wuraren da aka lalata, yayin da sabuwar gwamnati ta sha alwashin kwashe makaman da ke hannun ƙungiyar.

A Syria da ke makwabtaka, hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad ya janyo cikas a hanyar da Iran ke amfani da ita, wadda ta kasance babbar mai goya mata baya - musamman wajen samar da makamai da kuma kuɗaɗe.

Na kai ziyara wasu yankuna a kudancin Lebanon waɗanda hare-haren Isra'ila suka lalata, kuma na ga har yanzu goyon bayan Hezbollah ba ta ragu ba.

Sai dai, a ra'ayoyi da ake yi kan kafafen yaɗa labarai, wasu da ke goyon bayan ƙungiyar sun ce an yi kuskuren shiga yaƙin, kuma sun aza ayar tambaya kan makomar ƙungiyar a matsayin dakarun soji.

An kirkiro ƙungiyar Hezbollah a cikin shekarun 1980 don mayar da martani ga mamayar da Isra'ila ta yi wa Lebanon a lokacin yaƙin basasar ƙasar.

Har zuwa yau ɗaya daga cikin burinta shi ne wargaza Isra'ila.

Yaƙin da suka yi na karshe shi ne a shekarar 2006, wanda ya biyo samun kwanciyar hankali na tsawon shekaru.

Tashin hankali ya sake ɓarkewa a shekarar 2023 bayan da Hamas ta kai hari Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba, inda ta kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da sama da 250.

A lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-hare a Gaza, Hezbollah ta fara harba rokoki a ƙewayen arewacin Isra'ila, inda ta ce tana goyon bayan Falasɗinawa.

Isra'ila ta mayar da martani da hare-hare ta sama a kudancin Lebanon, kuma an tilastawa dubun dubatar mutane tserewa daga ɓangarori biyu na kan iyaka.

Fashewar na'urorin ya kasance wani sauyi a cikin rikici da aka daɗe ana yi. Na'urorin sun fashe yayin da mutane ke aiki, sayayya ko kuma ke zaune a gida.

Gomman mutane ne da suka haɗa da ƙananan yara biyu aka kashe, sannan dubbai suka jikkata, inda da dama suka nakasa.

Harin ya fusata mutane a Lebanon. Kwana guda bayan haka, ba zato ba tsammani su ma wasu na'urorin suka sake fashewa.

Na kasance a wurin jana'izar wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa.

Ƴan kungiyar Hezbollah, sun fusata - inda suka nemi mu kashe na'urori da kuma kyamarorin mu domin babu wanda ya san abin da zai iya fashewa gaba.

A cikin makonnin da suka bi baya, Isra'ila ta kai hare-haren bama-bamai ba ƙaƙƙautawa tare da mamaya ta ƙasa a kudancin Lebanon.

An kashe mutane kusan 4,000 a duk faɗin ƙasar, sannan wasu 18,000 suka jikkata.

Ga Hezbollah, rikicin ya zama bala'i. An kashe manyan shugabannin ƙungiyar da wasu mayaƙanta da dama tare da lalata yawancin makamanta.

Daga cikin waɗanda suka mutu har da Hassan Nasrallah, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana shugabancin ƙungiyar Hezbollah - an kashe shi a wani gagarumin hari ta sama da aka kai hedikwatar ƙungiyar ta sirri da ke karkashin wasu gidaje a Dahieh, inda Hezbollah ke da hedkwata a Beirut.

A karshen watan Nuwamba, bayan fafatawa ta tsawon lokaci, ƙungiyar ta amince da tsagaita wuta wanda wasu ke ganin ta miƙa wuya ne.

Kudancin Lebanon ya kasance matattarar mabiya Shi'a, wanda nan hezbollah ke da ɗimbin magoya bayan, kuma ɗaya daga cikin yankunan ƙasar da ƙungiyar ta daɗe da zama.

Na kai ziyara zuwa garin Kfar Kila da ke kan iyaka - wanda ke da al'uma 15,000 kafin a fara yaƙi. Garin ne kuma ya zama na farko da Isra'ila ta fara mamaya.

Isra'ila ta ce ta fara yaƙi da Lebanon ne don bai wa mutane da ke zaune a arewacin ƙasar damar komawa gida, waɗanda suka tsere saboda hare-haren Hezbollah.

A garin Kfar Kila, babu abin da ya rage, kuma tutocin Hezbollah ne kaɗai masu launin ruwan kwai ake gani kan gine-ginen da aka lalata.

Wata mata mai shekara 37 mai suna Alia ta je wurin ne da mijinta da kuma ƴayanta mata guda uku, ƴan shekara 18, 14 da kuma 10.

Ƙaramar cikinsu na sanye da bajo da ke ɗauke da hoton Nasrallah yana murmushi.

"Na san nan ne kaɗai gidana saboda abin da ya rage na wani shuka, da furanni da kuma wannan itaciya," Alia ta faɗa min.

Daga titin, ta nuna min wani abu da ta iya ganewa cikin ɓaraguzai. "Waɗannan su ne ragowar kujeruna. Wannan shi ne falo.

Wannan kuma ɗakin kwanciya. Wancan kuma shi ne keken ɗiyata," in ji ta. "Babu abin da rage".

An kiyasta cewa kuɗin da za a yi amfani da shi wajen sake gina wuraren da aka lalata a faɗin ƙasar zai kai dala biliyan 11, a cewar bankin duniya.

Ɗaya daga cikin kalubalen Hezbollah shi ne tallafawa waɗanda yaƙin ya shafa da kuɗi, wanda yana da muhimmanci domin ta ci gaba da samun goyon baya.

Waɗanda suka rasa gidajensu sun samu kuɗi dala 12,000 domin biyan kuɗin haya na shekara.

Sai dai ƙungiyar ba ta yi bayar da kuɗi don sake gina wuraren da aka lalata bako kuma biyan diyya ga waɗanda aka lalatawa wuraren kasuwanci.

Rashin ba da tallafin yadda ya kamata ya fara janyo fushi da ɓacin-rai.

Kayayyakin da ke shagon Alia sun kai na dala 20,000, kuma ta damu cewa babu wanda zai tallafa mata daga asarar da ta yi.

Iran da ke goyon bayan Hezbollah, na ɗaya daga cikin waɗanda ke bai wa ƙungiyar kuɗaɗe da makamai da kuma horo.

Sai dai ƙawayen Lebanon na son toshe duk wata hanya da Iran za ta bi wajen taimakawa ƙungiyar, don matsa lamba kan Hezbollah - inda suka ce babu wani taimako idan ba da taimakon gwamnatin Lebanon ɗin ba.

Karya karfin ƙungiyar da aka yi, ya sa masu suka na ganin hakan a matsayin dama ta karɓe makamai daga hannunta.

Alia ta faɗa min cewa: "Ba mu son duk wani agaji da zai zo wanda zai buƙaci mu ajiye makamanmu...

Ba za mu bari su ɗauki mutuncin mu ba ko abin alfaharin mu, su karɓe mana makamai kawai don gina mana gida. Za mu gina shi da kan mu."

Ba abin mamaki bane ganin cewa magoya bayan Hezbollah sun ci gaba da bijirewa.

Ga mutane da dama, ƙungiyar na da muhimmanci a rayuwarsu da kuma aƙidojinsu.

Amma ana gani da kuma jin ƙarfin Hezbollah a wurare da take kaɗai ba.

Kafin soma yaƙi, ana ganin ƙarfin sojojinta ya ma fi na sojojin Lebanon. Lamarin ya sa babu wani mataki da za a ɗauka ba tare da yardar Hezbollah ba.

Saboda yadda tsarin siyasar ƙasar yake, ƙungiyar na da wakilai a gwamnati.

A takaice, tana da karfin janyo tawaya a ƙasar, kuma ta yi hakan a lokuta da dama.

Sai dai yaƙin ya rage ƙimar da ƙungiyar ke da ita a cikin ƙasar.

A watan Janairu, majalisar dokokin Lebanon ta zaɓi sabon shugaba, tsohon shugaban soji Joseph Aoun, bayan zaman tankiya na shekara biyu wanda masu suka suka ɗora laifin haka kan Hezbollah.

A baya, ƴan majalisunta da ƙawayenta na fita daga zauren majalisa lokacin kaɗa kuri'a kan wani abu.

Amma Hezbollah, wanda aka yi wa rauni da kuma al'ummominta da ke buƙatar taimako, suna ganin ba za su iya hana komai ba.

A jawabin shan rantsuwa, Aoun ya yi alkawarin cewa zai saka sojojin Lebanon su kasance su kaɗai ke riƙe da makamai a ƙasar.

Bai ambaci sunan Hezbollah ba, amma kowa ya fahimci sakon.

Makomar Hezbollah ta dogara kan Iran. Ɗaya daga cikin dalilai da suka sa Iran ke goyon bayan Hezbollah a Lebanon shi ne domin daƙile duk wani hari daga Isra'ila, musamman kan makaman nukiliyarta. Wannan ya wuce yanzu.

An karya lagon wasu ƙungiyoyi da Iran ke marawa baya a yankin, ciki har da Hamas a Gaza da Ƴan Houthi a Yemen, abin da kuma take kira da ƴan gwagwarmaya.

Kuma faɗuwar gwamnatin Assad ya janyo cikas a hanyar Iran zuwa Lebanon - da kuma Hezbolah.

Ko da Iran ta yanke shawarar sake bai wa Hezbollah makamai, lamarin ba zai yi sauki ba.

Adam wanda ya jikkata a fashewar na'urori, yanzu ya koma wurin aikinsa na ma'aikacin jinya.

Yanzu ba ya aiki da daddare, watakila saboda ba ya gani sosai. Fashewar ta yi masa lahani, musamman a kansa da kirjinsa.

Yayin da yake saurin gajiya, yana buƙatar ɗaukar lokaci domin hutawa.

Lokutan yin tausa na taimaka masa wajen amfani da abin da ya rage a babban ɗan yatsarsa na hagu da yatsa na tsakiya.

Abin da ake gani kodayaushe a ɗakinsa shi ne hotonsa da ya ɗauka da hannunsa da ya samu rauni, riƙe da irin na'urar sadarwa.

Ya nuna min wani hoto na hannunsa, da ke nuna cewa ya sadaukar da abin da ya rasa ga Hassan Nasrallah, tsohon shugaban Hezbollah.

Shi, kamar sauran mutane, har yanzu suna yin imani da manufofin Hezbollah, da kuma irin rawar da take takawa.