An wanke fasto ɗan Najeriya kan zargin fyaɗe bayan shafe shekara takwas a gidan yari
An wanke wani fasto ɗan asalin Najeriya daga laifin yi wa wata matashiya fyaɗe a majami'arsa da ke Afirka ta Kudu, bayan shafe shekara takwas a gidan yari.
Timothy Omotoso ya musanta zarge-zarge 32 da aka yi masa, a wata shari'a da aka watsa kai-tsaye a gidan talabijin da kuma aka yi ta yayatawa a faɗin ƙasar
A 2018, matashiyar ta faɗa wa kotun cewa faston ya yi mata fyaɗe - wanda ke da wata majami'a a birnin Port Elizabeth - lokacin tana da shekara 14.
Lokacin yanke hukuncin ranar Laraba, alkalin da ke jagorantar shari'ar ya ce an samu mista Omotoso ba shi da laifi saboda masu gabatar da ƙara ba su gudanar da shari'ar yadda ya kamata ba.