Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza

  1. Obasanjo zai zuba jarin CFA biliyan 420 a Kamaru

    Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana shirin zuba jarin kusan CFA biliyan 420 a Kamaru.

    Wata sanarwa da kamfanin Aftel Cameroon Limited, wani reshe na Obasanjo Agro-Allied Business Ltd, ya fitar, ta tabbatar da cewa tsohon shugaban na Nijeriya zai zuba jarin ne a fannonin noma da gine-gine da kuma kasuwancin man fetur.

    Hukumar ƙididdiga ta Kamaru ta bayyana cewa a 2023 harkokin kasuwanci tsakanin Kamaru da Najeriya sun haifar wa Kamaru rarar ciniki na kusan CFA biliyan daya.

  2. Na kusa bayyana hujjojina na zargin Akpabio da cin zarafina - Natasha

    Dakatacciyar Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce ta kusa fitowa ta bayyana hujjojinta kan zargin da take yi wa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da cin zarafinta.

    Ta bayyana haka a tattaunawarta da tashar Channels, inda ta ce lokaci kawai take jira, kuma da zarar lokacin ya yi, ta fitar da hujjojin.

    "Idan lokacin da ya dace ya yi, zan fitar da hujjojina," in ji ta.

  3. Wakilin Syria a MDD ya yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila a ƙasarsa

    Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a Syria ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kai wa a ƙasar, yana mai cewa tana ƙara jefa yankin baki ɗaya cikin wani mummunan yanayi.

    Kalaman Geir Pedersen sun biyo bayan harin da Isra'ila ta kai ranar Laraba wanda ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 13.

    Isra'ila ta kai hare-hare da dama a Syrya tun bayan da ƴan tawaye suka hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamban bara.

    Haka kuma ta bayyana sabbin masu mulkin ƙasar a matsayin barazana ga tsaron Isra'ila.

  4. Hukumar kashe gobara ta tabbatar da ƙonewar ofisoshi a jami'ar North West ta Kano

    Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da ƙonewar wasu ofisoshi a jami'ar North West da ke jihar Kano.

    An dai ga wani faifan bidiyo yana kara-kaina a kafofin sadarwa, wanda yake nuna wuta tana tashi a benen mai hawa tara.

    A wata sanarwa da kakakin hukumar, SFS Kabiru Isah Jafar ya fitar, ya ce sun samu kiran kar-ta-kwana ne daga wani mai suna Mannir Abdullahi, wanda ya bayyana musu labarin gobarar.

    "Jami'anmu sun isa wurin, wanda bene ne mai hawa tara. Wasu ofisoshi ne da wasu sassa na benen suka kama da wuta, amma babu wanda ya rasa rai," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa sun samu nasarar ciro kayayyakin dubban kuɗi.

  5. Masu yaɗa cewa na yanke jiki na faɗi ƙarya suke yi - Wike

    Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya yanke jiki ya faɗi, har an fitar da shi asibiti a ƙasar waje, inda ya ce labari ne ƙirƙirarre.

    Wike ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Alhamis a lokacin da ya je ziyarar duba wani aiki wanda za a ƙaddamar a watan gobe domin bikin cikar Shugaba Bola Tinubu shekara biyu a mulki.

    A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Anthony Ogunleye ya fitar, Wike ya ce maƙiyansa na siyasa ne suka ƙirƙiri maganar domin su kawar da hankalin mutane.

    "Abin da yake faruwa shi ne saboda tsohon shugaban ma'aikatan jihar Rivers ya fito ya bayyana gaskiyar abin da ya faru na yunƙurin saka bam a majalisar dokokin jihar da ma yunƙurin kai hari a kan kadarorin gwamnati, shi ne domin su kawar da hankalin mutane daga maganar, sai suka ƙirƙiri wannan labarin. Babu inda na yanke jiki na faɗi ballantana ma a garzaya da ni ƙasar waje."

    Wike ya ce ko ranar da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi buɗa-baki kan zagayowar haihuwarsa ya je, "ranar Sallah kuma na jagoranci mazauna Abuja domin zuwa taya shugaban ƙasar barka da sallah. Amma irin maganganun na siyasa ba sa damuna, kuma ba za su kawar mana da hankalinmu ba," in ji shi.

  6. Mahara sun kashe mutum 10 a jihar Filato

    Aƙalla mutum 10 ne wasu mahara suka kashe a daren jiya Laraba a garuruwa biyar da suka kai hari a ƙaramar Bokkos da ke jihar Filato.

    Harin ya zo ne kwana ɗaya bayan an kai wani harin a garin Ruwi, inda aka kashe wasu mutum 10, sannan aka jikkata wasu da dama a lokacin da suke gudanar da bikin binne wata dattijuwarsu da ta rasu, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ci gaban al'aduna Bokkos, wadda shugabanta, Farmasum Fuddang ya sanya wa hannu ta fitar, ta ce mutane yankin waɗanda masu son zaman lafiya ne, "suna fuskantar barazana daga masu yunƙurin ƙwace musu ƙasa."

    "A mako ɗaya kawai an kashe mana sama da mutum 20," in ji sanarwar.

  7. Shugaban sojin Myanmar ya je taron tattalin arziki a Thailand

    Shugaban gwamnatin mulkin sojan Myanmar, Janar Min Aung Hlaing, ya isa ƙasar Thailand domin halartar wani taron tattalin arziki - ƙasa da mako guda bayan da ƙasarsa ta fuskanci mummunar girgizar ƙasa.

    Masu suka daga cikin Myanmar da ƙasashen waje sun ce ya kamata ya zauna a gida don taimakawa wajen sanya ido kan ayyukan agaji.

    Suna kuma ganin cewa gayyatar tasa ta halasta juyin mulkin da sojoji suka yi a Myanmar.

    (Wakilin BBC ya ce A farkon makon nan ne wata ƙungiyar ma'aikata ƴan ci-rani ƴan ƙasar Myanmar a Bangkok ta miƙa koke ga Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ta buƙaci kada ya zo ƙasar ta Thailand).

    Ana tunanin Janar ɗin zai iya neman ƙarin taimako don tunkarar bala'in girgizar kasar.

  8. Turji ya kusa komawa ga Allah - Hedkwatar tsaron Najeriya

    Hdkwatar tsaron Najeriya ta ce ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema ruwa a jallo ya kusa komawa ga Allah.

    Rundunar ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, inda rundunar ta ce tana cigaba da farautarsa, kuma kwanakinsa sun kusa ƙarewa.

    Wannan albishirin na sojojin na zuwa ne kimanin kwana ɗaya bayan Turji kashe mutum 11 a garin Lugu da ke ƙaramar Isa ta jihar Sokoto.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito daraktan watsa labaran na rundunar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Markus Kangye yana cewa za su cigaba da farauta tare da ganin bayan fitattun ƴanbindiga da suke cikin dazukan ƙasar.

    Haka kuma hafsan sojan ya musanta zargin yin watsi da sojojin ƙasar da suka ji rauni a fagen daga, inda ya ce suna iya ƙoƙarinsu domin kula da su, da ma jin daɗi da walwalarsu.

  9. Kashim Shettima ya tafi Senegal

    Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya tafi birnin Dakar na Senegal domin bikin cika shekara 65 da samun 'yancin ƙasar.

    Shi ne zai wakilci Shugaba Bola Tinubu yayin bikin 'yancin ƙasar, wadda ƙawar Najeriya ce a ƙungiyar Ecowas mai raya tattalin arziki ƙsashen Afirka ta Yamma.

    Senegal kan yi bikin ranar 'yanci daga Faransa duk 4 ga watan Afrilu, kuma za a yi bikin na bana ne a fadar Place de la Nation da ke Dakar.

    Ana sa ran Shettima zai koma gida bayan kammala bikin na kwana ɗaya.

  10. Shugaban Uganda ya isa Sudan ta Kudu kan fargabar ɓarkewar yaƙi

    Shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni ya isa Sudan ta Kudu inda ake fargabar sake ɓarkewar yaƙin basasa.

    Uganda ta tura dakaru domin mara wa shugaba Salva Kiir baya, bayan wani hari da wasu ƴan bindiga suka kai wa sojojin ƙasar wanda gwamnati ta ce suna biyayya ne ga mataimakin shugaban ƙasar Riek Machar.

    A makon da ya gabata ne dai gwamnatin ƙasar ta fara yi wa Mista Machar ɗaurin talala.

    A shekara ta 2018 ne Salva Kiir da Riek Machar suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya don kawo karshen yaƙin basasar shekara biyar wanda ya ɗaiɗaita kusan kashi ɗaya cikin uku na al'ummar ƙasar.

    A ranar Laraba ne masu shiga tsakani na ƙungiyar Tarayyar Afirka suka isa Juba babban birnin ƙasar.

  11. Gwamnan Legas ya bai wa mazauna birnin haƙuri kan cunkuson ababen hawa da aka samu

    Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bai wa mazauna birnin haƙuri kan cunkuson ababen hawa da aka samu sakamakon aikin gyaran babbar gadar 'Independence Bridge' da ke tsakiyar birnin.

    Cikin wata ziyara da da ya kai wurin aikin da safiyar ranar Alhamis, Gwamnan Babajide Sanwo-Olu ya bai wa ak'ummar birnin haƙuri kan cunkuson da aikin ya janyo musu, yana mai cewa za a gaggauta kammala aikin domin sauƙaka wa mazauna birnin.

    A ranar Laraba ne dai aka rife gadar domin aiin gyara ta, lamarin da haifar cunkoson ababen hawa a yankin, tun daga ranar Larabar zuwa yau Alhamis da safe.

    Hotuna da bidiyon da aka ya da a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mautane suka maƙale ciin cunkuson ababen hawa tare da nuna ɓacin ransu.

  12. Jamb ta sanar da ranar fara jarrabawar wannan shekara

    Hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'i ta Najeriya Jamb ta sanar da ranar 25 ga watan Afrilun da muke ciki a matsayin ranar fara jarrabawar wannan shekara ta 2025.

    Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya fitar, ya ce za a fara jarrabawar Jamb ta gwaji (Jamb-Mock) a ranar 10 ga watan na Afrilu.

    Hukumar ta kuma buƙaci masu rubuta jarrabawar su fitar da katunan jarrabawar da ake kira 'Exam Slip' - waɗanda suka ƙunshi cikakkun bayanan ranar da mutum zai yi jarrabawar da lokaci da kuma wurin da zai yi ta.

    ''Ana buƙatar masu rubuta jarrabawar su fara fitar da katunan tun daga ranar 3 ga watan Afrilu, domin samun isasshen lokacin shirya wa jarrabawar'', in ji sanarwar.

  13. Ɗan wasan Arsenal Gabriel zai yi jinya zuwa karshen kaka

    Ɗan wasan baya na ƙungiyar Arsenal Gabriel Magalhaes zai yi jinya zuwa karshen kakar wasanni ta bana, bayan samun rauni a cinyarsa.

    An sauya ɗan wasan ɗan asalin Brazil a wasan da Arsenal ta doke Fulham da 2-1 a gasar Premier ranar Talata a Emirates.

    Toshon ɗan wasan na Lille ya buga wasanni 28 cikin 30 na gasar Premier ta bana, inda Arsenal ɗin ta zama wadda ba a ci kwallo da yawa ba a bana - inda aka ci ta kwallo 25 kaɗai a gasar.

    "Za a yi wa Gabi tiyata a cinyarsa a cikin kwanaki masu zuwa, kuma nan da zai fara karɓar horo na musamman don ƙoƙarin dawowa a farkon kakar wasa ta baɗi," in ji sanarwar da Arsenal ta fitar.

    Ƙungiyar tana mataki na biyu a teburin gasar Premier, maki 12 a bayan Liverpool - inda ya rage wasanni takwas a kammala kakar bana.

    Gunners ɗin na shirin tunƙarar Real Madrid a matakin quarter-finals na gasar zakarun Turai.

  14. Labarin matashin da ya tsallake rijiya da baya da iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi

  15. Ƙudirin yi wa Sanata Natasha kiranye bai cika ƙa'ida ba - INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ce ƙudirin da wasu al'ummar mazaɓar sanatan Kogi ta tsakiya suka gabatar mata bai cika ƙa'ida ba.

    A makon da ya gabata ne al'ummar mazaɓar suka gabatar da ƙorafinsu zuwa hukumar INEC, inda suka buƙaci yi wa sanatan kogi ta tsakiya Sanata Natasha Akpoti-Uguaghan kiranye daga majalisar dattawan ƙasar.

    To sai dai cikin wata sanar da hukumar ta wallafa a shafita na X, ta ce ƙorafin al'ummar mazaɓar bai cika sharadi ba.

    Hukumar ta kuma yi alƙawarin bayar da cikakkun bayanai a nan gaba

    A watan da ya gabata ne dai Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da sanata Natasha kan zargin yunƙurin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio.

  16. Shugaban Myanmar ya isa Bangkok yayin da girgizar ƙasa ta kashe mutum 3,000

    Shugaban gwamnatin mulkin sojin Myanmar, Min Aung Hlaing na halartar wani taron yanki a ƙasar Thailand yayin da ƙasarsa ta fuskanci mummunar girgizar ƙasa da ta kashe dubban mutane tare da lalata birane masu yawa.

    Mummunar girgizar ƙasar da ta auku a ƙasar cikin makon da ya gabata ta kashe mutum 3,085 tare da raunata 4,715, yayin da ɗaruruwan mutane suka ɓace, a cewar gwamnatin mulkin sojin.

    Da dama daga cikin wuraren da aka samu girgizar ƙasar ba a samu isa gare su ba, wani abu da hukumomi ke fargabar samun ƙaruwar mace-mace.

    Kafanin diallancin labarai na AFP ya ce Min Aung Hlaing ya isa Bangkok a yau Alhamis gabanin fara taron shugabannin ƙasashen da suka yi iyaka da gabar Bangal a tekun Atalantika.

    Halartarsa taron wani abu ne da ba a saba gani ba, kasancewar ana haramta wa shugabannin da aka sanya wa takunkumi halartar irin wannan taro.

  17. Sojojin Isra'ila sun ce za su yi bincike kan kisan ma'aikatan agaji

    Sojojin Isra'ila sun ce suna binciken kisan da aka yi wa wasu ma'aikatan agaji 15 da na aikin ceto a kudancin Gaza a watan da ya gataba.

    IDF ya ce motocin mutanen sun tunkari inda sojojinsu suke a Rafah, ba tare da alamar da ke nuna cewa na ma'akatan agaji ba ne, kuma sun ce an samu wani ɗan Hamas a cikin waɗanda aka kashe.

    Ƙungiyar bayar da agaji da Falasɗinawata ce babu mayaƙan ƙungiyar cikin waɗanda ke cikin ayarin motocin, sannan ta ce motcin na ɗauke da wutar danja da ke nuna alamun na daukar marasa lafiya ne, kuma akwai rubutu ƙarara a jikinsu.

  18. Ministocin harkokin wajen Sahel na ziyara a Rasha

    Ministocin harkokin wajen ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar na kan hanyarsu ta zuwa Rasha domin ziyarar aiki ta kwana biyu.

    Ministocin na ziyarar ne ƙarƙashin inuwar sabuwar ƙungiyar ƙawancen ƙasashen yankin Sahel (AES) - wadda suka kafa bayan ɓallewa daga Ecowas.

    Ziyarar na zuwa ne bayan samun gayyatar ministan harkokin waje na Rasha, Sergei Lavrov.

    Cikin wata sanarwa da ministan ya fitar ya ce ''ganawar wadda za a yi birnin Moscow wani muhimmin mataki ne na sake gina cikakkiyar alaƙar da hadin kai tsakanin AES da Rasha''.

    A farkon makon nan ne Lavrov ya ce Rasha za ta buɗe ƙarin ofisoshin jakadancinta a Nijar da Togo da Gambiya da kuma Laberiya nan da 2026.

  19. Hungary za ta janye daga kotun ICC

    Gwamnatin Hungary ta sanar da cewa za ta janye daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC).

    Wani babban jami'i a gwamnatin Firaiminsta Viktor Orban, Gergely Gulyas, ne ya sanar da matakin - sa'o'i kaɗan bayan da Firaimista Benjamin Netanyahu wanda kotun ke neman kamawa ya isa ƙasar a wata ziyara.

    Orban ya gayyaci Netanyahu ne bayan da kotun ta bayar da sammacin kama shi tun watan Nuwamban 2024, inda ya ce matakin ba shi da wani tasiri a ƙasarsa.

    A watan Nuwamban shekara da ta gabata ne lauyoyin ICC suka ce "akwai ƙwararan hujjoji" kan zargin da ake yi wa Netanyahu na aikata laifukan yaƙi da take ƴancin ɗan'adam a yaƙin Isra'ila da Hamas.

    Sai dai Netanyahu ya yi Alla-wadai da matakin kotun, wanda ke da mambobi 125 daga ƙasashe.

  20. Jerin ƙasashen duniya da Trump ya lafta wa haraji

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ƙarin sabon haraji ga ƙasashen duniya a ranar Laraba bisa dalilin cewa hakan zai bai wa Amurka damar bunƙasa tattalin arziƙinta.

    Sabon harajin da Trump ɗin ya sanar bisa dogaro da wani umarnin shugaban ƙasa ka iya jefa matsalar tattalin arziƙi a faɗin duniya.

    To amma shi shugaban na Amurka ya yi amannar cewa lafta harajin ya zama dole domin cimma daidaito ta harkar kasuwanci tsakanin Amurkar da sauran ƙasashen duniya da kuma kare ayyukan yi da masana'antu na ƙasar tasa.