Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/06/2025

Taƙaitattu

  • MDD ta soma taron gaggawa kan rikicin Isra'ila da Iran
  • Rukunin farko na sojojin Afirka ta Kudu sun dawo gida daga Kongo
  • Iran ta harba makamai masu linzami tsakiyar birnin Tel Aviv
  • Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta - Ayatollah
  • 'An samu raguwar shigar da man fetur Najeriya saboda ƙaruwar aikin matatun ƙasar'
  • 'Ban san yadda na tsira daga hatsarin jirgin da ya kashe fasinjoji fiye da 241 ba'
  • Manyan Jami'an Iran biyar da suka mutu a hare-haren Isra'ila
  • Babu hannun Amurka a harin da Isra'ila ta kai wa Iran - Trump
  • Mali ta amince da ƙudurin ƙara wa mulkin soji shekaru biyar
  • Ta yaya za a kwatanta ƙarfin sojin Iran da na Isra'ila?
  • Isra'ila ta kai wa Iran jerin hare-hare da kashe manyan kwamandojinta

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida, Aisha Ja'afar da Usman Minjibir

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu dawo domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan, muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Kotu ta ɗaure ɓarayin masai na zinare a Birtaniya

    An yanke wa wasu maza biyu hukuncin zaman gidan yari a Birtaniya bayan sun saci wani masai na zinare da ya kai darajar dala miliyan 6.

    Masan wanda ke aiki, ya na ajiye ne a ɗaya daga cikin manyan wuraren da ake bajakolin kayyakin tarihi a Birtaniya.

    A ranar da suka yi satar, ɓarayin sun zo da safiya inda suka yi amfani da motocin sata wajen rusa kofofin katako, sannan suka yi amfani da guduma wajen shiga fadar Blenheim da ke kudancin Ingila, kafin su ɓamɓaro masan daga bango.

    Tun daga nan ba a sake ganin masan ba.

    Alƙalin ya bayyana ɓacewar masan a matsayin ''satar ƙarfin zuciya''

  3. Sojojin Isra'ila sun ce Iran ta harbo makamai masu linzami aƙalla 100

    Mai magana da yawun rudunar sojin Isra'ila IDF, Avichay Adraee ya ce Iran ta harba aƙalla makamai masu linzami 100 a karo biyu zuwa Isra'ila.

    A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce an kakkaɓo akasarin makaman, yayin da wasu kuma ba su kai inda aka so su kai ba.

    Hukumomi a fannin kiwon lafiya na Isra'ila sun ce mutane 40 ne harin ya shafa wanda a yanzu suke karɓar kulawa a asibitoci daban daban, kuma biyu daga ciki na cikin mawuyacin hali.

  4. Sojojin Amurka sun taimaka wajen kakkaɓo makamai masu linzami da aka harba Isra'ila -Rahotanni

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wasu jami'an Amurka biyu sun ce sojojin Amurka sun taimaka wajen kakkaɓo wasu makamai masu linzami na Iran da ta harba Isra'ila.

    Tun da farko Shugaban ƙasar Donald Trump ya umarci ƙasar Iran da ta koma kan teburin yarjejeniyar makamin nukiliya da take yi da Amurka.

    Trump ya kuma bayyana harin da Isra'ila ta kai wa Iran a matsayin kyakkyawa, har ma ya yi gargaɗi da cewa Isra'ilar na shirin karin wasu munanan hare-haren ma.

    Ya bukaci Iran da ta hanzarta cimma matsaya a kan shirinta na nukiliya domin dakatar da ci gaban rikicin.

  5. Rukunin farko na sojojin Afirka ta Kudu sun dawo gida daga Kongo

    Rukunin farko na sojojin Afirka ta Kudu waɗanda aka aika Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo sun dawo gida.

    Dawowan sojojin su aƙalla 250 shi ne matakin farko na janyewarsu bakiɗaya da za a yi a mataki mataki.

    Sojojin na cikin dakarun haɗin gwiwa na ƙawancen ƙasashen Kudancin Afirka (SADC) da aka aika domin taimakawa sojojin Kongo.

    An kai wa sojojin haɗin gwiwar hari a watan Janairu a lokacin da mayaƙan M23 masu samun goyon bayan Rwanda ke kusantowa.

    An kashe sojoji 20 lokacin harin, 14 daga cikisu ƴan Afirka ta Kudu ne, wanda ya kai ga matakin janyesu daga kudancin Kongo.

  6. MDD ta soma taron gaggawa kan rikicin Isra'ila da Iran

    Kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya ya soma taron gaggawa a birnin Newyork domin tattauna rikicin Isra'ila da Iran.

    Hakan ya biyo buƙatar da wasu ƴan Iran suka miƙa cikin wani saƙon gaggawa suna Allah-wadai da abin da suka kira hare-haren da ba halastacce ba kuma na ganganci kan cibiyoyita na nukiliya.

  7. Hotunan birnin Tel Aviv na Isra'ila bayan harin makami mai linzami daga Iran

  8. Iran ta kakkaɓo jiragen yaƙin Isra'ila biyu - Kafar yaɗa labaran Iran

    Kafar yaɗa labarai ta Iran ta ce dakarun juyin juya hali na ƙasar Iram sun kakkaɓo aƙalla jiragen yaƙin Isra'ila guda biyu daga sararin samaniyar ƙasar - sai dai zuwa yanzu BBC ba ta tabbatar da hakan ba.

    Yanayin da ake ciki na ƙara kazancewa cikin sauri.

    Aƙalla sa'a ɗaya ta ce wuce ne Iran ɗin ta harba makamai masu linzami birnin Tel Aviv da ke Israila a matsayin ramuwar gayya wanda rahotanni ke cewa ya jikkata da dama.

    A daren jiya ne dai Israilar ta kai hare hare kan cibiyoyin nukiliya na Iran,tare da lalata tashoshin jirgin sama, da cibiyar ayyukan inganta sinadarin Uranium, hare-haren da rahotanni ke cewa sun hallaka aƙalla mutane 78 tare da jikkata fiye da 300.

  9. An kunna garkuwar kare sararin samaniya a Tehran

    Kafar yaɗa labaran Iran ta ce an kunna garkuwar kare sararin samaniya a wasu sassan Tehran.

    Wasu bidiyo da wasu kafafen Iran suka wallafa na nuna haske a sararin samaniya, wasu rahotannin na cewa a birnin ƙasar ne.

    Rahotanni na kuma cewa sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare Iran.

  10. Iran ta harba makamai masu linzami tsakiyar birnin Tel Aviv

    Sojojin Isra'ila sun ce Iran ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami ɗazu-ɗazu kuma garkuwar sararin samaniyyar ƙasar na shirin cafke su.

    Sai dai kuma hayaƙi ya turnuƙe a tsakiyar birnin duk da cewa babu bayani dangane da wurin da makaman suka afkawa.

    Tuni aka umarci ƴan ƙasar da su nemi mafaka su kuma jira umarni a nan gaba.

    Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei dai ya yi gargaɗin cewa Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta.

  11. Kafar yaɗa labaran Iran ta ce an kai hari kan cibiyar nukiliya da ke Kudancin Tehran

    Kamfanin dillanci labarai na Fars mai alaƙa da rundunar sojojin juyin juya hali (IRGC) ya ruwaito cewa an jiyo fashewar wasu abubuwa kusa da cibiyar nulkiliya ta Fordow.

    Fordow na kudancin Tehran, kuma yana da nisan kilomita 32 a arewa maso gabashin birnin Qom, kuma yana da nisan mita 100 a ƙarƙashin ƙasa.

    A baya Amurka da ma wasu manyan ƙasashen Turai sun yi gargaɗi kan gano ɓurɓushin sinadarin Uranium da kyan shi ya kai kashi 83.7 a wurin.

    A daren jiya ne Isra'ila ta kai hari kan cibiyar nukiliyar Iran da ke Natanz a lardin Isfahan.

  12. Sauyin yanayi ne ya janyo ambaliya a Afirka ta Kudu - Ramaphosa

    Shugaban Afirka ta Kudu ya ce sauyin yanayi ne ya janyo ambaliyar da ta kashe aƙalla mutane 78 a ƙasar.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ziyarci mutanen da suka tsira daga abin da ya kira mummunan iftila'i a lardin Eastern Cape.

    Dubban gidaje da tituna da makarantu da cibiyoyin lafiya na cike da taɓo bayan ambaliyar da ta shanye su ta ja baya.

    Masu aikin ceto na ta bi gida gida suna neman gawarwaki ko kuma waɗanda suka tsira saboda mutane da dama sun maƙale a gidajensu bayan ruwa ya shiga gidajen cikin dare.

    Mista Ramaphosa ya kuma ziyarci wurin da ruwa ya tafi da wata motar safa ɗauke da yaran makaranta wanda yayi sanadiyyar mutuwar yara shida da manya uku, kuma ana ci gaba da neman yara huɗu.

  13. MDD ta yi gargaɗi kan katse hanyoyin sadarwa a Gaza

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce katse hanyoyin sadarwa da aka yi a Gaza na ci gaba da gurgunta ayyukan jin-kai.

    Mataimakin kakakin majalisar, Farhan Haq, shi ne ya bayyana haka, yana mai cewa matsalar ta kassara hanyoyin samun muhimman bayanai na gudanar da ayyuka masu matukar muhimmanci ga ceton jama'ar da ke halin kaka-ni-ka-yi.

    Hukumomin Falasdinu sun zargi Isra'ila da katse hanyoyin sadarwar da gangan.

    Sai dai wasu mutanen da ke da wayoyi masu layin waya ko sim na tafi-da-gidanka na iya sadarwa kadan-kadan ta intanet

  14. 'Isra'ila za ta fuskanci "mummunan sakamakon" abin da ta aikata mana'

    Sabon shugaban rundunar dakarun juyin-juya hali na ƙasar Iran, Muhammad Pakpour ya ce Isra'ila "za ta ɗandana kuɗarta".

    Muhammad wanda ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya saki bayan naɗa shi sakamakon kashe mutumin da ya gada ya ce lallai Isra'ila za ta ga mummunan sakamakon abin da ta aikata wa Iran.

    Sanarwar ta ƙara da cewa Iran za ta "ɗauki fansar" mutanen da aka kashe mata a harin inda ya ci gaba da cewa "Isra'ila ta keta ƴancin da tsaron Iran na ƙasa mai cin gashin kanta.

    Aƙalla masana kimiyyar nukiliya shida ne hare-haren na Iran suka kashe.

  15. An gano na'urorin bidiyo na jirgin Indiya da ya yi hatsari

    Masu bincike sun gano daya daga cikin na'urorin nadar hotunan bidiyo na jirgin Indiyan nan da ya yi hadari a jiya Alhamis jim kadan bayan tashinsa daga garin Ahmedebad, na kasar.

    Haka kuma an ce an gano daya daga cikin na'urori biyu na nadar bayanan jirgin, inda ake sa ran ta nan za a gano sanadin faduwar jirgin, kirar Boeing 787, Dreamliner, wanda ya rikito kasa, dakika talatin bayan tashinsa.

    Wakiliyar BBC ta ce Firaminista Nerandra Modi ya ziyarci Ahmed... a yau kuma ya ziyarci wasu daga cikin wadanda suka ji rauni da kuma mutum daya cikin mutanen cikin jirgin da ya tsira a hadarin.

    Dukkanin mutanen cikin jirgin 242, in banda fasinja daya babu wanda ya tsira da ransa.

    Akwai kuma wasu mutanen akalla takwas da ke kasa inda jirgin ya fado - hudu daga cikinsu daliban likitanci ne da jirgin ya hallaka.

  16. Farashin man fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra'ila a Iran

    Farashin man fetur ya yi tashin gwauron-zabi a duniya bayan harin da Isra'ila ta kai wa Iran.

    Masu zuba jari na fargabar cewa fadadar rikicin ka iya gurgunta samar da man daga yankin Gabas ta tsakiya.

    Kusan kashi ana safarar kashi daya bisa biyar na man da ake samarwa a duniya ta mashigar Hormuz - wata zirin hanyar teku, da ke kusa da iyakar Iran.

    Sai dai kuma sabanin tashin farashin darajar hannun jari a kasuwannin duniya ta yi kasa a sakamakon harin na Isra'ila a kan Iran.

    Dalilin hakan kuwa shi ne masu zuba jari ba sa son yanayi na rashin tabbas.

    To amma kuma darajar hajojin da ake yi wa ganin ba-gara-ba-zago kamar zinare da kudin Japan - Yen - darajarsu ta yi sama.

  17. Trump ya ce Iran tana da "dama ta biyu" kan yarjejeniya kan makamin nukiliya

    Donald Trump ya umarci ƙasar Iran da ta koma kan yarjejeniyar makamin nukiliya da suke yi da Amurka.

    Trump ya rubuta a shafinsa na Telegram cewa Iran "na da ƙarin lokaci" wajen cimma yarjejeniyar ta nukiliya.

    "Watanni biyu da suka wuce, na bai wa Iran wa'adin kwana 61 da ta "cimma yarjejeniyar". Ya kamata su yi hakan tuntuni. Yau kwana 61. Na faɗa musu abun da za su yi, amma suka kasa. To amma yanzu suna da dama a karo na biyu." In ji Trump

    Tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan nukiliya na shirin shiga karo na shida a ranar Lahadi a Oman. Sai dai kuma ana ganin tattaunawar za ta yi wuya domin Iran ta zargi Amurka da goyon bayan Isra'ila dangane da hare-haren da ta kai mata.

    Da ma dai Trump ya bayyana harin da Isra'ila ta kai wa Iran a matsayin kyakkyawa, har ma ya yi gargadi da cewa Isra'ilar na shirin karin wasu munanan hare-haren ma.

    Trump ya bukaci Iran da ta hanzarta cimma matsaya a kan shirinta na nukiliya domin dakatar da ci gaban rikicin.

    To amma a nata bangaren Iran ta bayyana hare-haren na Isra'ila a matsayin ayyana yaki.

    Haka kuma can a Lebanon kungiyar Hezobolla, ta yi gargadin cewa harin a kan Iran - babbar mai taimaka mata - na barazanar tayar da zaune tsaye a dukkanin yankin.

  18. Gidan talbijin na Iran ya ce mutum 78 hare-haren Isra'ila suka kashe

    Gidan talbijin ɗin ƙasar Iran, Nour News ya ce aƙalla mutum 78 ne suka mutu sannan ƙarin 329 ne suka jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila a wasu yankunan birnin Tehran da dare.

    Sai dai kuma kafar a shafinta na Telegram ta ce alƙaluman ba na hukuma ba ne.

    "Ba mu tantance waɗannan alƙaluma ba. Za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu."

    A wani ɓangare kuma rundunar sojin Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Iran - inda ta ƙara harar babbar cibiyar ayyukan inganta sinadarin Uranium din Iran din da ke Natanz, tare kuma da lalata filin jirgin saman Tabriz.

    Wakilin BBC ya ce manyan hare-haren na Israila na nuna manufa uku - lalata shirin nukiliya na Iran da kassara karfinta na kariya da kuma kashe masana kimiyyarta.

    Tun da farko Isra'ilar ta hallaka shugabannin sojojin Iran da dama, inda ta kashe shugabannin rundunonin sojin kasar, da kuma babban jagoron sojojin juyin-juya-hali, da sauran manyan kwamandoji.

    Isra'ila ta kai hare-haren a akalla birane shida, ciki har da yankunan da jama'a ke zaune a babban birnin ƙasar Tehran.

    Iran ta mayar da martani da harba sama da jirage marassa matuka dari daya a kan Israila.

    Israila wadda ke rufe ofisosin jakadancinta - na dan wani lokaci - a ƙasashen duniya ta ce ta kai harin ne domin tabbatar da wanzuwarta.

  19. Ma'aikatan jinya da Ungozoma a Ghana sun janye yajin aiki

    Ƙungiyar ma'aikatan Jinya da Ungozoma a Ghana (GRNMA) ta janye yajin aikin da ta shiga, bayan ta gana da kwamitin lafiya na majalisar dokoki.

    Shugabar ƙungiyar Perpetual Ofori-Ampofo wadda ta sanar da janye yajin aikin, ta yi kira ga gwamnati ta mutunta aikin ma'aikatan jinya kuma ta biya musu buƙatun su cikin gaggawa.

    Ma'aikatan lafiyan sun tsuduma yajin aiki ne sakamakon abin da suka bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar inganta yanayin aikinsu wadda suka cimma da gwamnatin baya.

    Gwamnatin mai ci a yanzu ta amince da aiwatar da yarjejeniyar a shekarar 2026 saboda a cewar ta kuɗaɗen ba sa cikin kasafin kuɗin wannan shekara.

    Yarjejeniyar ta haɗa da inganta albashi, da alawus alawus da kuma yanayin aiki.

    Yajin aikin dai ya kawo cikas ga aikin bayar da kulawar lafiya, wanda ya kai ga barin marasa lafiya ba tare da ma'aikatan da za su kula da su ba a asibitocin gwamnati da ke faɗin ƙasar.

    Hakan sai da ya kai ga gwamnatin ƙasar kiran tsoffin ma'aikatan jinya da ugozoma da suka yi ritaya su kawo agaji saboda yadda aiki yayi wa likitoci yawa.

  20. MDD ta yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila kan Iran tare da kiran 'kai zuciya nesa'

    Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya buƙaci Gabas ta Tsakiya su yi takatsantsan tare da yin Allah-wadai da harin da Isra’ila ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

    A madadin shugaban, kakakinsa ya bayyana cewa: "Guterres na nuna damuwa musamman kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan wuraren sarrafa nukiliya a Iran, a daidai lokacin da ake gudanar da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan matsayin shirin nukiliyar Iran."

    Kakakin ya ce, "Antonio Guterres ya buƙaci ɓangarorin biyu su yi takatsantsan tare da kaucewa fadawa cikin rikici mai tsanani, wanda yankin ba zai iya jure wa ba."