Da gaske Tinubu ya ce zai dakatar da shari'ar Musulunci a Najeriya?
Fadar shugaban Nijeriya ta musanta wani labari da ta ce na jabu ne, da ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na yunƙurin yi wa tsarin mulkin Nijeriya gyaran fuska domin sauya sunan ƙasar da kuma rusa dokar shari'ar Musulunci.
Ta ce labarin wanda aka wallafa ba tare da ambatar majiyarsa ba, wani ɓangare ne na "maƙarƙashiyar wasu ƴan siyasa da idonsu ya rufe a ƙoƙarinsu na haddasa ƙiyayya da janyo rikicin siyasa da tunzuri" gabanin babban zaɓen 2027.
Labarin dai ya bayyana ne a shafukan sada zumunta a makonnin da suka gabata kuma ya sake bayyana a baya-baya nan.