Kayan agaji sun fara isa Jamaica bayan ɓarnar guguwar Melissa
An kara karfafa duk wasu ayyukan jin kai a kasar Jamaica bayan mummunar barna da guguwar Melissa ta haddasa a kasar.
Kayan agaji sun fara isa cikin ƙasar bayan da hukumomi suka sake buɗe filayen jiragen saman ƙasar, ciki har da na babban birnin Kingston.
Gwamnatin Jamaica na ci gaba da kokarin dawo da wutar lantarki a yankuna da dama, yayin da ambaliyar ruwa ta ci gaba da hana zirga-zirga a wasu sassan yammacin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa gidaje da dama sun rushe yayin ruwan sama mai karfi, kuma rundunar sojin Jamaica na gudanar da aikin kwashe tarkacen gini da suka toshe hanyoyin shiga wasu yankuna da bala’in ya shafa.