Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 31/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 31/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Ibrahim Kakangi, Aisha Babangida da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonni kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Za mu kawo muku wasu gobe da safe. Kafin nan, kuna iya karanta labaran da muka kawo a yau idan kuka duba ƙasa.

  2. Labarai da dumi-dumi, Trump ya yi iƙirarin ana yi wa Kiristocin Najeriya kisan gilla

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa zai saka Najeriya cikin jerin ƙasashe "da ake da damuwa a kansu" saboda zargin yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla.

    Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na dandalin Truth Social, Trump ya ce "shi ne mataki mafi ƙanƙanta da ya dauka" zuwa yanzu.

    "Kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya," in ji shi. "Ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar. Saboda haka na ayyana Najeriya ƙasar da ake da damuwa a kanta".

    Bugu da ƙari, Trump ya ce ya bai wa 'yanmajalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa.

    Tun a farkon watan nan wani sanata a Amurkan ya yi zargin yi wa Kiristoci kisan gilla, wanda gwamnatin Najeriya ta musanta.

    Amma lamarin ya ci gaba da jawo muhawara a Najeriya game da sahihancin iƙirarin.

  3. Umarnin kotu ba zai hana mu cigaba da shirin babban taro ba - PDP

    Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP ta umarci mambobi da 'yan kwamatinta su ci gaba da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa duk da umarnin wata kotu da ya dakatar da ita daga yin hakan.

    A yau Juma'a ne wata kotun tarayya ƙarƙashin Mai Shari'a James Omotosho ta umarci jam'iyyar ta dakatar da shirin taron da ta tsara a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba.

    Cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar Debo Ologunagba ya fitar a yammacin nan, PDP ta ce "ta kaɗu" da hukuncin kotun, amma ba zai kawo mata tsaiko ba.

    Sanarar ta ƙara da cewa wani hukuncin Kotun Ƙoli na baya-bayan nan "ya tabbatar da ikon jam'iyya wajen tafiyar da al'amuranta na cikin gida da kanta".

    A gefe guda kuma, ta ce za ta ɗaukaka ƙara game da hukuncin.

    "Duk da haka...PDP ta umarci lauyoyinta su ɗauki matakin gaggawa domin ɗaukaka ƙara kan hukuncin bisa jajircewarmu wajen karewa da kuma ɗaukaka tsarin dimokuraɗiyya mai jam'iyyu da yawa a ƙasarmu," in ji sanarwar.

  4. An tsare jami'an soja da zargin yunƙurin hana gudanar da zaɓe a Guinea-Bissau

    Jami'an gwamnati a ƙasar Guinea-Bissau sun tabbatar wa BBC cewa ana tsare da wasu manyan jami'an rundunar sojin ƙasar a yau Juma'a.

    Hukumomi sun ce an kama jami'an ne saboda zargin su da yunƙurin "kawo wa dokar tsarin mulki cikas" a jajiberin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na 'yanmajalisa da za a yi ranar 23 ga watan Nuwamba.

    A cewar mataimakin babban hafsan sojan ƙasar, Janar Mamadou Touré, suna yunƙurin "hana gudanar da zaɓen.

    A 2019 aka zaɓi Umaro Sissico Embalo shugaban Guinea-Bissau, amma 'yan'adawa na jayayya game da sahihancin mulkinsa cewa wa'adinsa ya ƙare tun a watan Fabrairun 2025.

    Ƙasar da ke Afirka ta Yamma ta fuskanci yunƙuri ko kuma juyin mulki aƙalla sau 10 tun bayan samun 'yancin kanta a 1974.

  5. Babu shirin cire Andrew daga jerin magadan sarautar Birtaniya

    Fadar Gwamnatin Birtaniya ta tabbatar cewwa ba ta da shirin sauya dokar da ta tsara jerin magadan sarautar ƙasar duk da matakin ƙwace matsayin yarima na Prince Andrew da fadar ta yi.

    Andrew ne na takwas a jerin gadon sarautar kuma sai majalisar dokoki ta yi gyara kan dokar kafin a iya cire shi.

    Mai magana da yawun ofishin Firaminista Keir Stermer ya ce gwamnatin ba ta da niyyar yin hakan.

  6. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta dakatar da PDP gudanar da babban taro na ƙasa

    Babbar kotun tarayya ta umarci babbar jam'iyyar adawa a Najeriya Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa a wata mai zuwa.

    Rahoton jaridar Daily Trust ya ruwaito Mai Shari'a James Omotosho na bayar da umarnin bayan shigar da ƙorafi gabansa domin ya duba ko PDP ɗin za ta iya ci gaba da shirin gudanar da taro na 15 da 16 ga watan Nuwamba.

    Ana ganin mutumu uku da suka shigar da ƙarar masu yi wa Ministan Abuja Nyesom Wike biyayya ne, wanda ya ci alwashin hana gudanar da taron sakamaon rigimar da yake yi da shugabancin jam'iyyar.

    Masu shigar da ƙarar sun yi zargin cewa PDP ta gaza wajen bin dokokin mulkin jam'iyyar da kuma Dokar Zaɓe ta 2022 game da shirin gudanar da taron.

    Lauyan masu ƙorafi ya faɗa wa kotun cewa PDP ba ta gudanar da zaɓukan shugabancin jam'iyyar ba a jihohi 14, inda ya nemi kotun ta duba ko hakan ya saɓa wa doka.

    Kazalika, a kwanan nan Sakataren PDP na Ƙasa, wanda abokin siyasar Wike ne, ya shigar da ƙorafi ga jami'an tsaron Najeriya cewa shugabancin jam'iyyar sun saci sa-hannunsa a takardar da suka aika wa hukumar zaɓe Inec ta sanar da babban taron, zargin da PDP ta musanta.

    Yayin babban taron da aka shirya gudanarwa, wakilai za su zaɓi sabon shugabancin jam'iyyar na ƙasa, wanda zai bai wa masu adawa da Wike damar sauke dukkan masu yi masa biyayya a cikin ƙunshin shugabancinta.

  7. Masu zanga-zanga sun bijire wa umarnin sojin Tanzaniya kan dakatar da tarzoma

    Masu zanga-zanga sun sake fitowa kan tituna a Tanzaniya karo na uku, duk da gargaɗin da hafsan sojin ƙasar ya yi musu na su dakatar da tarzomar da rikici.

    Zanga-zangar ta ɓarke a manyan birane inda matasa ke nuna adawa da sakamakon zaɓen da aka gudanar ranar Laraba, suna cewa ba a yi adalci ba domin an hana manyan ‘yan adawa yin takara da shugabar ƙasa Samia Suluhu Hassan.

    Har yanzu intanet ɗin ƙasar a katse take, abin da ke hana samun sahihan bayanai kan mutuwar mutane, yayin da hukumomi suka tsawaita dokar hana fita domin rage tarzomar.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga jami’an tsaro na ƙasar da su guji amfani da karfi fiye da kima.

    “Mun damu da rahotannin mutuwa da raunuka da suka faru yayin zanga-zangar da ke da alaƙa da zaɓen a Tanzaniya. Rahotannin da muka samu sun nuna cewa aƙalla mutane 10 ne suka mutu,” in ji mai magana da yawun hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta MDD, Seif Magango, kamar yadda kamfanin Reuters ya ruwaito.

    Kungiyar Amnesty International da ke Kenya ta shaida wa BBC cewa saboda katsewar sadarwa a Tanzaniya, ba ta iya tabbatar da rahotannin mutuwa ba.

    Asibitocin ƙasar kuma suna ƙin bayar da bayani ga ‘yan jarida da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam kan adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata.

  8. Wane ne yariman Birtaniya da aka tuɓe wa rawani kuma me zai faru da shi?

    Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da tafkawa, a yanzu an tuɓe shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko muƙami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda ɗa ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II.

    Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da hakan.

    A yanzu "za a riƙa kiransa da tsuran sunansa, wato Andrew Mountbatten Windsor," in ji sanarwar.

    Masarautar na fatan wannan mataki nata zai kawo ƙarshen muhawara kan jerin abin kunyar da ake zargin yariman ya aikata waɗanda ake alaƙantawa da masarautar.

    Yanzu an tuɓe masa, ƙarfi da yaji, duk wasu sarautu da ke kansa, kamar yariman York da sauran su.

  9. Yau take Ranar Birane ta Duniya

    Yau ne ake bikin Ranar Birane ta Duniya da ake gudanarwa a kowace ranar 31 ga watan Octoba.

    An keɓe wannan rana ne don tunawa da muhimmancin birane wajen raya tattalin arziki da bunƙasa ci gaban al’umma da kare muhalli.

    Wannan rana tana mai da hankali kan rawar da birane ke takawa wajen samar da ayyuka da ilimi da kiwon lafiya da sauran abubuwan more rayuwa ga jama’a.

    Masana sun bayyana cewa birane suna da matuƙar muhimmanci wajen haɗin kai da samar da ci gaban kasa.

    A wannan rana, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira ga shugabannin ƙasashe da mutane su mayar da birane wuraren da za a samu lafiya da adalci da kuma ɗorewar rayuwa.

    A Najeriya dai, birane kamar Legas da Abuja da Kano na fuskantar matsaloli da dama ciki har da yawan jama’a da cunkoson ababen hawa da kuma gurbatar muhalli.

    Saboda haka, masana sun buƙaci gwamnatin tarayya da jihohi su ƙara mayar da hankali kan inganta tsarin birane da kula da muhalli.

  10. 'Na bar rundunar sojin Najeriya cikin farin ciki da alfahari'

    Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce ya bar aiki da rundunar sojin ƙasar cikin farin ciki da alfahari.

    Yayin da yake jawabi a wani ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka shirya masa kan bankwana da aikin soji a Abuja, babban birnin ƙasar, Janar Musa ya ce ya yi iya ƙoƙarinsa wajen bauta wa Najeriya da gaskiya da aminci.

    Tsohon babban hafsan sojin ƙasar, wanda ya shafe shekaru da dama a aikin sojin ƙasar, ya ce hidimarsa cike take da jajircewa da sadaukarwa.

    “Yayin da nake cire kayan soja a yau, ina yin hakan cike da alfahari, saboda irin gudummawar da na bayar wajen kare ƙasata," in ji shi.

    Janar Musa ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi don jagorantar rundunar tsawon fiye da shekaru biyu, yana mai kira ga dakarun ƙasar su bai wa sabon shugaban da sauran shugabannin rundunonin sojin ƙasar cikakken goyon baya.

    “Duk da cewa na bar aikin soji yau, ba zan daina ƙaunar ƙasata ba. Har yanzu soja ne ni a zuciya, kuma ɗan ƙasa ne mai kishin Najeriya,” in ji Janar Musa.

    A makon da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya sake fasalin manyan hafsoshin tsaron ƙasa, inda ya maye gurbin Janar Musa da Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon babban hafsan tsaron ƙasar.

  11. Jagororin PDP sun isa kotu kan shari'ar gudanar da babban taron jam'iyyar

    Jagororin babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun isa babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau domin sauraron hukuncin ƙarshe kan ƙarar da wasu shugabannin jam’iyyar na jihohi suka shigar.

    Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Iliya Damagum, da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ne suka halarci zaman kotun.

    Ƙarar dai ta fito ne daga Shugaban PDP na Jihar Abia, Abraham Ammah, da na Jihar Imo, Austine Nwachukwu, da kuma George Tuner daga Bayelsa, waɗanda suka buƙaci kotu da ta dakatar da gudanar da babban taron jam’iyyar da aka shirya yi a birnin Ibadan, Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025.

    Masu shigar da ƙarar suna zargin cewa an karya tsarin mulki na jam'iyyara da kuma yadda za a gudanar da zaɓen sabbin shugabanni a lokacin taron.

    Sun ce ba a bi doka da kundin tsarin jam’iyyar wajen shirya taron ba, don haka suka nemi kotu ta hana gudanar da shi har sai an warware matsalolin cikin gida da ke damun jam’iyyar.

    A halin yanzu, akwai ɗumbin mambobi da magoya baya na PDP da ke jiran sakamakon hukuncin kotun da zai bayyana makomar babban taron jam'iyya

  12. 'Sanya harajin kashi 15 kan shigo da man fetur zai janyo tashin farashinsa'

    Manyan ‘yan kasuwar man fetur sun yi gargaɗi cewa kafa harajin kashi 15 kan shigo da man fetur da dizal da shugaba Tinubu ya yi ka iya jawo ƙarin tashin farashin mai a kasuwa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Wannan harajin da Tinubu ya amince da shi ya haifar da rabuwar ra’ayi a ɓangaren mai da iskar gas na kasa

    Wasu ƙwararrun tattalin arziki sun yaba da matakin, suna ganin zai taimaka wajen rage shigo da man fetur daga waje da kuma ƙarfafa masana’antar man fetur ta cikin gida.

    Sai dai wasu kuma suna nuna damuwa kan yiwuwar tashin farashin man fetur wanda hakan zai shafi rayuwar talakawa.

    Masu ruwa da tsaki a harkar man fetur sun ce wannan sabon haraji zai iya kara matsin lamba ga masu amfani da man fetur a gida, musamman ma direbobi da masu masana’antu, yayin da gwamnati ke fatan hakan zai karfafa masana’antar man fetur ta cikin gida da rage dogaro da shigo da man daga waje.

  13. Kashe-kashen RSF a Sudan na tuno da hare-haren mayaƙan Janjaweed

    Sabbin bayanai kan kisan jama’a a birnin El-Fasher da ke yankin Darfur a Sudan sun sa ‘yan rajin kare hakkin dan Adam da ƙungiyoyin agaji suna ganin kashe-kashen RSF a Sudan na tuno da hare-haren mayaƙan Janjaweed.

    Ƙwace ikon El-Fasher, bayan watanni 18 da RSF ta yi ya nuna yadda rikicin ƙasar ya samo asali daga abubuwan da suka faru a baya da kuma yadda ake tafiyar da yaƙin.

    RSF ta samo asali ne daga Janjaweed, wata kungiyar maƙiya ta larabawa wadda ta kashe dubban mutane daga ƙabilun da ba Larabawa bane a farkon shekarun 2000.

    Ana zargin rundunar RSF da kisan ƙabilanci tun bayan barkewar rikici tsakaninta da sojoji a watan Afrilun 2023.

    Amma kuma shugabannin RSF suna musanta zargin, sai dai a ranar Laraba, jagoranta Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya amince da “take hakkin jama’a” a El-Fasher.

    An samun tabbacin zargin ne daga bidiyon da ‘yan RSF kansu suka yaɗa, waɗanda ake ganin suna nuna kashe-kashen mutane da aka kama da murnar mutuwarsu, da cin zarafi da tsangwama ga wasu. do a short headline for this

  14. Jihohin Najeriya bakwai da ke kan gaba a samun kudin shiga

    Adadin kuɗin da jihohin Najeriya ke samu daga kason tarayya ya kusan ninkawa idan aka kwatanta da kafin 2023, sakamakon cire tallafin man fetur, a cewar cibiyar budeget IT mai nazarin kasafin kuɗi a Najeriya.

    Galibin jihohin kan dogara da kuɗaɗen rabon razikin ƙasa da suke samu daga gwamnatin tarayya, wanda ake rabawa a kowane wata, tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin da kuma ƙananan hukumomi.

    Da kuɗaɗen ne jihohin ke gudanar da ayyuka da biyan albashi da kuma tafiyar da gwamnati.

    Don haka idan babu wannan kuɗi jihohin ƙasar da dama ba za su iya gudanar da kansu ba.

  15. ‘Yan sanda sun kuɓutar da ƴan ƙasashen waje 23 da aka sace a Nasarawa

    Rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ta bayyana cewa jami’anta sun ceto ƴan ƙasashen waje 23 daga hannun masu garkuwa da mutane, tare da kama mutum 14 da ake zargi da hannu a laifin a Jihar Nasarawa.

    A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar ranar Juma’a, an gudanar da wannan samame ne da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar Talata, 22 ga Oktoba, 2025, a Angwan Adamu Ruga Fulani Zone B, Riverside, Ado Mararaba, da ke Jihar Nasarawa.

    Adeh ta ce: “A cikin wata babbar nasara a yaƙin da ake yi da masu garkuwa da mutane da safarar mutane, rundunar Scorpion Squad ta kama mutum 14 da ake zargi da garkuwa da mutane, sannan ta ceto mutum 23, dukkansu ‘yan ƙasashen waje, daga hannun masu garkuwar.”

    Sanarwar ta ƙara da cewa aikin ya biyo bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa an yaudari wasu ‘yan ƙasashen waje zuwa Najeriya da alkawarin samun aiki mai kyau, amma da suka iso, aka kama su kuma aka nemi kuɗin fansa daga iyalansu ta WhatsApp da sauran kafafen sadarwa.

    Binciken farko, a cewar ‘yan sandan, ya gano cewa shugaban waɗanda suka aikata laifin mai suna Abubakar Jigiba yana da gidaje a Côte d’Ivoire da Ghana da Mali da Najeriya, yayin da ɗan uwansa ke kula da safarar mutane daga Mali zuwa Najeriya, inda ake tsare da su har sai an biya kuɗin fansa.

    “Bincike ya kuma nuna cewa an shigo da waɗannan mutanen cikin ƙasar ta hanyoyin da ba bisa doka ba, daga bisani kuma aka kulle su a gidaje biyu,” in ji sanarwar.

  16. Zanga-zangar adawa da gwamnati na ƙara ƙamari a Tanzaniya

    Ana sa ran zanga-zangar adawa da gwamnati za ta ci gaba a ƙasar Tanzaniya, bayan rahotannin tashin hankali da suka faru jiya a wurare da dama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an ‘yan sanda.

    Zanga-zangar ta samo asali ne daga fushin jama’a kan zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a makon nan, wanda aka ce an hana yawancin fitattun ‘yan adawa shiga zaɓen.

    Shugaban rundunar sojin ƙasar ya yi jawabi ga al’umma yana kira da su kwantar da hankalinsu da guje wa tashin hankali, yayin da ake ci gaba da samun rashin tabbas a fɗdin ƙasar.

    Rahotanni sun nuna cewa intanet har yanzu a katse take a ƙasar, abin da ke hana ‘yan ƙasa da manema labarai samun sahihan bayanai kan halin da ake ciki.

    Ana sa ran masu zanga-zangar za su sake taruwa yau don yin tafiya zuwa gidan gwamnati a birnin Dar es Salaam, kafin sanar da sakamakon zaɓen a ƙarshen wannan mako.

    Hukumomi sun ƙara tsaurara matakan tsaro a manyan birane, domin kauce wa rikice-rikice da ɓarna.

    Har yanzu ba a san inda Shugabar ƙasa Samia Suluhu Hassan take ba, yayin da ake ci gaba da yaɗa jita-jita game da lamarin.

    Ana sa ran ita ce za ta lashe zaɓen, duk da cewa masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa zaɓen bai kasance na gaskiya da adalci ba.

  17. APC ta samu kashi biyu cikin uku na kujerun majalisar wakilan Najeriya

    Jam’iyyar APC mai mulki ta samu kashi biyu cikin uku na kujerun majalisar wakilan Najeriya, bayan da wasu ‘yan majalisa guda shida suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar a ranar Alhamis makonni kaɗan bayan da ta cimma irin wannan rinjaye a majalisar dattawa.

    Cikin sabbin ‘yan majalisar da suka sauya sheƙar har da ‘yan jam’iyyar PDP guda biyar daga Jihar Enugu, da kuma ɗan jam’iyyar Labour ɗaya daga Jihar Filato.

    Wannan mataki ya ƙara ƙarfin jam’iyyar APC a zauren majalisar.

    Majalisar Wakilai tana da kujeru 360 gaba ɗaya, inda samun kashi biyu cikin uku ke nufin kujeru 240 kenan.

    Jam'iyyar APC yanzu tana da kujeru 243, yayin da PDP ta ragu zuwa 72. LP na da kujeru 21, NNPP 15, APGA 5, ADC 1, SDP 2 sannan YPP 1.

    Da farko dai a watan Yunin 2023, APC na da kujeru 175 kacal, yayin da jam’iyyun adawa suka tara 182 abin da ya ba su ƙaramin rinjaye a wancan lokaci.

    Amma bayan shekara guda na sauye-sauye, APC ta karfafa matsayinta a majalisun biyu.

  18. Tchiroma ya buƙaci ƴan Kamaru su zauna a gida don nuna adawa da sakamakon zaɓe

    Dan takarar jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban kasar, ya yi kira ga jama’ar kasar da su zauna a gida daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Nuwamba, a wani sabon mataki na nuna adawa da sakamakon zaɓen da ya ayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben.

    A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Tchiroma ya ce manufar wannan mataki ita ce tsayar da harkokin ƙasar gaba ɗaya, domin duniya ta fahimci cewa “muna nuna adawa, kuma ba za mu mika wuya ba.”

    Ya buƙaci jama’a da su rufe shagunansu, su dakatar da ayyukansu, su zauna a gidajensu, domin nuna haɗin kai da juna da kuma tunatar da gwamnati cewa “karfin tattalin arziki yana hannun jama’a ne.”

    Tchiroma, ɗan shekara 76, wanda tsohon kakakin gwamnatin ƙasar ne, ya bayyana cewa an ɗauke shi an kai shi zuwa wuri mai tsaro ta hannun wasu sojojin da ke goyon bayansa, wadanda yanzu ke kula da tsaronsa.

    Sai dai ya ƙara da cewa an sace mutane biyu daga cikin iyalansa da kuma mai musu girki a garinsa na Garoua.

    Kiran nasa na zuwa ne bayan rikice-rikicen da suka ɓarke bayan zaɓe, wanda ya yi sanadin mutuwar da raunata mutane da dama, tare da damƙe wasu masu zanga-zanga.

    A farkon makon nan, gwamnatin ƙasar ta ce Tchiroma Bakary zai fuskanci shari’a bisa iƙrarin nasara da kuma shirya zanga-zanga, wanda ta bayyana a matsayin tayar da fitina.

  19. Addadin waɗandu suka mutu sanadin guguwar Melissa a Jamaica sun ƙaru

    Aƙalla mutum 19 ne suka rasa rayukansu a ƙasar Jamaica sakamakon guguwar Melissa, kamar yadda Ministar Bayani ta kasar, Dana Morris Dixon, ta tabbatar, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kuma kokarin kai agaji ga yankunan da guguwar ta fi shafa.

    Guguwar, wadda ta kasance daya daga cikin mafi karfi da ta taba afkawa yankin Caribbean, ta kuma hallaka mutane 30 a kasar Haiti, a cewar hukumomin kasar.

    A cewar Dixon, “Akwai al’ummomi gaba ɗaya da ke ƙulle cikin ambaliyar ruwa, wasu kuma sun lalace baki ɗaya,” tana mai bayyana cewa an ga mummunar barna musamman a yankunan yammacin ƙasar.

    Har yanzu yawancin sassan tsibirin ba su da wutar lantarki, yayin da mazauna ke ƙoƙarin ceto kadarorinsu daga ambaliyar ruwa da laka.

    Mutane da dama suna cikin halin matsanancin bukatar taimako.

    Wasu yankuna kuma sun shafe ’yan kwanaki ba tare da ruwa ba, sannan abinci yana ƙara yin karanci.

    Sai dai yanzu kayan agaji sun fara shiga cikin kasar da sauri, bayan da filin jirgin saman babban birnin Kingston ya dawo aiki yadda ya kamata.

    Amma kananan filayen jiragen sama na yankuna, musamman wadanda ke kusa da wuraren da ake bukatar taimako sosai, har yanzu ba sa aiki gaba ɗaya.

  20. Gwamnatin tarayya ta fitar da kuɗi domin biyan bashin albashin ASUU

    Gwamnatin tarayya ta fitar da naira biliyan 2.3 domin biyan bashin albashi da sauran kuɗaɗen baya da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da sauran ƙungiyoyin jami’o’i ke bin ta.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi, Folasade Boriowo ta fitar a ranar Laraba inda ta bayyana cewa kuɗaden an fitar da su ne ta ofishin Akanta Janar na Tarayya.

    Sanarwar ta ce, “An fitar da jimillar naira biliyan 2.311 domin biyan bashin albashi da bashin ƙarin girma na jami’o’in gwamnati. Ana sa ran jami’o’in da abin ya shafa za su fara samun sakon biyan kuɗadensu a kowanne lokaci daga yanzu.”

    Haka kuma, gwamnatin ta bayyana cewa tana kusa da kammala sakin kuɗaden fansho a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

    Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dage wajen ganin an kawo karshen dukkan matsalolin da suka shafi walwala da kudaden jami’o’i cikin gaskiya da adalci da kuma hanya mai dorewa.