Wata wuta ta tashi a asibiti a Taiwan
Wata wuta da ta tashi a asibitin kudancin Taiwan ta kashe mutum tara.
Hukumomi sun ce wutar ta tashi ne bayan da gagarumar guguwa ta mamaye yankin, lamarin da ya kawo tangarɗa ga aikin ceto.
Wakiliyar BBC ta ce har yanzu dai ba a iya gano dalilin da ya haifar da gobarar ba, sai dai rahotannin cikin gida na cewa wutar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki.
Guguwar ta kwashe kwana biyu tana shawagi a kudancin gabar tekun Taiwan, kafin daga bisani ta afkawa yankin. Break
















