Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/08/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. 'Tattaunar Trump da Putin ba tare da Ukraine ba, ba za ta yi tasiri ba'

    Babbar jami'ar harkokin ƙetare a ƙungiyar Tarayyar Turai, Kaja Kallas, ta ce duk wata yarjejeniyar zaman lafiya kan Ukraine da za a kulla, matuƙar ba a sa ƙasar a ciki ba, to ba za ta yi tasiri ba.

    A lokacin da take tattaunawa da BBC, Ms Kallas ta sake jadadda kiranta na a sa shugaban Ukraine a tattaunawar ranar Juma'a da za a yi tsakanin shugaba Trump da Putin a Alaska.

    Ta yi gargaɗin cewa ba ɓoyayya abu ne burin Mista Putin na haifar da rabuwar kawuna da babakere a tattaunawarsa da Trump.

    Mista Trump dai na ganin shawararsa ita ce mafita a wannan yaƙi

  2. Giyar mulki na jan Trump - Ƴan Democrats

    'Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da mutumin da giyar mulki ke ruɗawa, bayan ya ce zai tura jami'an rundunar tsaro ta ƙasar birnin Washington don yaƙi da laifukan da ake ganin sun gagari ƴansandan birnin.

    Magajiyar birnin Muriel Bowser, ta ce matakin bai dace ba, sannan ta musanta batun da shugaban ke yi cewa an gaggara daƙile masu aikata laifi.

    'Yan Democrats a majalisa, sun ce wannan mataki babu wani abin da zai haifar face 'tsoro da hargitsi, kuma wannan yunƙuri ne kama hanyar kama-karya.

    Shugaban masu rinjaye a majilsar wakilai ya ce Mista Trump ya mayar da mulki kamar wata sarauta.

    Shi dai Trump ɗin ya ce birnin washington a cike yake da masu gararamba a tittuna suna aikata miyagun ayyuka kuma dole ya kawo gyara.

  3. Tsare Tambuwal ba zai hana shi yunƙurin kawo sauyi ba - PDP

    Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da kamawa tare da tsare tsohon gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, lamarin da ta zargi jam'iyyar APC da yunƙurin jefa dimokuraɗiyyar ƙasar cikin ruɗani.

    A wata sanarwa sakataren watsa labaran PDP na jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar, ya ce wannan na cikin yunƙurin cin zarafi da murƙushe jam'iyyun adawa a ƙasar.

    Ya ce ana wannan kame-kamen ne "a daidai lokacin da aka fara ƙoƙarin samar da haɗakar jam'iyyun adawa a ƙasar domin fuskantar zaɓe mai zuwa," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa kamen ba zai hana komai ba wajen yunƙurin da suke yi na kawo sauyi.

    "Muna kira ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ta daina zama karen farauta domin cin zarafin jam'iyyun adawa."

    Tun da farko, Hukumar EFCC ce ta gayyata, sannan ta tsare tsohon gwamnan bisa zarginsa da almundahanar kuɗi.

    Rahotanni sun ce sanatan ya isa ofishin hukumar ne da kansa domin amsa gayyatar da aika masa a ranar Litinin, sannan hukumar ta riƙe shi.

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC.

    Yau ma za mu ɗaura daga inda muka tsaya wajen kawo muku labaran kai-tsaye daga Najeriya da sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.