Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/12/2025

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Anjeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

  • Ghana ta kama ƴan Najeriya 32 kan zargin zamba ta intanet
  • Ƴan bindiga sun kashe mutum 11 a Australia
  • Cambodia ta rufe iyakokinta da Thailand yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa
  • Trump ya sha alwashin ɗaukar fansa kan kisan sojojin ƙasarsa a Syria

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Asabar.

    Muna nan tafe da wasu gobe da safe.

    Mu kwana lafiya.

  2. PDP ta shirya lashe zaɓukan 2027 - Tanimu Turaki

    Tanimu Turaki

    Asalin hoton, PDP

    Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Kabiru Tanimu Turaki, ya bayyana shirin jam'iyyar tasu na yin nasara a babban zaɓen 2027.

    Turaki na magana ne bayan ganawarsa da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta babban birnin jihar Ogun yau Asabar.

    Obasanjo ne shugaban ƙasa na farko ƙarƙashin PDP a 1999 kuma ɗaya daga cikin dattijanta a yanzu, yayin da har yanzu take fama da rikicin cikin gida.

    Yayin ziyarar, Turaki ya ce yanzu PDP ta fi koyaushe kasancewa cikin shiri "domin dawo da matsayinta a siyasar Najeriya".

    "PDP ta shirya tsaf don tunkarar zaɓen 2027. Amma sai mun fara cin zaɓen Ekiti, da na Osun. Idan muka yi haka babu wanda zai yi tantamar shirin da PDP ta yi na ƙalubalantar rashin iya mulki na APC," in ji shi.

  3. Ɗanbindigar IS ya kashe sojojin Amurka a Syria

    Sojojin Amurka a Syria

    Asalin hoton, Reuters

    Wani sojan ƙungiyar Islamic State sun kashe dakarun sojan Amurka biyu da tafintansu farar hula bayan kwanton ɓauna da ya yi musu a Syria, kamar yadda rundunar sojan Amurka ta bayyana.

    Jami'ai sun ce an raunata wasu dakaru uku a harin amma an harbe ɗanbindigar.

    Ba a bayyana sunayen waɗanda aka kashe ba har sai an sanar da 'yan'uwansu, a cewar rundunar US Central Command.

    Sakataren Tsaro na Amurka Pete Hegseth ya ce: "Muna sanarwa cewa, duk wanda ya kai wa sojojin Amurka hari - a ko'ina a duniya - zai shafe gajeriyar rayuwarsa da tunanin cewa Amurka za ta bi sawunsa, ta kama shi, kuma ta kashe shi."

  4. Faɗaɗa gidajen Yahudawa da Isra'ila ke yi a Gaɓar Kogin Jordan ya wuce misali - MDD

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Matsugunin Yahudawa na Kedar da ke yankin gaɓar yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye

    Wani sabon rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya ce gine-ginen da Isra'ila take yi a yankunan da ta mamaye na Falasdinawa a Gaɓar Yamma ta Kogin Jordan sun kai yawan da ba su taɓa kaiwa ba tun bayan da aka fara tattara bayanai shekara takwas da suka wuce.

    Sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Alla wadai da mamayar da Israilar ke yi, wadda ya kira da aikin da ba kakkautawa.

    Ya ƙara da cewa hakan na ƙara rura wutar rikicin bangarorin biyu da kokarin hana Falasdinawa hanyar shiga yankunansu, tare da barazana ga damar kafa kasar Falasdinu mai 'yancin kanta.

    Rahoton ya ce a shekarar nan Isra'ila ta amince ko kuma ta yi nisa da shirin gina wasu gidaje 47,000 a yankunan na Falasdinawa da ta mamaye wanda ya ninka na bara sau biyu.

    Isra'ilawa ƴan kama-wuri-zauna rabin miliyan ne ke zaune a Gaɓar Yamma tare da Falasɗinawa kusan miliyan uku.

  5. Rwanda ta saɓa yarjejeniyar zaman lafiya da Congo, in ji Amurka

    Trump tare da shugabannin Rwanda da Congo

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce ayyukan Rwanda a gabashin Dimokuraɗiyyar Congo ya saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Donald Trump ya ƙulla tsakaninsu.

    Ya ƙara da cewa za a ɗauki matakan ganin ɓangarorin sun ci gaba da mutunta tanade-tanaden yarjejeniyar.

    A gefe guda kuma, Rwanda ta ce Congo ta yi watsi da yarjejeniyar saboda yadda take yunƙurin ƙwato wani yanki da 'yantawayen M23 suka kama iko da shi.

    Sai dai Ministan Harkokin Wajen Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana mamakin zargin ƙasarsa da haddasa cigaban faɗan.

    'Yantawayen na M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun ƙwace gari na biyu mafi girma a yankin Kudancin Kivu mai maƙwabtaka da ƙasar Burundi.

  6. Ban yi nadamar goya wa Tinubu baya ba - Wike

    Wike da Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Ministan Abuja babban birnin Najeriya ya ce bai yi nadamar goya wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu baya ba tun daga 2022, duk da kasancewarsa ɗan jam'iyyar PDP mai adawa.

    Wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Nyessom Wike ya ce ya ɗauki matakin ne "bisa dacewa da ɗabi'a da kuma aƙidarsa", yana mai cewa "ban taɓa ɓoye goyon bayana ga Shugaba Tinubu ba tun daga farko".

    Ministan ya bayyana haka ne yayin taron bikin cikarsa shekara 58 da haihuwa yau Asabar a Abuja, wanda ya samu halartar 'yansiyasa daga jam'iyyu daban-daban.

    Wike ya goyi bayan Tinubu ne bayan samun saɓani da shugabannin PDP ana dab da zaɓen 2023, rikicin da ya kai shi ga zama minista a gwamnatin APC wanda kuma har yanzu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

  7. Gidaje miliyan ɗaya sun rasa wutar lantarki a Ukraine bayan harin da Rasha ta kai

    ...

    Asalin hoton, State Emergency Service Of Ukraine

    Fiye da gidaje miliyan ɗaya ne ba su da wutar lantarki a Ukraine bayan wani ƙazamin harin da Rasha ta kai cikin dare ya shafi makamashi.

    Ministan harkokin cikin gida na Ukraine Ihor Klymenko, ya ce yankuna biyar ne lamarin ya shafa, yayin da aƙalla mutane biyar suka jikkata, kuma ana ci gaba da aikin kashe gobara da ta tashi sakamakon harin.

    Hare-haren Rasha kan ababen more rayuwa na makamashin Ukraine dai ya zama ruwan dare tun lokacin da aka fara yaƙin.

    Moscow ta ƙara zafafa kai hare-hare yayin da ƙasar ke shiga lokacin hunturu.

    Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wakilin shugaban Amurka Donald Trump a na ƙasashen ƙetare zai je Jamus a ƙarshen wannan makon domin ganawa da shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky da shugabannin ƙasashen Turai domin tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin.

  8. Witkoff zai gana da Zelensky don tattaunawa kan yaƙin Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wakilin shugaban Amurka Donald Trump a ƙasashen ƙetare zai tafi Jamus a ƙarshen wannan makon don ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da shugabannin ƙasashen Turai a zagayen ƙarshe na tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine da Rasha.

    Steve Witkoff, wanda ke jagorantar yunƙurin White House na shiga tsakanin Ukraine da Rasha, zai tattauna sabon daftarin yarjejeniyar zaman lafiya da ake shirin yi a Berlin.

    Gwamnatin Trump dai na ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar kafin lokacin Kirsimeti, kuma ta gudanar da tattaunawa da dama da wakilan Ukraine da na Rasha a cikin ƴan makonnin da suka gabata, ko da yake ba a ga alamar samun nasara ba.

    Har yanzu dai ba a tabbatar da shugabannin ƙasashen Turai da za su halarci tattaunawar ta Berlin ba.

  9. Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yaye ƙarin kurata 3,439

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu (NAM), ya yi kira ga sabbin jami’an soja 3,439 da aka horas da su dukufa wurin nuna ƙwarewa yayin gudanar da ayyukansu.

    Dakarun da aka ɗauka waɗanda ke cikin runduna ta 89 na rundunar sojojin Najeriya, sun samu nasarar kammala horon na tsawon watanni shida a Nigerian Army Depot da ke Zariya

    Yayin bikin yaye sojojin, Laftanar Janar Shaibu ya ce horon da aka ba su zai tabbatar da cewa sun yi aiki tuƙuru cikin jajrcewa da nuna kisshin ƙasa.

    Ya tunatar da su kan irin rantsuwar da suka yi, yana mai cewa: “Da wannan rantsuwar, yanzu ya zama dole ku bi dokokin farar hula da na soja, ku guje wa duk wani abu da zai ɓata sunan sojojin Nijeriya ko kuma ƙasa, ku yi hidima da mutunci, da aminci da kuma biyayya ga hukuma.”

  10. Sojojin Najeriya sun daƙile harin mayaƙan ISWAP kan sansanin soji a Borno

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Dakarun sojin Najeriya a ƙarƙashin Operation HADIN KAI (OPHK) sun yi nasarar daƙile wani harin haɗin gwiwa da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai a wani sansanin sojoji da ke yankin Mairari na jihar Borno, inda suka yi mummunar illa ga ayyukan ƙungiyar a yankin.

    Wata sanarwa da ta fito daga jami'in yaɗa labarai na na Operation Hadin kai Laftanar Kanar Sani Uba ta ce mayaƙan sun yi yunƙurin kutsawa sansanin ta hanyar amfani da abubuwa masu fashewa da aka ɗaura a jikn ababaen hawa.

    Dakarun sun gano duka na'urorin nan da nan tare da kawar da su, tare da hana duk wani shiga cikin sansanin.

    Hotunan faifan bidiyo da na CCTV sun tabbatar da cewa an kashe mayaƙan da dama, yayin da wasu suka samu munanan raunuka.

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Sanarwar ta ƙara da cewa kayayyakin da aka ƙwato daga hannun mafaran sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47, da harsasai, da gurnetin hannu da babura da kuma na’urorin sadarwa.

    A halin yanzu dai sojoji na ci gaba da sintiri a yankin domin daƙile ayyukan mayaƙan tare kuma tabbatar da tsaron al’ummar yankin.

  11. Yarjejeniyar tsagaita wuta da Trump ya ƙulla a DR Congo ta wargaje bayan da ƴan tawaye suka ƙwace wani muhimmin birni

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya zargi Rwanda da neman jefa yankin 'great lakes' na Afirka cikin ƙangin yaƙi, mako guda bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Washington domin kawo ƙarshen rikicin da aka kwashe shekaru ana yi.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin shugaban Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo Félix Tshisekedi da shugaban Rwanda Paul Kagame a matsayin "mai cike da tarihi" inda ya ce "wata babbar rana ce ga Afirka, kuma babbar rana ga duniya baki ɗaya".

    Sai dai ƙungiyar ƴan tawayen M23 ta ce ta ƴantar da babban birnin Uvira gaba ɗaya a wani hari da Amurka da ƙasashen Turai suka ce ya samu goyon bayan Rwanda.

    Ƙwararru na Majalisar Dinkin Duniya a baya sun zarge Rwanda da cewa tana da iko a kan ayyukan dakarun ƴan tawayen.

    Rwanda ta musanta zargin, duk da haka, kasancewarta a Washington ya yi nuni da tasirinta kan M23.

    Ƴan tawayen dai ba su ne rattaba hannu kan yarjejeniyar da Trump ya cimma ba - kuma suna taka rawa a wata tattaunawar zaman lafiya ta daban a ƙarƙashin jagorancin Qatar, wadda ke ƙawancen Amurka.

    Ana ganin faɗan da aka yi na baya bayan nan na iya ƙara taɓarɓara yanayin rikicn da ake fama da shi a yankin mai cike da sarƙaƙiya

  12. Jamiyyar APC ta yi wa gwamnan Ribas rajista a hukumance

    ...

    Asalin hoton, RSG/Facebook

    Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya samu rijistar zama ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar a gidan gwamnati da ke Fatakwal.

    Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, Tony Okocha, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya miƙa katin ga Fubara a ranar Juma’a da ta gabata.

    Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Fubara ya ce ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne da nufin bun\ƙasa haɗin kai da ci gaban jihar Ribas.

    Fubara ya ce samun daidaito da jam’iyya mai mulki a matakin tarayya ya zama wajibi don tabbatar da zaman lafiyar siyasa da kuma hanzarta ci gaba a faɗin jihar.

    Gwamnan ya jaddada cewa a yanzu da jihar Ribas ta haɗe a ƙarƙashin inuwa ɗaya da gwamnatin tarayya, aikin da ke gabansa na ƙarfafa jam’iyyar APC da tabbatar da tafiyar siyasa cikin lumana a 2027 ya ƙara fitowa fili kuma a yanzu ana ganin haƙar za ta iya cimma ruwa.

    Bikin ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo (SAN).

  13. Ƙasashen Turai za su bai wa Ukraine bashin kuɗaɗen Rasha da aka daskarar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatocin ƙasashen Tarayyar Turai sun amince su ci gaba da riƙe ko dakatar da kadarorin Rasha na sama da dala miliyan dubu biyu, da suka dakatar da gudanarsu a yankin ƙasashen na -EU, tun bayan da Rasha ta mamayi Ukraine.

    An riƙe yawancin kuɗin gwamnatin Rashar ne a bankin Euroclear na Belgium.

    Shugabannin Turai na sa ran cimma wata yarjejeniya a mako mai zuwa - wadda a ƙarƙashinta za a yi amfani da kuɗin a bayar da bashin taimaka wa gwamnatin Ukraine.

    Ukraine na fuskantar matsalar rashin kuɗi ne bayan kusan shekara huɗu ana yaƙi, a don haka ƙasashen Turai ke son taimaka mata a matsayin ƙawarsu.

    A kan wannan kudiri jami'an Rasha sun zargi kungiyar ta Turai da sata.

    A ranar juma'ar da ta gabata ne babban bankin Rasha ya ce zai shigar da bankin na Belgium -Euroclear ƙara a wata kotu a Moscow - saboda shirin bayar da bashin kuɗin.

  14. An sako rukuni na biyu na hotunan gidan Jeffrey Epstein

    ...

    Asalin hoton, House of Oversight Committee

    Ƴan jam'iyyar Democrat da ke cikin kwamitin sa-ido na majalisar wakilan Amurka sun saki - rukuni biyu na hotuna daga gidan Jeffrey Epstein, attajirin da aka kama da laifin baɗala - da ya hallaka kansa a kurkuku.

    Rukuni na farko ya nuna wasu daga cikin hamshakan attajirai da manyan masu iko, da suka yi mu'amulla da Epstein, waɗanda suka haɗa da Donald Trump.

    An ga Trump a uku daga cikin hotunan, da suka haɗa da wani wanda wasu mata shida da aka rufe fuskokinsu don sirrantawa a hoton, suke tare da shi.

    Rukuni na biyu na hotunan kuwa ya ƙunshi yawanci gidaje ne ba mutane ba.

    Hotuna da aka sakin dai a yanzu ba sa nuna alamun wata baɗala, kuma fadar gwamnatin Amurka - White House ta bayyana sakinsu a matsayin wata kutungwila ta ƴan Democrat ta neman ƙirƙirar wani labari na ƙarya.

    ...

    Asalin hoton, House of Oversight Committee

    An ga tsohon shugaban Amurka - Bill Clinton da Yariman Ingila da aka raba shi da sarautar - ƙanin Sarkin Ingila Andrew Mountbatten, da shaharren mai shirya fina-finai, Woody Allen a cikin hotunan - Sai dai dukkaninsu sun musanta aikata wani abu na ba daidai ba a alaƙarsu da marigayi Epstein.

  15. Ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin Thailand da Cambodia bayan Trump ya ce an tsagaita wuta

    Thailand/Cambodia

    Asalin hoton, Getty Images

    An ci gaba da ɗauki ba daɗi a kan iyakar Thailand da Cambodia da ake takaddama a kai, sa'o'i kaɗan bayan Shugaba Trump ya ce ƙasashen makwabta sun amince su dakatar da artabun.

    A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta, firaministan Thailand -- Anutin Charnvirakul -- ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan soji har sai ta ji babu sauran wata barazana ga yankinta ko al'ummarta.

    Tun da farko ma'aikatar tsaron Cambodia ta ce jiragen saman ƙasar Thailand sun yi ruwan bama-bamai a gine-ginen otal da wata gada.

    Ƙasar Thailand ta ce fararen hula da dama ne suka jikkata sakamakon harin makamin roka da Cambodia ta kai ma ta.

    Aƙalla mutane ashirin ne aka kashe tare da raba dubunnan mutane da muhallansu cikin kwanaki shidan da suka gabata.

  16. Buɗewa

    Jama'a barkamu da wannan safiya ta ranar Asabar, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.

    A yau ma za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya juma'a wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na Whattsapp da Facebook da X da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare a mu.